← Book details Hayateeey Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 40

Sashe 5

Hayateeey Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata mota Ferrari GTO bak'a ce tayi parking a gabar school d'in, kusan minti biyar shuru ba'a bud'e motar ba sai can General Aliyu Sanusi Sodangi ya bud'e motar yafita ya zagaye b'angare d'aya side na motar ya bud'e kofa. Kafarta d'aya d'auke da high heel bak'a tafara saukewa kan kusan seconds goma ta sauke d'ayar kafan. Straight skirt bak'i neh ajikin ta sai dogon top iya gwiwan ta shima bak'i tayi rolling gashinta da veil bak'i. Tsoki yaja yace
"Dole nah gyara lock nah kofan nan bazaiyu ina bud'e miki kofa kullum ba sai kace driver ki kuma Wlhy nan gaba idan nakara kallon ki da irin wannan heel d'in saina tattaka ki" itadai batace masa komai ba ya shige motarsa yayi gaba. Ciro wayan ta tayi a cikin jakar ta tareda dialing number k'awar ta Eesha, ringing d'aya Eesha ta d'auka tace
"Kibani just 10mins yanxu zaki ganni" Fedo jan tsoki tayi kawai ta katse wayan ta.

Kalle kalle take a makarantan har idon ta yakai kan wani Shop an rubata '''COFFEEHOUSE''' a hankali ta taka har cikin coffeehouse d'in tayi ordering Coffee, bayan an kawo mata Seat data zauna sam baiyi mata ba wani yaro ya kura mata ido gashi wajen kusa da window tanajin sanyi. D'auka coffee cup nata tayi tareda tashiwa a seat d'in dan ta koma seat na baya. Tafiya take a hankali tayi missing step gashi dogon takalmin dake kafan ta zube luuu zata fad'i taji an kamota

Bud'e idon ta tayi a hankali dan ganin wanda ya kamota, ido hud'u tayi da ISSAM. Fuskan sa a murtuke yake kallon ta
"Astagfirullah" yayi mumbling, take ta gyara tsayuwan ta fad'a a hankali
"As if baya committing sins more than tab'a mace" taja wani dogon tsoki. Tsayawa yayi yana kallon ta dan kamar yaganeh ta but wata zuciyar nace masa ba ita bace ai wancan kabarta a Nigeria. Juyawa tayi zatayi tafiyar ta yaje gyalen ta yace
"Are you insane, next time you should watch where you're going plus you can't even open your filthy mouth and say thank you kina jan tsoki, I really hate that" ranta idan yayi duba ya b'aci wai 'filthy mouth' ranta b'ace tace
"How dare you!!!! How dare you open your big mouth and insult me kuma kana wani magana bance thank you ba. Why should I even say thank you to a person who bumped into me last month and he can't even say sorry"

Kallon ta ya tsaya yakeyi dan yanxu yakeda tabbacin itan ce, sai can yace
"Just be glad I'm not making you pay for my Suit and ban buge bakin kiba" kallon jikin sa take taga ashe coffeen duk ya zube a maroon Suit nasa , kuma Coffee nada d'an karen zafi. Juyawa yayi yayi tafiyarsa ya barta tsaye..... Cizon yatsan ta tayi tace ISSSAM kenan muna nan da kai

Wayarta neh yafara ringing ta d'auka da wuri tace
"Wlhy Allah Eesha baki kyauta mun ba ina wani Coffeehouse opposite Whey Libry" nan da minti biyar sai ga Eesha tazo, yarinya ce sa'ar Fido chocolate colour siririyace sosai kuma tanada tsayi, ba laifi tanada kyau iya gwargodo. Hugging na Fedo tayi tace
"Gurl been a while, tun time da muke service fa" had'a rai Fedo tayi tace
"And so? Shineh zaki shanya ni for almost an hour yanxu"
"Very sorry my love"
"Don't call me that OK!"
"Kiyi hakuri toah Fiddausi"
" please next time karki k'ara, you know I am new here yaarrr"
"Kefa banza ce Allah sa karki hakura"

Haka sukaita yawo da Eesha tagama nuna mata makarantan tareda kaita department nasu, a yau tagama duk abunda yakamata ta gama ita bata dawo gida ba sai karfe taran dare. Tana shiga taci karo da Aliyu a parlour yana danne danne a laptop nasa. Gaishe sa tayi ba tareda ya amsa ba yace

"Sai yanxu?"

Eh kawai tace tareda kokarin shiga d'akin ta, daka mata tsawa yayi yace

"Ain't done with you gurl da zaki wuce, tun d'azu nake kiranki mesa baki d'auka ba?"

"Banji ba wollah wayar na Silent"

"And you can't call back"

"Sorry ba kud'i a wayar shiyasa"

"And kinfi karfi ki kirani da wayan Eesha koh? Lemme tell you one thing nan gaba idan kika kai karfe shida a waje sai jikinki ya fad'a miki. Very stupid girl kawai" tura bakin ta tayi ace da girman ta shekaru ashirin da hud'u tana neman shiga na biyar nan da wata shida amma ace za zaneta, lallai ashe za'aga drama, kai baima isaba. Shiga tayi cikin d'akinta ta watsa ruwa dan tana fashin sallah, shafa cream tayi ajikin ta tareda saka dogon kaya da cardigan akai dan garin ana sanyi sosai. Kunna heater na d'akin tayi dan yayi warming d'akin cox yayi sanyi sosai amma warmer bayayi. Dogon tsoki taja tareda d'aukan laptop nata da wayanta tazo parlour ta zauna, a lokacin Meena tana manne ajikin Aliyu ita a dole tana masa shagwab'a. Tayi niyan ta koma ciki amma wata zuciyar tace zauna kiga ikon Allah. Zama tayi daram a gabansu tana facing nasu, mugun kallo Aliyu ya mata amma hakan bai hanata zama daram ba. Meena kuma ganin haka yasa ta k'ara zagewa tana kissing nashi shima yana biye mata, ganin abun nata yana son wuce gona da iri yace
"Ummm Meeenah bari nagama aikin nan tukunna"
Inaa ita kuma sai k'ara narke masa take, tsawa ya daka mata yace

"Please just leave me alone". Ranta idan yayi dubu ya gama b'aci, Fedo sai dariya take a hankali wanda ya k'ara kular da Meena. Tashiwa tayi tashiga ciki a fusace, ran Fedo kuma yayi fari kal sai murmushi take tana danne danne da laptop nata. Aliyu neh ya daka mata tsawa yace
" Dan Ubanki dariyan meh kike kuma what's the reason zakizo kisani a gaba kina kallo nah"

"Warmer d'aki nah baya aiki kuma wollah akwai sanyi shiyasa" tsoki kawai yayi yacigaba da aikin gaban sa.

Can yunwa yaci karfin ta tashiga kicin koh zata samu abun sakawa a baki amma shal ba komai tace
"Kut!!! Yarinyan nan yar iskace bata ajiye mini abinci ba mtswww" kunna gas tayi ta dafa indomie wanda yaji atargu ta zuba a plate ta kawo parlour. Cigaba da aiki take a laptop nata duk hankalin ta yana kan binciken da take akan Issam tana d'an tab'a Indomie ta. Aliyu kamshin Indomie yariga yagama cika masa hanci yanata had'iye saliva yaga ina idan baici bafa akwai matsala.
D'aga idonsa yayi yana kallon ta gaba d'aya hankalin ta na kan laptop d'in ga left hand nata wanda ta tusa shi a cikin dogo bak'in gashin ta. Zuwa yayi da hankali ya d'auka plate d'in indomie ba tareda da tasani ba danma Tv yana aiki ya kura volume balle taji karan tafiyan sa......
*HAYATEEY*

Pure Moment Of Writers(p.m.l)

Written By Nana Fa'ad

_In dedication to Fido Sodangi_

{July,2017 }

```Page 12```

D'aukan plate na Indomie yayi ahankali yawuce kitchen ya juye a plate ya b'oye a wardrobe yak'ara zuwa parlour ya ajiye mata plate d'in. Duk abunda yayi bai wuce secs talatin ba. Zama yayi a kujera ya had'a rai yana aikin sa, Fido kuma juyawan da zatayi ta d'eba Indomie taga wayam ba komai a plate d'in. Juye juye tafara tagafa su biyu neh a parlour kuma tanada tabbacin ba ita ta cinye ba dan Indomie da zafi kuma ga zafin pepper. Ihu tayi ta tashi a wajen tazo dab kusa da Aliyu tace
"Wlhy Yaya akwai aljani a gidan nan, na ajiye indomie kan na juya sun cinye" wani tsawa ya daka mata yace
"Kee kishiga hankalin ki bawani aljanu da suke gidan nan, tun d'azu naga kina cin Indomie kuma yanxu kice aljanu neh suka cinye, kinadai daci kamar gara"

Itadai duk jikin ta yayi sanyi dan tasan ba ita ta cinye abincin ba tace
"I swear Yaya Aliyu wlhy Allah ban cinye ba"
"Just sharrrapp I don't wanna hear anything idan bake kika cinye ba toh ubanwa ya cinye Stupid gurl"
"Ohk fine, nagode"

Jiki a sanyaye ta kwashe laptop nata da wayarta tashiga d'akin ta. Duk da haka hankalin ta bai kwanta ba tsoro duk ya mamaye ta. Tana shiga d'akin ta Aliyu ya tashi da sauri ya nufe kitchen ya d'auko Indomie ya ajiye a dinning yafara ci. Da k'yar ya iya yaci dan yaji ahaka yana had'awa da Juice meh sanyi yana wayyoo Allah nah yaji yarinyan nan tana son kashe ni washhhh....

.....Washegari.......

Tun kusan karfe takwas Aliyu ya shirya yana jiran Fido ta shirya ya sauke ta a school, duba agogon hannun sa yayi yaga past nine. K'ofan ta yafara bubbuga wa yana cewa
"Idan kika k'ara minti goma wlhy tafiya zanyi na barki kusan awa d'aya kenan ina aikin jiranki"
A lokacin Fido tafito a wanka da sauri ta shafa cream ta d'auko rigan ta Material bak'i da touches blue, ta d'auka veil blue da takalmin ta bak'i da d'an colour blue high heel as always. D'aukan kayan makeup nata tayi ta zubasu a babban designer jakarta. Da gudu gudu tafita a cikin gidan tasamei sa a mota ta zauna tana sauke numfashi.
"Gerrrouttt". Yece mata a tsawace, kallon sa take with so much surprise on her face tace
" what!!! Why???"
"Are you asking me why? Bakisan kiyi sallama ba kan kishigo dallah fita malama" ajiyan zuciya tayi tana kokarin ajiye jakarta a motar yace
"Kifita da duk wani abunda kika shigo dashi" d'aukan jakarta tayi sai tura baki take dan ya matukar bata haushi tafita a motar. Da sallama ta bud'e motar tashiga ta rufe kofan nan take yaja motarsa yana wani shan k'amshi.
Chapter 5 · 0% Book details