← Book details Hayateeey Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 40

Sashe 17

Hayateeey Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shuru yayi bai amsa ba, tacigaba
*"What is meant for you, will reach you even if it is beneath two mountains. And what isn't meant for you, won't reach you even if it is between your two lips. Allah chose for you a spouse before you were even born"*

Jikin sa yana kakkarwa ya kamo hannun Mum nasa ya rik'e gam yace
"Mother inason Fido, duk da tayi aure na d'auka sonta zai ragu amma kullum son ta yana multiplying acikin Zuciya nah, I don't really know how to explain this to you. Infacts words aiint enough to express how much I love her but ki yarda dani idan nace miki She's My HAYAAT, ITACE RAYUWA TA!"
"Shhhh My Son, a yanxu matar mutum kake magana, kayi istigfari karka yi sab'o, so ba hauka baneh, kata addu'a don shine maganin komai. Kasani matar mutum kabarinsa, ba wanda ya isa ya aura matar wani. Babu wanda ya isa!"

A sannu da lallashi ta basa ruwan yasha.

_Bayan Wata Biyar_

Fido girki take a kitchen ta rame tayi baki sai ka rantse ba ita bace, gefen ta kuma Basma ce zaune akan keken ta, tayi girma sosai kamar wata 'yar shekara biyu. Basma ce tafara kuka gashi tana girki ta rasa yadda zata yi. D'aukan Basma tayi zuwa d'akin ta tahad'a mata Nan tabata tasha, da k'yar ta samu ta lallashi ta tayi shuru. Komawar ta kitchen taga an k'ara mata wutar girkin ta gas d'in naci sosai ga warin k'onan miya. Bud'e miyar da zatayi taga miyar ya k'one kurmus. Zuciyan tane yayi bala'in b'aciwa tasan kan tabar kitchen ta rage wutar. Fita tayi a kitchen d'in ta wuce d'akin Meena direct.
Meena, Teema da Ramlah neh zaune suna shewa. A tsawace Fido tace
"Uban waye ya k'ara mini wuta bayan na rage kan nabar kitchen d'in?"
"Uban ki" cewar Teema, kan tagama fad'a taji saukan mari mai kyau da lafiya a fuskar ta, Fido ta nuna mata yatsa tace
"Next time zan miki marin da yafi haka, ni sa'ar kice? Ni sa'ar kuce? Duk wanda ya k'ara tab'o ni a gidan nan wlh zan koya masa hankali 'yan iska kawai"
Ramla tace
"Kece babbar 'yar iska ai, wanda saura one week da auren ki kika kasa hak'uri kika kwana a gidan wani gardi"
"Shiyasa Miji nah har yau ya kasa had'a kwanciya da ita, me zaiyi da left over, second hand ai wlh.." Cewar Meena, bata k'arasa ba itama taji saukan mari mai rai da lafiya a fuskan ta. Fido tace
"Daga ke har mijin naki wallahi bana tsoron ku, shima daga yau na daina barin sa wallahi balle kannen sa, ku d'in banza" taja dogon tsaki tabar d'akin.

Baki bud'e suke kallon ta, Ramla tace
"Wallahi bata isaba, zamu mata dukan gaske kan mubar gidan nan, wallahi baza taci bulus ba"
Meena tace
"Wallahi bata isa ta tab'a fata na nabar taba, tayi kad'an, sai ta raina kanta wallahi a yau d'in nan"

Fitan Fido kenan taci karo da Eesha, nan take tayi gudu ta rungumeta ta fashe da kuka tace
"Eesha dan Allah ki taimaka mini, bazan iya zama a gidan nan ba, gidan nan idan banda bala'i da masifa ba abunda yake cikin gidan nan"
Eesha tayi hugging nata sosai tace
"Shhhh ki daina fad'an haka, duk abunda yayi farko toh hak'ika yanada karshe, muje d'akin ki"

"A'a ki kije ga can d'aki nah" tareda nuna mata
"Zan shiga kitchen na d'aura girki zanzo na sameki"
"Ohk toh"

Kitchen ta shiga ta d'aura sabon girki, amma bana na ita da Eesha ta dafa koh ajiye wa Aliyu batayi ba. Bayan ta gama ta kai musu suka zauna suka ci. Fido tace
"Ya Faruq?"
Eesha tayi murmushi tace
"Lafiya sa kalau yana ma gaishe ki"
"Allah sarki, nimafa ina son zuwa miki Allah baiyi ba"
"Ayyah ba komai, shin yaushe zaki fara fita aiki Fido?
"Wallahi kedai bari, Aliyu ya hanani kuma yace idan na fad'awa Abba a bakin aure nah. Yaya Aliyu mugu neh Eesha" ta fashe da wani irin kuka
"Tunda nayi aure koh gate ban lek'a ba, kullum ina cikin gidan nan, bai damu dani ba, na zama musu mai aiki kawai"
Eesha tace
"Shhhh ki daina fad'an haka akan mijin ki, ki zama mai rufe sirrin mijin ki, duk abunda yayi farko yana da karshe, kita addu'a In Shaa Allah komai mai wuce wa neh"

Haka suka ta hira har karfe biyar, daga nan Eesha tace zata wuce gida. Rakata tayi zuwa kasa Basma na hannun ta, a parlour k'asa Meena suna zaune da Teema da Ramla.
Meena ta mik'a hannu akan Basma taje wajen ta, Basma ta rushe da kuka ta girgiza kanta ta kankame Fido. Bayan sun fita Teema tace
"Meena tun ba'aje koh inaba har 'yarki ta fara gudun ki?"
Ramla tace
"A'a lalle kinada aiki a gaba"
"Kan gaba zan shafe ta a dorar k'asa" cewar Meena. Duk suka kwashe da dariya sukace
"I trust you girl"
"Yanzu abunda zamuyi idan tashigo mu karb'a Basma koh bataso mu kaita d'aki sai muci uban 'yar iska" cewar Meena.
Duk suka amsa da
"Yes kin kawo shawara"

By

Nana Fa'ad
*HAYATEEY*

Pure Moment Of Life Writers
[We don't just entertain, we touch the ❤ heart of the readers]

_In dedication to Fido Sodangi_

{August, 2017}

```Page 28```

Har bakin gate Fido ta rakata tace
"Nagode sosai Eesha da advice da kika bani, In Shaa Allah zanyi amfani dasu"
"Karki mini godiya, what are friends for?"
Fido tayi murmushi tace
"You're more than a friend to me"
Eesha tayi murmushi tace
"Really, wow! Thank you. Bye"
"Bye"

Tana shiga cikin gida Meena ta karb'a Basma dukda irin kukan da take tsalawa, Fido tace
"Ki barta mana tunda bata so"
"Nida 'yata kuma, kya jiki fa"
Bayan Meena ta amsa Basma ta mik'a wa Ramlah ita, Ramla da gudu ta shigar da Basma d'aki ta rufe kofa.
Ganin su uku tayi suna zuwa kanta, tace
"Ya haka dai? Wani abu neh?"

Meena tace
"Taruwan dangi zamu miki ba komai ba"

Kan ta iya k'ara magana suka hau kanta dukkan su uku, duk yadda tayi ta kare kanta amma karfin mutane uku ya wuce wasa. Jibgan ta suke kamar ba gobe, Meena tana ta sama, Ramla tana kan ciki, Teema tana kafa. Da ikon Allah Fido koh ihu batayi duk da yadda suke jibgan ta saima k'okarin ramawan da takeyi.

Sun kusan minti goma suna abu d'aya, sai can dabara ya fad'o mata ta kama fatan Meena ta ciza kamar ta samu nama har sanda jini ya fara fitowa. Ihu Meena take sosai nan take ta tashi akan ta, Ramla da take ruwan cikin ta takama gashin kanta wanda yasha attachment ta ringa ja kamar zata raba kanta da gashin. Ba shiri Ramla ta taso akanta. Teema wacce ta rik'e kafa ta samu ta mata wani irin naushi a baki har sanda jini ya fito. Tashiwa tayi gashin kanta duk a barbazo ga kayan jikin ta sun yage duk ana kallon surar jikin ta. A tsawace tace
"Dan Allah kuzo idan kun isa, idan ku mahaukata neh ni kuma babbar mahaukaciya ce"

Zuwa kanta suka fara, ganin zasu k'ara hawwa kanta da gudu ta shiga kitchen ta d'auka tab'arya ta fito. Tace
"Kuzo dan Uban ku"
Meena itama shiga kitchen d'in tayi tafito da nata tab'aryan. Suna zuwa kusa da ita tafara kwad'a ma Teema da Ramla a jiki wanda yasa suka kwanta flat a kasa. Saura ita da Meena suna kalle kallen juna.
Meena zata buga mata tab'arya ta tare da nata kawai sai ga tab'aryan duka biyu a k'asa. Shigan ta Fido tayi ta hau ruwan cikin ta tana d'irka. Zo kuga yadda Meena take ihu take fad'an "Wayyyooo Allah nah kuzo ku taimaka zata kashe ni!"

Ganin Aliyu nayi ya shigo parlour da gudu ga S.A a bayan sa. Wurgar da Fido yayi kamar kayan wanki ya fara jibgan ta. Sai cewa yake
"Zaki kashe mini mata koh?"
Da k'yar S.A ya kwace ta a hannun sa, ganin irin kayan da yake jikin Fido yasa ya fita a parlour da sauri. Aliyu bak'in ciki neh ya rufeshi gashi S.A ya gan masa mata a haka. Jan ta yayi har zuwa d'akinta ya cire belt nasa yafara zane ta yana fad'in
"Uban mei yakai ki parlour har kije kiyi fad'a da su ehh, abunda kike so yafaru tunda S.A ya gama ganin surar ki"
Fido kuka sosai take tace
"Yaya Aliyu wallahi she started it, itada Teema da Ramla"
Yana jin haka ya fita a d'akin ya rufe kofa ya sauk'o k'asa daidai lokacin su Teema da Ramla sun kwasa kayan su zasu gudu gashi da k'yar suke iya tafiya Aliyu ya cafko su ya rufe kofa ya fara jibgan su da belt, dukan su yake har sanda belt nasa ya tsinke. Bai hak'ura ba yacigaba da dukan su da hannu da duk karfin da Allah ya basa. Yace
"Ku fad'a mini gaskia ku kuka fara neman fad'an ta koh?"
Da sauri Teema tana kuka tace
"Mune Yaya dan Allah kayi hak'uri bazamu k'ara ba dan Allah Yaya karka kashe mu"
Sanda ya gaji dan kansa ya barsu tareda jansu ya fitar dasu a cikin parlour ya wurga musu jakan su yace
"Kubar gida nah idan na k'ara kallon kafar ku cikin gidan nan sai jikin ku ya fad'a muku, 'yan iskan yara kawai"

Shiga yayi cikin d'akin sa ya watsa ruwa ya wuce masallaci lokacin su Teema da Ramla har sun bar gidan. Shi bai dawo gidan ba sai kusan karfe tara na dare.
Chapter 17 · 0% Book details