← Book details Hayateeey Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 40

Sashe 3

Hayateeey Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan minti talatin jirgin su ya d'aga zuwa Kt, cikin minti goma sha biyar sai gasu a Umaru Musa Yar'aduwa airport, bayan sun kwashe kayan su suna jira azo a d'auke su zuwa gida, can sai ga wata mota perfection bak'a tazo tayi parking a gaban su, wani saurayi wankan tarwad'a dogo neh yafito a motar fuskan sa d'auke da murmushi ya durkusa har kasa ya gaishe da Mum
"Mum sannu da zuwa ina yini"
"Lafia k'alau Son mun samei ku lafia"
"Lafia k'alau wlhy" mik'ewa yayi yaja gyalen Shamcy yace
"Shamcy beb sai k'atuwa kike zama fa" tura masa baki tayi tace
"Allah Yaya Khaleal kadaina ce ina zama k'atuwa banso" yayi murmushi yace
"Tam naji baby last" juyawa yayi wajen Fido yace
"Mss Beauty ina gaisuwa" murmushi Fido tayi wanda yake kashesa tace
"Yauwa Mallam" tareda wartan key motar hannun sa ta bud'e motar tashiga driver seat tareda kicking motar ta juya ta d'aga musu gira tace
"Sai kuzo mu tafi ai I really wanna go and rest"
Goruba road tayi dasu straight cikin wani babban gida, cikin gidan flat neh guda biyar sai kuma upstairs wanda yake bakin gate
Flat na gefen Upstairs d'in suka shiga, wata tsohuwace zaune kan kujera ta rik'e remote a hannu tana kallon Mbc Bollywood, yadda ta maida hankalin ta akan Tv sai ka rantse tana jin yaren. Shamcy da gudu tazo ta rungume ta tace
"Ohhhhhh My Innas" Tsohuwar tsayawa tayi tana kallon ta tace
"Wannan ba Fiddausi ba" Fido tazo gaban ta tace
"Kai Inna just five months back fa mukazo Kt hutu ace bakya ganeh mu, a haka kike kallon Indian film koh mei kike kallo a ciki Oho, keba gani meh kyau ba keba jin yaren ba kinga asaran zama kenan" dunkule Inna ta mata tace
"Toh ni ina zan ganeh ku, kullum sai k'ara girma kuke kuma uwarku taki ta aurar daku, da a kauye kike da yanxu keda Shamsiyya kunada jika" ta juya ta kalle Shamcy tace
"Yanxu ke Shamsiyya shekarun ki nawa" Shamcy ta tura bakin ta tace
"Innas I am just Sixteen"
"Sittin na gidan ku, ki kiyaye ni 'yar rashin kunya yarinya daga tambayan shekarun ki zakice mini sittin, koh marigayi mahaifin ku baikai sittin ba" Shamcy ta fashe da dariya Fido ce tayi guntun tsaki tace
"Inna toh mei tace, tace goma sha shida, a turance Sixteen"
"Toh ni ina zan sani, turanci ai sai ku 'yan rashin kunya yaran zamani"
Kefa Fedo
"Ashirin da hud'u" ta fad'a a takaice, salati Inna tayi ta aza hannu a ka tace
"Nashiga uku, yanxu shekarun ki har yaka ashirin da hud'u ba aure ba yaro, Inna Lillahi Wa Inna Ilayhir Raji'un, ni lokacinda nakeda shekarun ki ai marigayi da wayon sa, gaskia hakan bazaiyu ba, bari Salisu yazo asan yadda za'ayi, a cikin yara samarin gidan sai a had'a ku da d'aya" Fedo tace
"Tab, karki ma fara wlhy Inna ni sai nagama makaranta zanyi aure kuma kiji ...." bata k'arasa maganar ba Mum tamata mugun kallo, take tayi shuru
"Ni nashiga uku, Makaranta fa kikace, toh wlhy ba a gidan nan ba, shekaru nawa kikayi kina makaranta har yanxu baki gama ba, wannan wace irin kwakwalwa gareki, gaskia wannan rashin illimin a wajen uwarki kika gada ba wajen marigayi Muhammadu ba, kuma keda makaranta yakare" Fedo shiga tayi cikin d'aki dan gani take a yadda takeji a ranta ba wanda ya isa ya hanata zuwa United Kingdom, ta kudirce a ranta zuwa two weeks zatabar kasar Nigeria.....

Bayan Mum sun gama magana da Inna akan yaran duk za'a musu aure, Mum tashiga cikin d'aki ta sameh Fedo kwance kan gado da waya a hannun ta, shafa kan Fedo tayi tace
"Mamata ya naji kina maganar sabon abu wai shi makaranta, kamata yayi kiyi aure idan yaso koh professor kizama amma da aure akanki dan aure shineh mutuncin 'ya mace" tashiwa Fedo tayi tace
"Mum bazaki ganeh baneh, kinsan ni lecturer ce, bazan iya zama a position d'ina na Assistant Lecturer ba, I wanna be on my own, Masters kawai zanje nayi kuma shekara d'aya neh, pls Mum ku barni naje nayi nadawo"
"Toh idan zakiyi saidai a garin nan"
"Mum wlhy a garin nan sai nakai shekaru biyu ban gama ba, amma kinga kasar waje highest shekara d'aya zanyi na dawo pls Dan Allah Mum"
"Shikenan toh, zan ma wan Dad naku magana" Tayi hugging mum nata tace
''Thank you so much Mum, please try your possible best naje nayi masters d'innan"
"I will sweeryh yanxu kitashi ki shirye kuje ku gaisa da mutanen gidan" had'a rai tayi tareda turo bakin ta tace
"Tab Mum gaskia a gaje nake, ni koh zani ma side nah Mami zan shiga gaskia bazan shiga wajen Umma da Hajja ba"
"Kidai shiga kinji ai duk d'aya suke please"
"Ohk Mum anything for you" tashiwa tayi akan gado tareda yafa gyalen ta tafesa turare suka fita itada Shamcy dan gaisar da mutanen gidan...
B'angaren Mami suka fara shiga da fara'ar ta karb'e su, zama sukayi suna hira sosai da 'yar ta Ayeesha wacce take sa'an Shamcy, daga nan suka shiga side na Hajja, Hajja da kyar ta amsa sallaman su tacigaba da abunda takeyi, sai can Shamcy tace
"Amm Hajja Zee bata gida neh"
"Eh" kawai tace tareda shiga cikin d'akin ta..
*HAYATEEY*

Pure Moment Of Writers(p.m.l)

Written By Nana Fa'ad

In dedication to Fido Sodangi

{June,2017 }

Page 9

Dogon tsoki Fedo taja tace
"Aikin banza, ke Shamcy tashi mu tafi basai ta k'ara kallon kafar mu a Side nata ba, ni wollah tunda nashigo nakejin wari zuciya nah tashi ma yake ai da mun d'ebo mata turaren wutan da mukazo dashi daga Maid" rufe bakin ta Shamcy tayi tace
"Shhhh dan Allah ki rufa mana asiri kiyi shuru please dan ni wollah tsoron matar nan nake"
"Mtswww you are nothing but a coward, dallah tashi mu wuce" tashiwa sukayi suka shiga Side na Uwargida Umma. Sallama suke tun a bakin kofa amma shuru ba amsa ba, tusa kai sukayi suka shiga ciki to their very suprise sukaga Fatyma a parlour tana zaune kan kujera da pot na shisha agaban ta tana zuga, Shamcy was shocked, Fedo taja dogon tsoki dan tasan halinta har a snap take posting videos tana shan Shisha tace
"Teema bakisan mahimmancin sallama ba koh" d'aga kai Teema tayi tareda jan tsoki tace
"Sannu ke wacce kika sani" tacigada shan Shishan ta, wayan ta dayake gefen ta Shamcy ta d'auka tace
"Adda Teema irin wayata" hararan ta Teema tayi tace
''Ni sa'ar kice,wannan ba iPhone 6 baneh iPhone 6+ ce"
"Eh I know kin gan nawa same colour with yours" tareda ciro nata, karb'an wayan tayi Teema tana juyawa tace
"Hmmm kicedai na Fedo" Shamcy tayi dariya tace
"Ai Adda Fedo iPhone 7 yana fitowa koh wata d'aya baiyi ba tasiyo" tareda mika mata wayar Fedo dan duk yana hannun ta. Teema ji tayi zuciyar ta yayi bak'i k'irin, a yadda take jin kanta babbar yarinya ai da kunya, tun da takejin haushin Fedo because she's always ahead of her. Tsoki taja tace
"And so what, nasan koh a yawon iskanci aka siyo mata" murmushi Fedo tayi tace
"Ai Teema iskanci ma kala kala neh, kingani koh a cikin 'yan iskan ni daban ce" tashiwa tayi tareda jan tsoki tace
"Shamcy tashi mubar nan it makes me puke" Teema ta zuga Shishaa ta busa mata iskan tace
"It makes you Uwarki ba Puke ba hegiya" murmushi Fedo tayi had'e da girgiza kai takama hannun Shamcy suka bar side d'in.

Da daddare Abba yadawo gida ya had'a meeting. Bayan sun bud'e da addu'a Alhaji Sanusee wanda suke kiransa da Abba yayi gyaran murya yace
"Abunda yasa nace duk ku had'u anan shineh daga yau Fiddausi da Shamsiyya sun dawo gidan nan permanent, bazasu k'ara komawa Maiduguri and acikin samarin gidan idan Allah sa Fedo sun daidaita da d'aya daga cikin su sai a d'aura musu aure"
"Cabd'i nidai bada tilon d'ana ba" cewar Hajia Khadija, Maryama tayi caraf tace
"Nidai 'yayana maza biyu kuma duk sunada aure kuma bazasu k'ara ta biyu ba ehn" Abba ya daka musu tsawa yace
"Kuyi shuru, shin mehsa bakuda kunya neh, toh zan tara samarin gidan acikin su idan akwai wanda yakeso shikenan khalas" Mum mahaifiyar Fiddausi ce tayi magana tace
"Alhaji Dan Allah inada magana"
"Inajin ki Zainab"
"Ammm daman Fiddausi ce takeson yin Masters nata kan tayi aure shineh tace dan Allah na maka magana" Hajia Maryama tace
"Cab, duk girman tan nan ai..." Bata k'arasa ba Abba ya tsaida ita da hannu yace
"A inaa takeson yin Masters d'in" Mum tace
"A UK"
"That's very good, zan barta amma da sharad'i d'aya" ya juya yana kallon Fedo
"Sharad'in shineh idan Allah sa kin gama kina zuwa gida koh sati biyu bazaki k'araba zan aurar dake, kin amince" d'aga kai Fedo tayi alamun Eh ta amince, yace "Yawwa Madallah" yacigaba
"Daman Aliyu Haydar an turashi wani training a UK so inaga zaku tafi tare" duumm zuciyar Fedo ya buga, a rayuwar idan akwai wanda takejin shakkan sa toh bai wuce Yaya Aliyu ba, General Aliyu Sanusee Sodangi. Hajia Maryama ce ta buga wani uban salati tace
"Wani Aliyu, Aliyun nawa, Haba Alhaji kana adalci mana, bayan kasan Aliyu da matarsa zaiyi tafiyar nan"
"Nasani ai sabida haka kimun shuru, kuma ai zama ita kad'ai a wata uwa duniya ba dad'i" hmmm kawai Hajia Maryama tace had'e da kananan maganganu....

ASALIN SU
Chapter 3 · 0% Book details