← Book details Hayateeey Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 40

Sashe 30

Hayateeey Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Bayan sunje gida kowa ya wuce side nasa, ita tayi sallah a gida shi kuma yaje masallaci bai dawo ba sai bayan isha'i. Zaune take a d'akin ta tana danne-danne da wayarta yayi sallama yashigo d'akin, guntun tsaki taja tace
"Kai gaskia anyi asarar ilimi, wai mutum bazai iya jiran a amsa masa sallama kan yashigo ba?"
"Ai naga gida na kuma d'akin matata nashiga"
"Dan haka bazaka iya jiran a amsa maka sallama kan ka shigo ba?"
"Yeah wifey"
"Mtswww toh mai yakawo ka d'aki nah?"
"Yunwa nakeji"
"Sai kuma aka ce maka inada abincin da zan baka?"
"Dafa mini zakiyi"
Kallon uku saura kwabo ta masa tace
"Nice zan dafa maka abinci? Allah sawwaka"
"It's your responsibility ai as my wife"
"Stop it, karka k'ara ce mini ni matar ka abun b'ata mini rai yake"
"You have to accept that da kinki da kinso, ina ji a jiki nah watarana zaki soni fiye da yadda nake sonki, gwara ki fara nuna mini so tun yanzu before na mutu, kar yazama miki so late watarana kina dana sanin mesa baki nuna mini so da kauna ba"
"Allah sawwaka, a yau idan ka mutu cewa akayi zai dame ni? Dan Allah fita mini a d'aki banson surutu dayawa"
"Abincin fa Hayateey?"
"Banda abinci kuma bazan iya girka wa ba"
"Yunwa fa nakeji"
"Sai kazo ka cinye ni ai nasan dagasken yunwa kakeji"
"Na cinye ki?" Ya k'ara tambaya yana wani irin murmushi, nan take ta d'aga kanta tace
"You really have a dirty mind, I beg you please don't think otherwise"
Murmushi ya koma yi ya taso daga kan kujeran sa yaje daf kusa da ita, ita kuma tana ja da baya, yace
"Na cinye ki koh?"

By

Nana

Fa'ad
*HAYATEEY*

Pure Moment Of Life Writers
[We don't just entertain and educate, we also touch the ❤ hearts of the readers]

Written By Nana Fa'ad

_In dedication to Fido Sodangi_

{Sept., 2017}

Follow me on Wattpad @Nana_Faad. Do read my write-ups and please don't forget to SHARE/VOTE!!!

```Page 44```

*Wishing you all a happy sallah, May we witness many many more*

Ja da baya take shi kuma yana matsowa kusa da ita yana wani irin murmushi yace
"Kikace na cinye ki koh?"
"Kayi misunderstanding d'ina please"
"Kamar ya? Kikace na cinye ki ai kuwa zan cinye ki, koh ban samu na cinye kiba nasan koh latsan ki nayi zanji na k'oshi"
"Kayi hak'uri please ka barni nayi maka alkawari zan dafa maka koh indomie ne"
"No ai ke zakifi Indomie taste"
Wani deadly look ta masa tace
"Kamar ya?"
"Oshh! I mean zakifi Indomie d'and'ano"
"Ai ba turancin akace maka bana jiba, nidai please ka matsa banson kayan k'azanta"
Matsowa yake ita kuma tana ja da baya har takai jikin bango, yace
"No where to escape now Hayateey"
"Please don't do anything stupid"
"Ain't doing anything stupid I just wanna.."
"You just wanna what???" ta fad'a tsawace, zai k'ara matsowa ta turesa da hannun ta, hannunta ya kama ya rik'e gam wanda bazata iya kwatar kanta ba, lips nata ya had'a da nasa yana kissing passionately, duk iya k'okarin ta na hanasa amma ina yafi k'arfin ta
Sanda yagaji dan kanshi yabar ta yace
"Yanzu na d'an ji dama-dama duk dama ban cinye ki d'in ba"
"Allah ya isa na k'azami kawai"
Chapter 30 · 0% Book details