← Book details Hayateeey Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 40

Sashe 34

Hayateeey Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Shiga d'akin ta tayi tana tunanin ashe fa Issam bai sake taba, rufe kofan d'akin tayi ta zauna dirshan a kasa ta rushe da wani irin kuka, a yanzu take dana sanin abunda ta masa. Nan take ta ciro wayarta ta latsa number'n Kbad
Yana d'aukawa tace "Kun aikata aikin neh koh kuwa"
"Tun yaushe Hajiya ai yanzu nashi ya k'are". Katse wayan tayi ta k'ara rushewa da kuka, Inna sai bubbuga k'ofa take akan ta bud'e kofa amma tak'i, Shamcy ma tayi bugun duniya taki ta bud'e. A k'arshe suka kira Mummy suka sanar da ita abun da ake ciki. Cikin fifteen minutes sai gashi tazo gida, buga kofan take tace
"Habibty ki bud'e mini kofa Mummy ce, idan baki fad'a mini damuwar kiba mawa zaki fad'a?" A haka ta mata dad'in baki ta bud'e mata kofa. Tana bud'e wa ta fad'a jikin Mummy ta kuma rushewa da sabon kuka, Mummy kuma sai lallashin ta Tamshi, a haka har ta lallashe ta tayi shuru. Bayan duk sun zauna Inna tama Mummy bayanin abun sa Fido ta fad'a mata, Mummy tace
"Habibty wannan k'arya kikayi, nasan halin Issam yana sonki sosai bazai miki haka ba ki fad'a mini gaskia meya had'a ki dashi?"
Fido muryan ta yana shacking ta fara zano musu tun daga farko har binsa datayi UK har abunda yafaru a yau. Salati Mummy tayi ta wanke ta da wani irin mari wanda yasa taga stars tace
"Kin bani kunya kin bani mamaki, sai kace niba uwarki ba. Nida nake zaman matar shi na barwa Allah komai ranar gobe zamuyi hisabi dasu balle ke yarinya k'arama, how are you even sure eh shi d'in neh? What prove do you have? Da dagaske kike ai da kin fad'a mini muyi sueing nasa a court. Wannan ba daidai baneh sam"
Durk'usawa tayi gaban uwarta tayi tana kuka tace
"Mummy ki yafe mini nasan banyi dai-dai ba, I made a very big mistake Mum. Mummy inason Issam fiyeda komai a yanzu, but nayi alkawarin zanga bayan shi and I can't live with mutum da shine sanadiyyar mutuwar mahaifina, Mummy I can't" ta kuma rushewa da wani kuka, Mum tace
"Yanzu abunda zakiyi ki kawo mini evidence akan shiya kashe mahaifin ku idan ba haka ba bazan tab'a yadda dake ba"

Tasowa tayi ta d'au safe d'in ta latsa password d'in kamar yadda ya fad'a Fiddausi sai gashi kuwa ya bud'e. CD plates biyu neh a ciki, d'auka d'aya tayi ta saka a DVD tayi playing

****************
Six Years Back

Alhaji Babangida Badamasi (Mahaifin Issam) zaune akan kujera a parlour'n sa yana duba wasu files, Yaya Ahmad neh yashigo cikin parlour'n suka gaisa, bayan sun gaisa Yaya Ahmad yace "Umm daman Uncle neh ya aiko ni wato ka amince da deal d'in?"
D'aga kai Alhaji Babangida yayi yace
"Haba dai ya Muhammadu zai mini haka? I told him several times wannan abunda sukeso na musu da governor bazai yuba, bazan iya bud'e musu wajen nan ba sabida budget na talakawa neh His Excellency ya bani a hannu na, nasan Muhammad bayin kansa baneh governor neh yake zuga sa"
Cire bindiga yayi yace "Tunda baka yarda da deal d'in nan ba sukace na kashe ka na cire yatsan ka kaga easily zamu bud'e wajen"
Tsaki yaja yace "You people ain't serious kun d'auka zaku iya tsoratar dani neh?"
Dariya Yaya Ahmad ya fashe dashi yace
"Mesa zamu tsoratar da kai ehhh? I am freaking warning you for the last time"
Tsawa ya daka masa yace "Get out of my house now!"
Murmushi Yaya Ahmad yayi yace
"Say your last prayer"
"I said getout!"
Nan Ahmad ya harb'esa ya gutule yatsan shi ya fita a gidan da gudu...

***************

Salati Mummy tayi tace
"Ashe daman Issam yaron marigayi Babangida neh? Ikon Allah! Wallahi ban tab'a sanin matar shiba dan kullum tana garin su Yamen batason zama a nigeria"

Fido kuma kanta neh ya d'aure ta rasa ganeh gaskiyar maganar, nan ta k'ara cire d'ayan CD plate d'in, ganin paper tayi nan take ta ajiye CD ta bud'e paper'n, bud'e paper tayi ta fara karantawa

_Hayateey my heart is telling me kamar kin ganeh ni you just agreed to marry me so that you can avenge the death of your beloved Dad but believe me wallahi Allah banje gidan ku da niyyar kashe mahaifinki ba. Da farko na d'auka shiya turo yayan ki Ahmad akan yazo ya kashe Dad d'ina that's why nayi alkawari sai na rabasa da dukiyan sa tunda naga yana bala'in son kud'i not knowing that shima baisan da zancen ba. But I want you to know that I love you sooo much!!!!_

Wasu zafafan hawaye neh suke sauk'a akan kuncin ta, ashe shima haka aka kashe mahaifin sa?. A take ta taso tsaye tayi gudu tashige d'akin ta Mummy da Inna sai kiranta suke amma koh ta kulasu. Fitowar ta sai ga hijabi da key na mota a hannun ta, Mummy nan take ta bita itama tana cewa "Mamana ina zuwa karki yarda ki fita a gidan nan yanzu k'arfe sha biyun neh"
Fido koh sauraron ta batayi ba ta shige motarta ta danna wani irin horn nan take mai gadi ya bud'e mata gate ta fisga motar. Wayarta ta d'auko ta latsa number Kbad tace
"Kbad har yanzu kuna wajen?"
"A'a fa bama wajen but kan mu aikata mishi ya bamu wasik'a mu kawo miki yanzu muna hanyan gidan ku ma"
Ganin motar su Kbad tayi nan ta musu full light tareda danna musu horn suka tsaya. Parking motar ta tayi ta fito a motar ta tasame su, tace tana hawaye tace
"Ina wasik'ar"
Mik'a mata sukayi ta juya tashiga motar ta, kunna wutar motar ta tayi ta bud'e letter d'in wanda duk jini ya d'an b'ata taga

*Ni Issam Babangida na sake matata Fiddausi Muhammad Sodangi saki d'aya*

Nana

Fa'ad
*HAYATEEY*

Pure Moment Of Life Writers
[We don't just entertain and educate, we also touch the ❤ hearts of the readers]

Written By Nana Fa'ad

_In dedication to Fido Sodangi_

{Sept., 2017}

Follow me on Wattpad @Nana_Faad. Do read my write-ups and please don't forget to SHARE/VOTE!!!

```Page 47```
Chapter 34 · 0% Book details