← Book details Hayateeey Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 40

Sashe 20

Hayateeey Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gidan Eesha ta wuce direct, a d'aki ta same Eesha tana gyara kan gado. Tab'a ta tayi nan ta firgita harda d'an "wayyoo Allah".
Fido ta k'yalk'ale da dariya tace
" Amma ke muguwar tsoraciya ce"
Eesha ta b'ata rai tace
"Kinsan abunda kikayi bai dace ba koh?"
"But atleast da kin rufe kofa ai, Allah ya kiyaye idan b'arawo yashigo fa?"
Wani kallo Eesha ta watsa mata, Fido tace
"So sorry Swthrt! Wai tun safe me kikeyi baki gyara kan gadon ki ba? Kinsan first thing abunda mace yakamata tayi idan ta tashi a bacci shineh gyaran gado"
"Toh sannu uwata"
"I am just saying neh"
"Toh Ban gode ba I don't need your advice"
"Ba godiyar ki nake buk'ata ba, break fast zaki had'o mini"
"Ki shiga kitchen ki had'a".
"Wallahi baki isa ba, daga class fa nake, idan baza kiyi ba sai na tafi gidan mu Allah"

Ganin she is serious Eesha tace
"Ohk bara na dafa miki Indomie zaifi dahuwa da wuri"
"Be fast!"

Bayan minti biyar sai ga Eesha da Indomie wanda yaji kayan had'i, Fido karb'a tayi tace
"Thanks love" tafara ci.

Tana cikin ci ta kalla k'awarta tace
"Guess wa na had'u dashi yau?
" I ain't good at guessing, so tell me who?"
"Mts! ISSAM"

Nan Eesha ta gyara zaman ta tace
"Ohh haba" tayi mata wink.
Fido taja dogon tsaki tace
"Kina da damuwa wallahi. Tell me something?
" What?"
Fido ta ajiye plate na hannun ta tace
"He aiin't himself anymore"
Eesha tace "Ban ganeh ba? Kamar ya?"
"He ain't the Issam I used to know, ya canza mini gaba d'aya, his looks and everything. Tell me, meke damun sa?"

Gyara zama Eesha tayi tace
"Its a long story"
"Bani labari k'awata"
"Hmmm akwai wata yarinyan da yake so neh"

Dogon tsaki taja tace
"Dama duk wannan abun akan mace ce? Gaskia har naji kunya. Duk irin wannan girman kansa har mace zatasa ya shiga cikin wani yanayi? Bata son sane? Koh da yake macen da zata so Issam sai wanda batasan halin sa ba, a yau koh da tana son shi wallahi zanyi iya k'okarina dan ganin na raba su sabida Issam doesn't desearve to be love"

"Hmm yarinyan da yake hauka akanta bata ma san yana yiba. Kinsan me ake kira da UNREQUITED LOVE? Koh da a yau ya furta yana sonta toh a tunanin sa baza ta tab'a sonshi ba"

"Why?" A zuciyan ta kuma tunani take koh yarinyan tasan asalin sa wato d'an fashi, idan har ta sani toh dole ta nema yarinyan.

Eesha tace
"Tayi aure, but luckily for him mijin ta ya sake ta"
"Awww haba?"

"Eh sun rabu, but zan bashi shawara yanxu shine dai-dai lokacin da zaiyi approaching nata ya fad'a mata sirrin dake ransa"

"Ina yarinyan take, I desperately wanna met her" Fido ta tambaya

"You so stupid!!!! KECE ISSAM KESO, KECE ISSAM YAKE BURIN SPENDING REST OF HIS LIFE WITH! KECE RAYUWAR SA!"

By

Nana Fa'ad
*HAYATEEY*

Pure Moment Of Life Writers
[We don't just entertain and educate, we also touch the ❤ hearts of the readers]

_In dedication to Fido Sodangi_

{August, 2017}

Follow me on Wattpad @Nana_Faad. Do read my write-ups and please don't forget to SHARE/VOTE!!!

*HBD in advance my small sis Meenarh Parrot and Sadnaf wish you age with grace with Allah's khair now and always*

```Page 32```

Fido kallon ta take with so much surprise on her face, sai can ta fashe da dariya tace
"You must be kidding me right?"
Eesha ta b'ata rai tace
"I'm freaking serious Fiddausi, wallahi Issam yana mutuwar sonki. Mu bamu sani bama, Mum nasa ce tak'ira Faruk tace Issam ba lafiya, so har Abj yaje dan duba lafiyan sa. A time d'in Mum nasa take tambayar sa wacece Fido. Faruq ma was shocked lokacin data tambaye sa, shine ya mata bayani akan k'awata ce ke. So a time d'in mukasan dalilin ki Issam bashida lafiya, dalilin ki yashiga wani irin yanayi"

Fido zuciyan tane ya buga, zuwa kusa tayi da Eesha tace
"Tell me this is not true, tell me you're kidding me"

"Wallahi Allah da gaske nake"

"Tun yaushe yake so nah?"
"I don't know so I can't tell"

Ji tayi ta rikice gaba d'aya, tama kasa tunani. Jin sallaman da ake a k'ofa yasa Eesha ta d'au hijabin ta tace
"Bara na duba wake sallama"
D'aga kai Fido tayi ba tareda da ta amsa mata ba. She was so confused ta rasa me zatayi. Cusa hannu tayi cikin sumar kanta tace "Ya Allah help me"
Da sauri Eesha ta shigo cikin d'akin tace"Guess wanda yake sallama"
"Banson dogon surutu just tell me who?"

"Masoyin ki"
"What!"
"Issam neh, yazo neman Faruq nace masa baya nan kinsan abunda yace?"

"I don't wanna know please kibar zancen yaron nan"

"Cewa yayi yaga motar ki na miki magana ku gaisa"

"What? Kice bazan fito ba"

"Haba dan Allah sai kace k'aramar yarinya, please"

Da k'yar Eesha tayi convincing nata akan ta fita su gaisa. Hijabi dogo ta saka na Eesha ta fita.

Zaune yake a parlour yana karanta Magazine, jin motsin ta ya ajiye magazine d'in. Sallama tayi da hankali wanda bata tab'a tsammanin zaiji ba balle ya amsa
"Wa'alaykis Salaam"

Neman waje tayi ta zauna tana facing nasa tareda crossing leg. Kusan minti goma ba wanda yace k'ala a zuciyan ta cewa take anya wannan yana so na kamar yadda Eesha ta fad'a mini kuwa? Koh dai wani abun daman yake nema?

Tana cikin tunanin nan Issam yace
"Naji labarin abunda yafaru, so sorry for your lost ya hak'uri"

A hankali ta furta
"Mun gode Allah"

Daga nan kuma shuru ba wanda yace wani abu, wani dogon tsaki taja tace
"Please if you don't have anything to say can you please excuse me"

Kallon ta yake with so much tenderness in his eyes, kallon ba k'aramin kashe mata jiki yayi ba ya d'an yi murmushi ta gefe wanda ya k'ara fidda asalin kyawun sa duk da ya rame, yayi duhu yace

"Were you expecting me to say something? Akwai maganar da kike so kiji koh kin d'auka zan fad'a miki wani abu neh bayan wannan?"

Ranta neh yayi mugun b'aci tace
"No! Yaro irin ka ma what will I expect ka fad'a mini? N-o-t-h-i-n-g" tayi emphasizing word d'in.

Shuru yayi yana kallon k'aramin bakin ta, bai san ta yadda zai fara furta mata sirrin dake ransa ba. Wucewa tayi ta koma ciki ranta a b'ace, ta rasa yadda akayi Issam yake looking down on her.
Shigan ta d'akin ta cire hijabin tayi wulle dashi, Eesha ta kashe mata ido tace
" 'Yan mata ya akayi?"
Dogon tsaki taja tace
"Ki mantar da d'an iskan nan"
"Shhh dan Allah kiyi shuru karki bari yajiki"
"Allah sa ya jini, tsoran sa nake?"

"Shikenan magana ya wuce"

Fitan ta a d'akin yayi murmushi tareda tab'a k'irjin sa, ji yake yadda zuciyan sa ke bugawa fast
"Ina sonki ki Fido bansan ta yadda zan b'ullo miki ba, kece komai nah, kece rayuwata"

Washegari

Fido tasha hijabin ta har k'asa sai faman karkad'a key motar take
"Shamcy! Shamcy wallahi idan baki fito mun tafi ba zan fasa kaiki shopping d'in"
Nan Shamcy ta fito a d'akin tasha kwalliyar ta tayi kyau tace
"Adda Fido ya bakiyi make-up ba"
"Muje banson dogon surutu".
Tun lokacin da Basma ta rasu da mutuwar auren ta har yau bata k'ara kwalliya ba, koh kajal bata sakawa a idonta. Daga lipgloose shikenan. Tun lokacin tana cikin wani irin damuwa, tasan mutuwa da mutuwar aure duk daga Allah neh. Duk da bata son Aliyu amma zuciyan ta taji ba dad'i a lokacin da ya sake ta( duk yadda mace suke da mijin ta idan ya sake ta dole sai taji ranta yayi bak'i k'irin koh da bata sonsa)

Tafiya suke cikin motar ta har suka iso babban super market. Parking motar ta tayi suka shiga cikin shopping mall d'in. Shamcy sai d'iban abu take tana sakawa cikin basket Fido tace
"Wallahi idan kud'in ya wuce 20k bazan biya ba"

Lan k'wasar da kanta tayi tace
"Ayyah Adda Fido ba haka mukayi dake bafa"
"Kee nidai na fad'a miki"

Juyawan da zatayi kawai tayi kicibus da wani, cikin b'acin rai zatayi masifa kawai tayi ido hud'u da Issam, a hankali taja da baya. Shamcy tace
"Ahh Yaya Issam koh"
Murmushi yayi yace
"Ashe kin ganeh ni Baby"
Wani farin ciki taji daya kirata da Baby
"Eh mana ai dole, naje auren Yaya Faruq ai kuma kai ka kawo Adda Fido gida lokacin"
Cusa hannun sa yayi cikin sumar kansa yace
"Eh haka, I thought baki wayeni ba ai"
Kan Shamcy ta bada amsa tace
"Kee zo mu tafi inada meeting yanzu"
"Ohk Bye" Shamcy ta d'aga masa hannu tayi gaba, Fido zatabi bayanta ya rik'e hijabin ta ya kashe mata ido d'aya yace
"Ban ganeh bafa?"
"Baka ganeh me ba?"
B'ata rai yayi ya had'e giran sa yace
"You keep on following me duk inda naje, tell me why"
Kallon mamaki take masa wai tacika binsa
Yace "You are wasting my time my gurl"
Deadly look ta masa tace
"Don't call me that again, mesa ma zan bika?"
D'aga kafad'a yayi yace
"Nima shineh ban sani ba, but I don't like it ki daina kinji?"
Yayi wucewar sa ya barta, ranta neh yayi mugun b'aci nan taje ta biyan kud'in aka ce mata an riga an biya, hararan Shamcy tayi tace
"Mesa kika barsa ya biya?
"He insisted and there is nothing I can do"

Dogon tsaki taja tace
"Muje"

_Bayan sati d'aya_

Shamcy zaune take da Inna suna shan fruit salat sukaji sallama, hijabin gefenta ta d'auka tace shigo bismillah. Musa mai gadi neh yayi sallama ya shiga parlour yace
"Inna ana sallama da Shamcy"
Shamcy cikin mamaki tace
"Waye?"
"Issam wai"

Shamcy bud'e baki tayi she can't believe Issam yazo wajen ta, nan take tace "kace yashigo"
Chapter 20 · 0% Book details