← Book details Hayateeey Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 40

Sashe 16

Hayateeey Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fashewa da kuka tayi tace
"Yaya Aliyu please karka mini mummunar fassara, don't think otherwise, na yarda na kwana a gidan Issam but please ka yarda dani ba abunda ya shiga tsakanin mu"
Tsawa ya daka mata yace
"Don't dare try to explain anything to me, sabida ba k'aryan da zaki fad'a mini na yarda. And kuma me har zaikai ki gidan namijin da ba muharramin ki baneh? Nayi dana sanin amincewa na aure ki. I so much regret it Fido"
"Please hear me out!"
"Shhhhhh wallahi a halin yanxu koh voice naki bana k'aunar ji"

Fita yayi a d'akin, yana fita ta rushe da kuka, sanda tayi mei isarta ta share hawayen ta tayi alwala tayi sallah tana rok'an Allah yasa Aliyu ya fahimce ta. Daga nan ta kwanta bacci b'arawo yayi gaba da ita.

Aliyu yana fita a d'akin yaga Meenah tana lek'e. Tsawa ya daka mata yace
"Uban mei kikeyi anan"
"Amm daman nazo zan wuce kitchen neh"
"Kitchen tanan, zaki b'ace mini a gaba koh sai jikin ki ya fad'a miki?"
Da sauri tabar wajen, maganganun Fido yana yawo a brain nata, wato Fido har gidan wani take zuwa ta kwana. Tafi tayi tace "Ikon mai sama wonders shall never end ohhh"
Zuwa d'akin ta tayi lokacin Basma tana rusa kuka, dogon tsaki taja tace
"Gaskia sai na nema me raino dan ni gaskia bazan iya wahala ba".

Aliyu yana shiga d'akin sa flat ya kwanta a kasa, ya rasa me yake masa dad'i, he always dreamed of this night, gashi yazo amma bazai iya kusantar taba. Yace
"Why Fiddausi, kinsan yadda nake sonki kuwa? Kinsan yadda nake bala'in kishin ki? Koh fuskan ki banso maza su gani balle murmushin ki har yakai ga siffan ki. Na soki Fido, amma a yanxu I don't think ina miki son da nake miki a baya" haka ya ringa maganan zuci daga baya can bacci ya kwashe sa.

Washegari da safe Fido tana kwance tana bacci, tunda ta idar da sallah subh ta k'ara komawa bacci dan har yanxu gajiyan jiya bai bar jikin taba. Tana cikin bacci taji an watsa mata ruwa a fuska, nan take ta farka.
Yaya Aliyu neh tsaye yana watsa mata mugun kallo yace
"Ba hutu baneh ya kawo ki gidan nan maza ki tashi ki dafa mini abinci kinsan breakfast early nake ci koh"
Da kyar ta iya mik'ewa tace
"Toah Yaya Aliyu"
Dogon tsaki yaja yace
"You can't fool me so please stop acting innocent"
Shuru tayi bata basa amsa ba tafita a d'akin. Da k'yar ta samo kitchen, tunanin irin abincin da zata musu take daga baya tayi deciding tayi potatoes da liver sauce, d'anwake da fish roll.
Cikin awa biyu ta gama girkin, d'auko su tayi zuwa dinning taga already dinning a cike da food flakes na abinci. Ajiye nata flasks d'in tayi tashiga ciki dan wanka.

Super wax d'inkin riga da skirt wanda ya amshe jikin ta tasaka, yayi mata mugun kyau kamar a jikin ta aka d'inka. D'aura d'ankwali tayi ta shafa powder da lip gloss. Simple make-up tayi amma ba k'aramin kyau tayi ba. Fesa jikin ta tayi da designers turare kusan kala bakwai wani k'amshi mei dad'i neh yake tashiwa a jikin ta.

A hankali take tafiyar ta mei d'aukan hankali har tazo kan dinning d'in. A lokacin Aliyu da Meena already suna wajen, tsananin kishi Meena taji a lokacin da ta d'aga ido ta kalle Fido, ita kanta tasan Fido ta had'u gaba da baya.
Kujera Fido ta nema ta zauna a can nesa dasu, Aliyu daya kalle ta take ya sunkuyar da kansa, ta masa masifan kyau but kyaun d'in banza ta gama raba jikin ta a waje ya fad'a a zuciyan sa. Yace
"Inna ta aiko da abinci tun da sassafe naga bazan iya ci baneh shiyasa nasaki ki girka wani, but sam k'arnin abincin ki yana tada mini da zuciya so I decided naci na Inna kawai"
Meena tace
"Moon of my life nima gaskia abincin Inna zanci wannan will make me puke idan naci"
Fido dai shuru tayi tana kallon ikon Allah, haka suka d'eba abincin Inna su Peper soup na kayan ciki, rusted chicken, alale da kunun madara. Abincin ta koh tab'awa basuyi ba. Potatoes ta d'iba ta had'a shayi, da kyar ma take iya ci. Ganin Aliyu tayi da Meena suna bawa junan su abinci, ita kam koh ajikin ta koh irin kishin nan bata jiba, ta d'anci abunda zata iya ci zata tashi kenan Meena tace
"Moon of my life ya maganar samo mini mai rainon da zakayi"
Murmushi ya mata tareda yi mata Peck yace
"Don't worry, ai yanxu kin samu mai raino, ga Fido me amfanin ta? Kinsan ai daman bana son bawa 'yata ma wata bare tana rik'e mini ita tunda Allah yasa Fido tana gidan nan kuma 'yar gida ce ai sai tana miki rainon, shin me ma amfanin ta? Daga yau ita zatana dafa mana breakfast, lunch da kuma dinner. And plus ta zama nanny Basma as from yanxu, Kinji koh?"
"Eh naji"
"Good yanzu ki karb'a Basma "

D'aukan Basma tayi ta wuce da ita d'akin ta.
Fido tana zaune rik'e da Basma tana mata wasa Meena ta shigo d'akin ba koh sallama ta mik'a mata kayaki tace
"Ga kayan Basma anan, and kuma abincin ta yana store a kitchen ki kwaso wanda zakina amfani dashi d'akin ki kinji koh"
Fido shuru tayi batace komai ba, a zuciyan ta cewa take idan ba k'addara ba har Meena ta isa ta fad'a mata magana tayi shuru ai ba'ayi taba.
"Keee dake fa nake magana kin mini shuru"
"Ohk naji"

Dogon tsaki Meena taja ta fice a d'akin. A hankali Fido yaje kitchen ta had'o ma Basma abinci ta bata, ita mamaki ma take yarinyan da koh shekara d'aya bata cikaba bar an yaye ta Ikon God!

Da daddare bayan ta had'o musu dinner suna zaune suna ci, Aliyu sai wani zazzare ido yake yace ma Meena
"Dearie nikam bakijin zafin atargon abincin nan neh?"
Meena ta kashe murya tace
"Moon of my life wallahi nima dakyar nake iya cin abincin nan, banda pepper ma ai oil yayi yawa wai a haka ake dafa fried rice"
Duk maganganun da suke Fido jinsu kawai take dan tasan yanxu tafara cin karo da wulakanci.
"Keee" Aliyu ya fad'a a tsawace
"Maza tashi kije ki dafa mana Indomie wannan abincin naki ba iya ci zamuyi ba"
Fido ta maraice murya tace
"Yaya Aliyu ka tausaya mini wallahi a gaje nake please"
"Zaki tashi koh sai na kakkarya ki?"
Kan ta tashi Basma ta fashe da kuka, Aliyu yace
"Amma ke yarinyan nan kin bata abinci kuwa"
"Ina kuwa zata bata muguwa so take yunwa ya kashe mini d'iya"
"Ki bata abincin ta idan kin gama ki kawo mana Indomie mu nan"
"Toah" ta amsa masa ta d'auke Basma suka bar wajen.
Meena tace
"Wallahi Moon of my life Fido...."
Bata karasa maganan taba ya daka mata tsawa yace
"Will you shut up"
Nan take tayi shuru, ita ta lura a gaban Fido neh kawai yake mata wulakanci amma baya yadda a bayan idon ta ayi maganar ta. Tunani take wani irin tarko zata had'a da zaisa Aliyu ya rabu da Fido.

Cikin minti goma sha biyar sai gata tazo da Indomie a plate, dira musu tayi a gaban su zata juya ta koma Aliyu yace
"Ina zuwa?"
"D'aki, nabar Basma ita kad'ai"
"D'auko ta"

Juyawa tayi ta wuce d'akin ta ta d'auko Basma, karb'an Basma yayi yace
"Kwashe abincin ki kikai kitchen na koshi"
Bak'in ciki neh ya cikata amma ba yadda ta iya, kwace su food flakes d'in tayi. Meena tace
"Ki wanke su karki barsu haka nasan halin ki muguwar k'azama ce keh"

Wani kallo Fido ta watsa mata nan take tayi shuru, ganin abun ya b'ata mata rai Aliyu yayi caraf yace
"Toh karya tayi neh? Kije ki wanke su idan kin gama kizo ki amsa Basma"

Ficewa tayi zuciyan ta na k'ona, hak'ika sunci mata mutunci, wani zazzafan hawaye neh suke sauko wa kan kuncin ta tace
"Issam you make things worst for me and I won't forgive for that. I swear to Allah I won't spare you, the moment na bar gidan nan kaine target na!

By

Nana Fa'ad
*HAYATEEY*

Pure Moment Of Life Writers(p.m.l)

[We don't just entertain, we touch the ❤ heart of the readers]

In Dedication To Fido Sodangi

{August,2017}

I dedicated this page to members of Pure Moment Of Life Writers: Sad-nas, Mushkurat Othman, Mrs Fawwaz, Ayshat Asym, 'Yar gatan Sadnaf, Jannart Lameed'o, Sumyn bash, Leemcykhan, Mhis B hal, Aisha salihu, Faridat Musa, Minash bawa, 'yar adami, Raks Ruky, Aisha hanwa kai all & wanda sukaga a previous page d'ina. I heart❤ you all.

```Page 27```

Kwance yake a gadon asibiti ya rame yayi duhu, kamar ba Issam wanda mata suke hauka akan sa ba, gefen sa Mummy ce zaune kan kujera ta rik'e hannun sa damuwa fal a fuskar ta. A tsaye kuma wani mutum neh rik'e da Cup yana addu'a yana tofawa cikin ruwan, bayan ya gama ya mik'a wa Mum yace
"Karb'i ki basa yasha, In Shaa Allah idan ana yawaita addu'a zai samu sauki, zan na zuwa ina masa addu'a and kuma yana tashiwan dare yana nafila, addu'oin da na basa yana karanta wa, zan wuce ana jirana, dan Allah ki tabbata yasha"

Karb'a Mum tayi tace
"Nagode sosai Mallam, In Shaa Allah zamu dage da addu'a"
"Ba komai Hajiya, ni zan wuce"
"Ka gaida gida''
" Gida zai ji" tareda da fita a d'akin.

Mum mik'a masa tayi tace
"Ungo karb'a kasha Issam"
Juya kansa d'ayan gefen yayi yace
"Mum ki yarda dani yanxu sam bata raina na jima da fidda ita a cikin zuciya ta"
"Naji na yarda but dan Allah ka karb'a kasha"

Mum ta taso zuwa inda ya juya tace

"My Son dan Allah ka karb'a kasha, shin bakayi Imani da qaddara ba?"
Chapter 16 · 0% Book details