← Book details Hayateeey Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 40

Sashe 36

Hayateeey Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A lokacin da Fido tabar d'akin Issam ta cewa su Kbad su aikatar da aikin data saka su d'aukan adda Kbad yayi yace
"Alhaji kayi bye-bye da jin dad'in duniya"
Wani yanka ya masa a hannun sa shineh dalilin dayasa yayi k'ara sosai dan yashige shi komai, Kbad ya b'arga boxers nasa ya d'aga gaban sa zai fara yankawa kenan Issam da k'yar ya iya furta
"Zan muku doubling kud'in data baku"
Kwashewa da dariya sukayi d'aya daga cikin su yace
"Kasan nawa aka bamu kuwa? Naira na dukan naira har dubu d'ari"
"Zan baku dubu d'ari biyu ku kunce ni"
Kbad koh sauraron sa baiyi ba ya aza adda akai yaja sai ga jini yana malala, dariya sukayi sukace
"Wanna soma tab'i neh, next kawai idan mun aza akai bazamu cire ba sai mun rabashi kashi biyu"
Suka k'ara rushewa da dariya, 'yan sanda neh suka shigo d'akin suka nuna musu bindiga. Ba k'aramin tsorata sukayi ba dan a rayuwar su sun tsana 'yan sanda koh sojoji. Da sauri d'aya daga cikin police d'in ya d'aura wa Issam wajen yana masa sannu. Haka 'yan sandan sukayi arresting 'yan daban kusan su goma suka saka su a motar su, Issam da k'yar ya iya furta yace wa inspector d'in yace
"Taya kuka san ina cikin wannan yanayin?"
Inspector Tukur yace
"Wannan baiwar Allah'n ita tazo ta sanar damu mu kuma mukazo cikin gaggawa"
D'aga idon da Issam zaiyi yaga yarinya kyakkyawa ajin farko wanda ak'alla bazata haura shekaru ashirin da biyar ba, fara sol ce ga idon ta dara-dara, hancin ta tsit kamar pencil sai bakin ta madai daici. With so much surprise Issam yace
"SALALA?"
Murmushi tayi tace "Ya Issam don't stress yourself muje asibiti"
"Tell me yakika sani?"
Ajiyar zuciya tayi tace
"Tun da rana nazo ni gidan na maka surprise visit naji tana waya, na kiraka a waya har na gaji baka d'aga ba a k'arshe nayiwa 'yan sanda waya bayan munzo gidan kuma mai gadi yace kun fita, haka muka ta neman ku a gari daga baya kuma muka dawo gidan"

"Nagode Salala"
"Anything for you broh"

Suna haraban gidan gaba d'aya Fido ta kira Kbad a waya, har d'aya daga cikin police d'in zaiyi receiving Issam ya hana yace
"Ku barshi yayi picking and kayi pretending baka tareda 'yan sanda kuma kace mata na baka letter ka bata"
Haka Kbad yayi receiving call d'in
Yace "tun yaushe Hajiya ai aiki ya k'are" zai cigaba Issam yayi masa nuni da hannu akan yayi shuru itama already ta katse wayan. Haka sukayi plan akan su Kbad su shiga motar su sukai mata takardan saki idan yaso sun bata sai su wuce dasu police station. Police d'in sunyi suyi arresting nata amma yahana. Tun a mota ya rubuta mata saki d'aya wanda koh kad'an bawai dan yaso ba sabida kawai bata sonshi and bazaiso ya zauna yana cutar da ita batason shi ba and duk da yana sonta bazai iya cigaba zama da ita ba. Suna hanyan gidan su Fido ta k'ara kiran Kbad a lokacin Kbad yake sanar da ita Issam ya bata sako. A idon su Issam Kbad ya bata letter harta shiga cikin motar ta....

Asibiti direct aka wuce dashi daga nan aka masa taimakon gaggawa aka d'inke wajen. Doctor daya d'inke ya kira Salala gefe lokacin kusan k'arfe biyu, bayan sun gaisa yace mata
"A gaskia an samu matsala dan yanzu possibility da zai haihu is 40% but akwai Allah In Shaa Allah zai iya producing egg"
Zuciyan Salala ba k'aramin bugawa yayi ba tace
"Yanzu Doctor idan na d'auke sa na kaisa India fa? Akwai wani friend nah likita neh sosai he's good in this field"
"Ohk ba komai zaki iya kaisa can"

Tun a dare take waya take neman flight na India, akace mata sai jibi zai tashi a Lagos, haka ta nema na Abuja da k'yar wajen wata friend nata da take aiki a Umaru Musa airport. Da asuba ta kira abokin sa Faruq sukaje su airport k'arfe bakwai cif jirgin su ya d'aga zuwa Abuja kuma a k'arfe goma jirgin da zai kaisu Lagos zai tashi.

Mum har zub da hawaye tayi dataji abunda Fido ta shiryawa d'anta, a gaggauce suka shirya kayan su zuwa airport. A k'arfe goma dai-dai jirgin da zai kaisu Lagos ya d'aga.......

***************************

Fido haka ta ringa shafan pictures d'in tana kuka, a k'arshe zube kasa tayi bacci mai nauyi ya d'auke ta...

_Washegari_

Ita bata tashi a bacci ba sai k'arfe goman safe, a yanzu ta d'an ji kanta yayi sauki kad'an amma jirin har yanzu yana nan. Duba agogon jikin bango tayi taga 10:05, da sauri ta taso daga kwance tace
"Subhan' Allah". Wani relief taji data tuna tana fashin sallah, da k'yar ta iya ta cire kayan ta, bud'e wardrobe nashi tayi ta d'au towel ta d'aura. Kwasan kayan ta tayi ta wanke su tas ta shanya a toilet d'in tayi wanka.
Haule ce tayi sallama tashigo d'akin da tray a hannunta ta dira a k'asa, bayan sun gaisa Haule tace
"Hajiya kinsha bacci koh?"
Murmushi Fido tayi tace
"Wallahi nasha bacci har naji ciwon kaina da d'an sauki"
"Ai dole, naga yanayin ki jiya shiyasa na had'o miki da maganin bacci"
Zaro ido Fido tayi tace "Haba shineh baki fad'a mini ba?"
"Na d'auka kin ganeh su neh ai kiyi hak'uri ashe sha kawai kikayi"
"Karki damu ba komai"
Jan tray d'in tayi zuwa gaban Fido tace
"Ga abinci nan"
Murmushi Fido tayi tace
"Haba Haule nasa ki wahala haka?"
"Ahhh haba dai wani wahala, ba wani wahala wallahi. Ni zan d'an fita sai na dawo"
"Toh sai kin dawo"

Bayan Haule ta fita ta bud'e abincin fried yam neh da kwai, wasu zazzafan hawaye neh suka fara sauk'a kan kuncin ta, Issam neh ya dawo mata akai dan bashida abincin da yakeyi da safe sai fried yam da kwai tace *" I miss you Issam"*. Haka tana cin abincin tana hawaye. Sallama taji da sauri ta d'aga kanta, ganin Mummy da Mami tayi, da gudu taje ta rungume Mummy tana wani irin kuka mai tsoma zuciyan duk wani mai sauraro tace
"I had gotten so used to seeing him everyday, that now he was gone, the house was painfully and obviously quiet"
"Shhh kiyi shuru Habibty In Shaa Allah zaki samu Issam ki daina damun kanki"
Haka sukaita lallashin ta tayi shuru, daga baya sukace ta shirya zasu koma gida, duk yadda tayi akan su barta zata zauna suka k'i. Haka ta bisu zuwa asibiti aka rubuta mata magani aka sallame Yaya Khaleal suka d'au hanyan KT. Su basu isoba sai da yamma likis, suna sauk'a a motar 'yan gidan suka fara fitowa d'aya bayan d'aya suna lek'a su. Itadai bata kulasu ba tashiga cikin gida......

**********************
_Bayan Kwana Biyar_

India
New Delhi

Taj Mahal Hospital

A wani babban d'akin cikin asibitin Issam neh kwance akan gado Mummy kuma zaune a gefen sa tana had'a masa shayi, bayan ta had'a ta mik'a masa ya karb'a yafara sha, Mummy murmushi tayi tace
"Yanzu jikin da sauki koh?"
"Sosai Mummy ai na warke saura mu koma gida"
"Nikam mene kabi ka damu mu koma gida, daganan fa sai Yemen"
Had'a rai yayi yace "Mummy Yemen kuma?"
"Sosai kuwa kuma zamu kai kusan wata shida haka"
Nan take ya ajiye cup d'in shayin hannun sa yace
"Mummy har wata shida? Toh business namu fa?"
"Akwai managers ai and suna alerting naka komai"
"Mummy ni gask...." Bai k'arasa ba ta tare numfashin sa tace
"Nasan dalilin dayasa kake son komawa Nigeria, toh wallahi bari kaji na rantse da Allah wallahi Allah idan ka maida Fiddausi bani babu kai, kai koh na mutu ban amince ka aure taba"
Zuciyan sa ne yayi mugun bugawa, bai san lokacin da ya taso ya kama hannun Mummy ba yace
"Dan Allah Mummy karki mini haka Mummy.."
"Shhh idan ka k'ara mini zancen ta ban yafe ba, yarinyan da take neman halaka ka, yarinyan data tsaneka, yarinyan datake son ganin bayan ka, ka fad'a mini wani irin mutum neh zai maka haka idan ba babban mak'iyin kaba"
Shuru yayi ya zuba rinannun idanuwan sa yana kallon ta
"Fad'a mana! The truth is always bitter nasani but ni mahaifiyar kace kuma nace BAKAI BA ITA HAR ABADA, muna komawa Yemen za d'aura auren ka da Salala faqat!"
Komawa gado yayi ya kwanta tareda rufe eyes nasa da k'yar ya iya furta
"Allah sa hakan shine mafi alkhairi Mummy"
Murmushi tayi tace
"Ameen Son Allah maka albarka"

_Bayan wata biyu_

Fiddausi ba k'aramin lalacewa tayi ba, ta daina fita aiki ta daina zuwa ko ina kullum tana aikin kuka. S.A yayi×2 da ita akan tunda ba idda akanta a d'aura musu aure amma tak'i. A koh wani bayan kwana biyu take zuwa Abuja koh sun dawo amma kullum amsar d'aya neh basu dawo ba..

Kamar koh wani bayan kwana biyu yau ma tana Abuja cikin gidan su Issam ta saka mai gadi a gaba tana masa kuka tace
"Dan Allah ka taimaka ka bani number sa dan Allah"
Wani irin tausayin ta Haule taji dan kowace rana idan tazo tana rok'on number'n su amma basu tab'a bataba dan Mummy tace kar a bawa kowa number'n. Haule tace
"Fiddausi a gaskia bamuda number'n mai gidan ki amma munada number Hajiya"
Da sauri Fido tace "Ku taimaka mini ku bani dan Allah"
Haka suka bata number'n nan take ta latsa, ringing d'aya biyu Mummy tayi picking, nan Fido ta taso tsaye tana farin ciki tace
"Mother ina yini, dan Allah Fiddausi ce, dan Allah karki katse wayan ki saurare ni"
Kit Mummy ta katse wayan, haka ta ringa trying amma bata picking. Daga baya ta d'au jakarta ta musu godiya ta shige motar ta wanda yanzu ta d'au driver musamman wanda zaina kawo ta Abuja yana maidata gida KT.....
Chapter 36 · 0% Book details