← Book details Hayateeey Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 40

Sashe 24

Hayateeey Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwance yake akan kujera a parlour, ji yake zuciyan sa kamar an d'aura dutse mai nauyin gaske, duniyan ya masa zafi sai wasu zazzafan hawayen da suke sauk'a akan kuncin sa. Meena ce tayi sallama tashigo, dan tsaban bak'in ciki ya k'asa d'aga ido ya kalle ta, zama tayi a d'ayan kujeran da yake facing nasa tace
"Moon of my life inata jira kazo ka d'auke ni shuru, nata kiranka a waya baka d'auka wa what happen?"
Ji yake kamar ya tashe ya rufeta da duka dan bak'in ciki, ganin baida niyar amsa mata tace
"Moon of my life dakai fa nake"
Bud'e idanuwan sa yayi yana kallon ta, sai can da k'yar ya iya furta
"Ki koma daga inda kika fito"
"What! Me kake nufi?"
Wani tsawa ya daka mata yace
"Nace ki koma daga inda kike, kije na SAKE KI SAKI D'AYA"

Hankalin ta tashe hawaye yana sauk'a kan kuncin ta tace
"Yaya Aliyu mena maka? Mena maka da zaka d'auka wannan d'anyan hukunci?" Ta fashe da wani irin kuka.
Tasowa yayi ya d'auke ta daga ita har jakarta ya fitar da ita a gidan sa, ya nuna ta da yatsa yace
"Yanxu ba asara bibbiyu kikayi ba uku-uku kikayi. Na farkon shineh dalilin muguntarki 'yarki ta mutu, na biyu shineh mahaifanta kalau yake har koma tayi wani auren, na uku kuma shine mutuwar auren ki"
Meena fashewa tayi da wani irin kuka ta durk'usa ta kama kafan sa tace
"Dan Allah Yaya Aliyu ka taimaka mini, ka cece ni, kaine farin ciki nah, kaine jin dad'i nah, nasan na afka babban kuskure amma ka yafe mini wallahi zan gyara hali nah, wallahi ina k'aunar ka, ina masifan sonka, sonka neh sanadin abunda nayi, ka yafe mini dan Allah"
"Bazan tab'a yafe miki ba Meena, bazan tab'a yafe miki ba. Kin kashe mini 'yata, kin rabani da masoyiyata, kin rabani da farin ciki nah, kin rabani da Fiddausi wanda a yanxu ta mini nisa sabida haka bazan tab'a yafe miki ba"

Juyawa yayi ya shiga cikin gidan sa yaja door d'in. Kwanciya yayi a k'asan tiles yana mai wani irin nishi zuciyan sa kamar an zuba wuta. Tunanin irin wulakancin daya ringa mata yake, wasu zazzafan hawaye neh suke sauk'o wa yace
"Ki yafe mini Fido, wallahi ina sonki, ina matuk'ar sonki, koda da rana d'aya ban tab'a tsanan ki ba kawai maganar baki neh, gashi yanxu kin mini nesa".

S.A yace "Kin tabbata Fido, promise me you'll come back to me"
Fido tace "I promise In Shaa Allah"
Murmushi yayi yace "Nagode sosai Beauty, idan akwai abunda ya shige miki gaba just give me a call kinji? Ni bana k'auna ki zauna da wannan beast d'in"
"Karka damu beast d'in bazai mini komai ba, bakaga koh a film d'in Beauty and the Beast ba?"
"That's just a movie"
Fido tayi murmushi tace
"I know just kidding you, but karka damu In Shaa Allah bazai mini komai ba"
"Ohk zan tafi, take care"
"Aiit Thank you! Bye"

Fita yayi a d'akin, yana fita tayi ajiyan zuciya ta zauna ta bud'e kunun madaran da Dije ta kawo mata ta fara sha tana lumshe ido. Bayan ta gama sha tayi brush da alwala tayi sallah daga nan tabi lafiyar gado....

Washegari da safe bayan tayi sallah ta shirya cikin riga da skirt atamfa super mai kyaun gaske ta yafa mayafin ta, ba k'aramin kyau tayi ba. Mum ce tayi sallama tashigo d'akin tana murmushi tace
"Wow kinyi kyau"
Fido rufe fuskan ta tayi da tafin hannun ta tana murmushin k'arya. Mum ta kama hannun ta suka zauna bakin gado Mum tace
"Kinsan mai yafaru jiya?"
Girgiza kanta tayi, Mum tace
"Ina fad'a wa Issam an aura masa ke nan take ya farka, Fiddausi Issam yana sonki sosai dan haka ina rok'an ki dan Allah don't ever betray him cox it will break him into million piece of broken glass please"
"In Shaa Allah Mum"
Rungumeta Mum tayi tace
"Nagode 'yata, Allah miki albarka"

Daga nan driver ya kaita asibitin, tana shiga d'akin ta gansa kwance yayi uban rama kamar ba Issam ba, zuwa tayi kusa dashi tana mai k'are masa kallo
"Tun jiya na k'asa samun nutsuwa, ina cikin wani irin farin ciki mara misaltuwa, I can't really tell you how happy I am" tareda bud'e idon shi k'yar a kanta wanda tayi mugun tsorata dan ta d'auka yana barci, yace
"Don't move back Hayaateey! Come closer to me"
Tsayawa tayi cak a inda take, da k'yar ta iya bud'e baki tace
"How do you know nashiga d'akin kuma nice?"
Kirjin sa ya nuna mata yace
"Zuciyata, my heart! A duk ranar da zan had'u dake sai zuciyana ya fad'a mini, kinsan dalili?"
Girgiza kanta tayi, murmushi yayi yace
"Because you are my HAYAT! Kece RAYUWATA"

Rasa abun cewa tayi, kujera ya nuna mata yace
"Ki zauna please karki gaji da tsayuwa"
Ba musu ta zauna, kallon ta yake baya koh kifta ido, ganin kallon bana k'arewa baneh tace
"Ga breakfast na kawo maka"
Murmushi yayi yace
"Are you the one that cooked it?". Girgiza kanta tayi, yace
" Naso naci abincin da kika girka da kanki but duk da haka bai b'aci ba you will feed me with your own hands"
Had'a masa tea tayi mai k'auri da chips da kwai ta mik'a masa tace
"Kaci"
Murmushi ya mata yace
"Feed me with your own hands"
Had'a rai tayi tace
"Idan baza kaci ba ka barshi, ance mini you're critically sick baka iya koh magana nazo naga sab'anin haka"
Tasowa yayi ya zauna mai kyau yace
"Duk wanda ya fad'a miki haka toh da gaske neh, banida lafiya sabida rashin ki, but tunda na sameki ai na warke, yanxu garau nakeji"
Wani dogon tsoki taja tace
"Sai katayi ai, ashe zaka kwana da yunwa idan har ni zan baka abincin"
"Haka zakice?"
Koh amsa masa batayi ba ta d'au wayarta a jakarta ta kunna data ta fara chating abunta tareda tusa chewgum bakin ta tana kas-kakas. Ido ya zuba mata yana kallon ta, baisan dalilin dayasa yake jin sonta har cikin ransa ba. A haka har zuhur yayi baici abincin sa ba, wata Nurse ce tashigo d'akin bayan ta gama dubasa tace
"Kasha maganin ka yau kuwa?"
"Eh nasha but yanxu ina jin dizziness sosai"
"Kaci abinci?"
"A'a"
"What! Bakaci abinci tun safe ba? Why? Wannan datake zaune take danne dannen waya wacece da bazata baka abinci ba?"

Murmushi yayi yace
"She's my wife"
"Matar ka? A'a dai wasa kake mini ai ba matar da zata bar mijin ta da yunwa koh lafiyan sa kalau balle kai da baka da lafiya"
Wani mugun harara Fido take masa, Nurse d'in zama tayi ta d'eba abinci zata basa a baki ya girgiza mata kai yace
"Mik'o mini kawai zan iyaci da kaina"
"Zaka iya?"
"Zan iya don't worry"
"Ohk toh ba komai"

Tasowa Nurse d'in tayi tace
"Issam dear please next time kar a turo masu aiki haka wanda basuda aiki sai na chating bayan an biyasu dan suzo suna kula da mara lafiya"
Wani uban tsaki Fido taje tama rasa mai zatace idan ba rainin hankali ba taga tayi kama da mai aiki neh, Nurse d'in bata kula Fido ba tace
"Issam dear sai anjima"
Murmushi yayi yace
"Nagode sosai, bye"
Tana fita ya fashe da dariya Fido kuma sai hararar sa take tace
"Wallahi nan gaba idan ta kuma ce ni 'yar aiki sai ta raina kanta, after all gwara ma ta d'auke ni 'yar aiki akan ta yarda ni matar ka"
Kallon ta ya tsaya yi yace
"Sabida meh? Sabida kinfi k'arfin a k'iraki da matata?"
"Eh" ta basa amsa a takaice, murmushi yayi yace
"I am proud to call you my wife, so very proud. Ina alfahari dake, bazan tab'a gajiya da godewa Allah daya bani ke a matsayin matata ba, inaso ki sani ina sonki kuma zan jure duk wani wulak'ancin da zaki mini, ina ji a raina wata rana zaki soni, zaki soni fiye da yadda nake sonki!"
Wani dogon tsaki taja tace
"Wallahi bazan tab'a sonka ba, you have no idea irin abubuwan dana tanadar domin ka sabida haka kar kace zaka juri duk wulak'ancin da zan maka sabida bazaka iya ba"

Kuyi hak'uri kunji ni shuru kwana biyu wallahi zirga zairgan asibiti nake Anty nah ba lafia

#MunaMugunTare❤

By

Nana

Fa'ad
*HAYATEEY*

Pure Moment Of Life Writers
[We don't just entertain and educate, we also touch the ❤ hearts of the readers]

_In dedication to Fido Sodangi_

{August, 2017}

Follow me on Wattpad @Nana_Faad. Do read my write-ups and please don't forget to SHARE/VOTE!!!

```Page 38```

Murmushi yayi yace
"Wow! So much hatred! Why?"
Koh basa amsa batayi ba ta tashi tashiga toilet tayi alwala, shima tashiwan yayi da k'yar ya shiga toilet dan alwala. Bayan duk kansu sun idar Dije ta kawo musu abinci ta gaishe su tace
"Ni zan koma gida Allah k'ara sauki"
"Ameen nagode Dije" Fido kuma koh k'ala bata ce ba, Dije tana fita a d'akin ta janyo tray na abincin ta d'eba iya wanda zata iyaci tafara ci abunta, Issam kam sai kallon ta yake yana murmushi, bayan ta gama ci yace
"Nima ki zuba mini naci"
D'auko wani plate zatayi ta zuba masa yace
"Zuba mini a plate da kika ci"
Ba musu ta zuba masa ta mik'a masa, yana ci yana kallon ta abun haushi yake bata, dogon tsaki taja tace
"Wai cin abinci kake koh kallo na? Wallahi na tsana kallon nan kallo sai kace maye"
"Kika sani koh mayen neh?"
"Ahhh kam gaskia ba shakka dan kayi kama da su"
Murmushi kawai yayi ya cigaba da cin abincin sa itama sai faman chating take da wayar ta.
Chapter 24 · 0% Book details