← Book details Hayateeey Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 40

Sashe 25

Hayateeey Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da misalin k'arfe hud'u na yamma Dr yazo ya duba sa yaga yasamu improvement sosai yace zai rubuta masu takardan sallama, wani relief da dad'i taji sabida ta tsana zaman asibitin. Daga nan Issam ya kira driver dan ya maida su gida, cikin minti goma har Fido ta gama had'a kayan d'akin, sai kallon ta yake yace
"Kin matsu ki koma gida koh bakison zaman asibiti?"
"Na tsana zaman asibiti"
Murmushi yayi kawai ya barta, can sai ga Bala driver yazo ya kwashe kayan su suka shiga mota sai gida.

Mum ba k'aramin farin ciki tayi ba data ga d'an ta har ya warware, tace "kashiga d'aki kayi freashing up Fido jeki ki taimaka masa"
"Toh"
Mum tace "Inaga ma yau Fido zata koma side naka tunda ka dawo gida zansa a kawo miki kayan ki can"
Wani bakin ciki neh ya rufe ta but ta rasa abunda zata ce, wuce part nasa sukayi, babban parlour neh da d'aki d'aya shima babban gaske, sai toilet da kitchen. B'ata rai tayi tace
"Yanxu anan zamu zauna?"
"A'a ana gyara mini gida nah na KT nan da sati d'aya zamu koma can"
Wani relief taji dan tasan idan suna gida d'aya tareda mahaifiyar sa bazata iya aiwatar da abun da tazo domin shi ba, yace
"Nasan kina aiki and you love your job, kuma baki karb'a leave ba sabida abun yazo a gaggawa. Nima inada aiki a company nah na KT idan yaso kan nagama zan nema miki lecturing a Nile In Shaa Allah zaki samu"
"Karma ka wahalar da kanka dan ni sam zaman abuja baso nake ba"
"Baso kike ba amma dole ki zauna sabida mijin ki a garin yake"
Wani kallo ta watsa mishi tareda jan dogon tsaki ta shige ciki.

Bayan yayi wanka ya canza itama haka yace
"Zanje masallaci sai bayan isha zan dawo"
"Uhum" kawai tace ya girgiza kansa yafita yana takawa da k'yar, itama fitan sa tayi alwala tayi sallah.

Sai bayan Isha'i yadawo gidan lokacin tana kallon wani series a AMC Into the badlands, bayan ya zauna na minti biyar yace
"Kizo muje wajen Mum muci dinner"
Girgiza kanta tayi tace "Kace wa Dije ta kawo nan ni bazan je can naci ba"
Bai musan ta taba ya d'au wayarsa ya kira Dije yace
"Ki kawo mana abincin mu nan" ya katse wayan. Cikin mintuna biyu sai ga Dije tayi sallama ta shigo da abincin. Dira musu tayi a gaba tace
"Yaya Issam ga abincin, ya jiki?"
"Da sauki"
"Toh Allah k'ara sauki"
"Ameen Dije nagode" yana maganar kamar wanda akasa sa dole, wani uban tsaki taja nan take duk suka zuba mata ido suna kallon ta, Dije nan take ta tashi tabar musu fili, Issam ya b'ata rai yace
"Ni wai ke 'yar tasha ce?"
"Cikikkiya ma kuwa"
"I seee"

Da daddare tayi ta saka bump shot da wani d'an guntun riga, baza gashin ta tayi wanda tsawon sa har kafad'a. Sai wani shan k'amshi take taje ta dawo, Issam tunda ya d'aga kai ya kalle ta sau d'aya bai k'ara kallon taba. Kwanciya yayi akan gado yana karanta hisnul muslim, zuwa tayi ta tsaya masa a ka ta aza hannu a kwunkoso tace
"Zan kwanta"
Can gefen gadon ya matsa yace
"Bismillah kwanta"
Dogon tsaki taja tace
"Tare zamu kwana a gado d'aya kake nufi?"
"Eh" tareda bata amsa a takaice.
"Nidai wallahi Allah bazan kwana gado d'aya dakai ba"
Tasowa yayi yace
"Ki kwanta"

Kwanciya tayi akan gadon shi kuma yayi shimfid'a a k'asa ya kwanta yace
"Don't forget to recite Suratul Mulk before sleeping"
"Toh sannu Mallam toh ni ban iya ba"

Shuru yayi bai k'ara cewa komai ba, kusan mintuna talatin da kwanciyar ta ya tashi ya d'au stool ya zauna kusa da gado ya karanta mata Suratul Mulk ya tufa mata duk tana jinsa shi a tunanin sa tayi bacci. Daga nan ya koma shimfid'an sa ya kwanta bacci.

Da asuba a hankali yake buga gefen gadon, bud'e eyes nata tayi a hankali ganin sa datayi a tsaye akanta taja uban tsaki tace
"Menene kuma?"
"Subh Hayateey"
"Toh sannu Sudeis"
"Bud'e idonki da kyau shureim neh"
Wani uban tsaki ta k'ara ja tareda tasowa akan gadon ta shige toilet tayi alwala, bayan ta fito ya mik'a mata hijabi ta karb'a ba musu yaja su sallah, bayan sun idar yaringa karato addu'a ita kanta ba k'aramin mamaki tayi ba, sai cewa take a zuciyan ta ashe haka yake da illimin addini? Sai can kuma tace ilimin addinin da baya amfani dashi toh meh amfanin sa?. Cire hijabin jikin ta tayi bayan ta shafa addu'an tana k'okarin kwanciya yace
"Me kike shirin yi?"
"Abunda idon ka yagani maka"
"Karki kuskura kice zaki koma bacci ki bari rana ya fito"
"Karna koma bacci na maka meh toh"
"Ki karanta Qur'an"
Zatayi magana ya daka mata tsawan daya firgita ta yace
"Bana son musu"
Haka ta taso akan gadon ya mik'a mata Al Qur'ani ta amsa, haka ta ringa recieting har sanda rana ta fito ta ajiye ta koma baccin ta, ita kanta taji zuciyan ta yayi sanyi.

Da safe bayan tayi wanka ta tsara kwalliya sai zirga-zirga take daga parlour zuwa d'aki dan kawai ya ganta, shi kuma koh d'aga kai baiyi ba balle yasan ma tanayi. Can kusan k'arfe goma tana zaune tayi crossing leg a parlour tana kallon film a HBO channel Game of Thrones Issam yashigo yace
"Hayateey tashi ki d'au mayafinki muje mu gaida Mum"
Bud'e baki tayi tana kallon sa sai can tace
"Tab! Wace Mum?"
Shuru yayi yana kallon ta ya kasa cewa komai, wani dogon tsaki taja tace
"Kaga Mallam ni yunwa nakeji a kawo mini abinci naci"
Shuru yayi yana kallon ta sai can ya d'au wayarsa ya latsa number Dije, tana picking yace
"Dije please ki kawo mana breakfast namu nan" ya katse wayan.
Cikin two minutes sai ga Dije tashigo da tray na abinci, tace
"Amarya kin tashi lafiya?"
"Idan ba lafiya ba ai baza ki ganni haka ba"
Shuru Dije tayi tace "Yaya Issam gashi nan na kawo"
"Yawwa Dije nagode"

Dije tana barin parlour Fido taja tray d'in gabanta ta zuba abinci tana ci tana kallon ta, shidai Issam girgiza kansa yayi tareda fita a parlour.

Bayan Sati D'aya

Fido ta gaji da zaman gidan, tabbas tasan idan har suna zaune a gidan su Issam bazata iya aiwatar da komai ba. Gashi yanxu lamarin Issam yana bata tsoro, takan tambaye kanta anya Issam namiji neh kuwa? Idan ma namijin neh toh tabbas bashida lafiya sabida kullum tana cikin saka k'ananan kaya masu bayyanar da tsadadden surar ta amma koh d'aga kai bayayi ya kalleta balle har ya tunkare ta da wani abu.

Wani irin kuka ta fashe dashi tareda aza hannu a kanta, Issam dake parlour take yashigo cikin d'akin ya durk'usa zai tab'a ta tamasa wani irin tsawa
"Don't touch me with your filthy phalanxes"
Maida hannun sa yayi ya zauna kusa da ita hankalin sa duk a tashe yace
"Meya faru Hayateey? Mesa kike kuka"
"Gida"
"Gida kuma Hayateey?"
"Aiki nah"
"Ohhh so sorry! Karki damu Hayateey gobe In Shaa Allah zamu koma KT kinji? Yanxu ma zan tattara miki kayan ki please don't cry! If you cry it will break my heart"

"Promise?"

"I promise"

Fita yayi a d'akin yace bara na sanar da Mum, tun lokacin da tabar part na Mum koh da wasa bata k'ara shiga wajen ta da sunan zata gaishe taba, bata tab'a girki ba saidai a kawo mata. Wani shu'umin murmushi tayi tace
"Had it been kasan abunda nake niyan aikatawa a kanka hmmmmmm"

Nana

Fa'ad
*HAYATEEY*

Pure Moment Of Life Writers
[We don't just entertain and educate, we also touch the ❤ hearts of the readers]

_In dedication to Fido Sodangi_

{August, 2017}

Follow me on Wattpad @Nana_Faad. Do read my write-ups and please don't forget to SHARE/VOTE!!!

```Page 39```

Mum tana zaune a d'akin ta laptop akan cinyarta Issam yashigo da sallama, duk'usawa yayi har kasa ya gaishe ta, amsawa tayi da fara'ar ta tace
"Son ya akayi?"
Sosa suman kansa yayi yace
"Amm Mother daman Fiddausi ce takeso ta koma wajen aikin ta dan bata karb'a leave ba and kuma nima inaso naje na duba gidan mai na KT da company nah"
Mum ajiyar zuciya tayi tace
"Son zo ka hau kan gado"
Tasowa yayi ya zauna a bakin gado kusa da ita yana facing nata, hannun sa ta kama tace
"Son akwai abunda nakeso na fad'a maka, but farko lemme ask you something"
Hankalin sa gaba d'aya ya tattaro zuwa gareta yace
"Ohk Mother"
"Shin kasan asalin Fiddausi? Kasan baban ta?"
Girgiza kansa yayi yace
"A'a Mother bansan shiba, but ai ya rasu"
"Kasan sunan sa?"
"Eh Muhammad"
"Muhammad wa?"
"Gaskia Mum ban sani ba"
"Asalin sunan matar ka Fiddausi Muhammad Sodangi"
A take ya taso tsaya yace
"What!? Mum are you sure? No that's not true"
"Bazan fad'a maka abunda i aiin't sure of ba, naje gidan su da kaina, mun had'u da wan baban ta Sanusi, nasan shi farin sani"
Wani gumi neh yake sauk'o wa a goshin sa duk da sanyin AC split na d'akin, ya rikice iya rikicewa, Mum ta zaunar dashi tace
"Son laifin uba baya shafan d'a, so inaso kayi hak'uri ka zauna da ita, ka mini alkawarin bazaka rabu da ita a wannan reason d'in ba"
Kaman hannun Mum yayi gam yace
"Mother I told you, She's my HAYAT! Bazan iya rabuwa da itaba, ina son ta, so na hakik'a"
Murmushi Mum tayi tareda shafa fuskan d'anta tace
"Allah maka albarka, Allah kawo zuri'a nagari"
Da k'yar ya k'wak'ulo murmushi yace
"Thank you Mum"
"Gobe In Shaa Allah zanzo mu gaisa da amaryan kan ku tafi"
"A'a Mum karki zo zatazo ma ta gaishe ki In Shaa Allah"
"Ba komai Son zanzo"
Chapter 25 · 0% Book details