Sashe 22
Hayateeey Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Fido da daddare ta kasa bacci sai tunanin Issam take, ta rasa solution da zatayi tayi avenging abunda yayiwa mahaifin ta. Tasan kuma idan ta aura S.A Lagos zasuje dan acan yanxu yake. Cusa hannun ta tayi cikin sumar kanta tace "Ya salaam me zanyi dan na rama abunda Issam ya mini, nayi rantsuwa bazan barshi ba koma wallahi bazan tab'a barin sa ba, sai yayi dana sani wallahi"
Da sassafe Issam ya wuce airport dan koh bacci bai samu yayi ba a daran jiya
Koh minti talatin ba'ayi ba jirgin ya d'aga zuwa Abj.
Yana shiga gida Mum nasa tayi welcoming nashi tace
"Son ya Katsina ya hanya?"
Murmushin dole yayi yace
"Kalau Mother Alhamdulillah"
Mum tayi murmushi dan tasan d'anta ba mai yawan son surutu dayawa baneh, kusan secs talatin yace
"Mum har yanxu kina son kallon Zee world?".
Murmushi tayi tace " Eh wallahi" can kuma yace
"Ina Salala bata dawo ba?" Murmushi Mum tayi tace
"Eh bata dawo ba"
"Anty Sajida fa?
Mum kama hannun sa tayi tana kallon cikin idon sa da yayi jazur, tasan Issam bashida yawan tambaya haka, tasan halin shi yana k'okarin b'oye mata halin da yake ciki neh. Tace
"What's up anhh? Chatter is a fool's pursuit. Your eyes can't hide what your words conceal. Mesa bazaka bar tears d'in su sauk'o ba? Don't imprison them, let them free."
Sai ga hawaye shar shar yana sauk'o wa kan kuncin sa, Mum abun har tsoro yake bata. Issam koh a k'arami bai kuka, last kukan sa mutuwar mahaifin shi neh wanda bazasu tab'a mantawa ba, sai kuma soyayyar da yakewa Fido. Issam ya rik'e Mum nasa gam yace
"I really love her Mother, I so much love her. My Qalb only beats for her! She's my HAYAT Mother!"
Rungume tilon d'anta tayi tana lallashin sa kamar yaro, tunani take meh yakamata tayi ta cece d'an ta. Sai can dabara yazo kanta tace
"Son karka damu In Shaa Allah Fido matar kace"
"Inaa Mother Fido tariga tamun nisa"
"In Shaa Allah, katashi kashiga d'akin ka kayi freashing up"
"Ohk"
Da k'yar ya iya tashi, yana cikin tafiya sai kawai taji daf mutum ya fad'i. Ba k'aramin girgiza tayi ba dataga ya fad'i kasa. Da gudu taje wajen tana girgiza shi tana cewa
"Issam habeebi dan Allah ka tashi, na maka alkawarin zaka aure ta, ka tashi Fido is yours I promise"
Amma inaa koh numfashi bayayi, a guje ta fita tayiwa masu gadi da aiki magana nan sukazo suka d'auke shi suka saka shi cikin mota sai asibiti. Ana kaishi likita suka rik'e shi emergency, ganin likita ya fito a operation room d'in Mum a guje ta samu likitan tace
"How was he Dr?
"Karki damu In Shaa Allah he'll be OK, but inaso idan mun gama ki same ni a office"
"Ohk ba matsala, but yanxu zanyi tafiya katsina In Shaa Allah idan nadawo a yau d'in nan zan same ka"
Dr mamaki neh yacika shi ace d'anta rai hannun Allah tana maganan zatayi tafiya yace
"Zakiyi tafiya kuma? Kinsan irin halin da d'anki yake ciki kuwa? Koh ba d'anki baneh?"
"He is my son nasan me nakeyi, bye"
Ta juya a guje ta samu driver ta Bala, tace
"Bala k'arfe nawa yanzu?"
"Tara cif Hajiya"
"Kaimu Katsina banson wani magana kashiga muje"
Take suka shiga motar sai Katsina, cikin awa d'aya sai gasu a KT sabida yayi gudu sosai, k'iran number Eesha tayi ta bata address na gidan tace idan taje anguwan tace tana neman gidan Professor Sanusi Umara Sodangi, zuciyan Mum neh ya buga jin sunan Prof. Sanusi Umara Sodangi, tunani take koh dai 'yarsa ce? Tana sake2 a ranta har suka iso anguwan.
Gidan su Fido direct ta tsaya sabida gidan sananne neh sosai, tana shiga ta had'u da Aysha suka gaisa, Mum tace
" 'Yan mata inane side nasu Fido "
Aysha tayi murmushi tace
"Muje na kaiki"
Fido zaune take a parlour itada Inna suna cin biski da miyan kuka, Inna sai santi take tace
"Ai idan bakwanan ba wanda zaiyi biskin nan"
Fido tayi dariya tace
"Kai Inna biski ma har abun so neh?"
Aysha tashigo parlour tayi sallama, ganin bak'uwa a bayan ta Fido ta tashi tana sannu da zuwa ta nuna mata kujera ta zauna. Aysha tace
"Adda Fido kinyi bak'uwa"
Inna tace "Toh ikon Allah"
Fido har kasa ta durk'usa ta gaishe ta, Mum tace
"Lafia kalau 'yata"
Daga nan Aysha tafita ta basu waje, Inna tace
"Baiwar Allah daga ina?"
Mum tayi murmushi tajuya tana kallon Fido tace
"Kin ganeh ni kuwa Fiddausi?"
Fido shuru tayi tana tunanin inda ta santa dan tabbas her face looks familiar, tunani take tayi taga ta kasa tunowa ta girgiza kanta tace
"A'a wallahi ban ganeh ki ba"
Mum tayi murmushi tace
"Mun tab'a had'uwa sau d'aya a Maiduguri international airport, time d'in kuna tareda Issam, ni mahaifiyar sa ce"
Wani mugun mamaki neh yacika ta, tunani take toh meya kawo Mum nasa kuma gidan su?. Inna tace
"Ohhh sannu da zuwa 'yata, ashe ke mahaifiyar Issam ce, yaron kirki d'an albarka, ke Fiddausi maza tashi ki kawo mata abun motsa baki"
Fido zata tashi Mum tace
"Karki damu Inna, a yanxu da nake muku magana Issam yana asibiti rai a hannun Allah, na tabbata ciwon zuciya ke damun sa, kuma a dalilin Fiddausi"
Inna ta kama baki tayi salati tace
"Na shiga uku, Issam neh kwance a asibiti rai a hannun Allah akan wannan mummunar yarinyan, shi gashi kyakkyawa d'an balarabe yasa ma kansa damuwa? Inna lillahi wa inna Ilayhir Raji'un, akan wannan banza? 'Yata kije kizo da magabatan sa gobe za d'aura musu aure"
Mum tace "a'a baza ayi haka ba, Fido sai ta yarda"
Mum ta kama hannun Fido hawaye na sauka akan kuncin ta tace
"Daughter nah duk abunda kikayi deciding dai-dai neh, I can't force you and nobody can force you, You've your own right to decide what's best for you. But ina rok'on ki da Allah ki cece d'ana, ina sonshi, ina matuk'ar sonshi, You're his HAYAT! Kinsan irin condition da yake yanxu kuwa? Dan Allah ki taimaka mini."
Fido ba k'aramin mamaki tayiba ganin babbar mace tana mata kuka tana rok'an ta, amma zuciyan Fido koh karaya baiyi ba. Fido tana mai zubda kwalla ta share hawayen Mum tace
"Don't cry please Mother, na amince, wallahi zan aure sa"
Mum wani rungume ta tayi tana kuka tace
"Nagode, Nagode"
Fido wani irin murmushi tayi tace
"Ba komai kar kimini godiya Mum"
A zuciyan ta kuma cewa take
"Kun kawo kanku gidan mutuwa! I'm gonna use this opportunity nayi shattering life na Issam"
By
Nana Fa'ad
*HAYATEEY*
Pure Moment Of Life Writers
[We don't just entertain and educate, we also touch the ❤ hearts of the readers]
_In dedication to Fido Sodangi_
{August, 2017}
Follow me on Wattpad @Nana_Faad. Do read my write-ups and please don't forget to SHARE/VOTE!!!
```Page 35```
Inna itama da guntun hawayen ta tace
"Alhamdulillah Allah mungode maka! Fiddausi Allah miki albarka, Hajiya kinyi sa'a dan da yamma Sanusi zaibar k'asa yanxu muje a masa magana"
Da Inna da Mum suka wuce part na Abba, a lokacin yana zaune yana kallon channel saudi suka yi sallama ya amsa musu. Mamaki neh ya cikasa da yayi ido hud'u da mahaifiyar Issam itama haka, yace
"Hajiya Rumah? Ikon Allah kece wannan?"
Zuciyanta ya buga da ganin sa, daman tun lokacin da aka bata address na gidan take sake-sake a ranta, last time dai tasan yana zama a Kd, murmushin dole tayi tace
"Alhaji Sanusi rai kanga rai"
"Bismillah" yace dasu duk suka zauna, Inna tace
"Sanusi ina kasan Mahaifiyar Issam?"
"Inna baki ganeh taba koh? Ai wannan matar Babangida ce, kin manta lokacin har kina zolayan sa akan yaje ya auro balarabiya mesa bai aura 'yar k'asar shiba?"
Inna tayi salati tace
"Ikon Allah, wannan matar marigayi ce? Ashe Issam d'an mu neh? Ahh shikenan abu yayi kyau"
Nan dai aka samu akayi hira irin long time no see d'innan, sai can Inna tace
"Sanusi kaji Ikon Allah wai d'an marigayi Babangida shi yakeson Fiddausi"
Abba ya bud'e baki yana mamaki yace
"Lalle kam abu yayi kyau nayi farin ciki da haka, ai lokacin anso a had'a Fiddausi da Issam sai duk suka nuna basaso, gashi yanxu Allah ya k'ara had'a su"
Mum zuciyan tane yayi mugun tsinkewa addu'a takeyi Allah sa Fido ba 'yar marigayi Muhammad baneh, tayi k'arfin hali tace
"Alhaji shin Fiddausi 'yar wajen marigayi Muhammad neh?
"Eh wallahi 'yarsa ce"
Bugun zuciyan tane ya tsanan ta, nan take wasu zazzafan gumi suke sauk'o wa akan fuskan ta dukda sanyin AC split, ji take kamar tace afasa maganar, da zata iya cire son Fiddausi aran Issam data cire dan sam Issam bai dace da Fiddausi ba, but lafian d'anta yafiye mata komai a rayuwa.
Nan Inna ta zayyanawa Abba halin da Issam yake ciki, Abba yace
"Ikon Allah haka abun yayi tsanani, Hajiya Rumah gobe ki turo da magabatan sa a gobe za'a d'aura masu aure a tafi da matarsa, daman da yamma zanyi tafiya but zanyi postponeding tafiyan "
Hajiya rasa abun fad'a tayi, da k'yar ta kirkiro murmushin k'arya tace
"Nagode Alhaji Allah bar zumunci"
"Ahhh haba ba komai wallahi, gobe suzo"
"Toh shikenan Alhaji, nizan wuce"
"Toh shikenan Hajiya, Allah basa lafiya"
Daga nan tafita tama Bala magana, nan suka kama hanyan Abuja hankalin ta duk a tashe, ta rasa abunda yake mata dad'i, a haka har suka iso cikin Abuja, asibitin direct suka wuce har zuwa lokacin Issam bai farka ba. Komawa gida tayi tayi wanka tayi sallah ta dafa abinci ta k'ara komawa asibitin. Daga nan Doctor ya nema ganin ta tahau office nashi, bayan ya nuna mata kujera ta zauna Dr Samaila yace
"Amm Hajiya yaron ki is on very critical condition, but karki tada hankalin ki In Shaa Allah he'll be ok. Ammm abunda yasa nake neman ki shineh zuciyan yaron nan dab yake da bugawa, ina meh rok'an ki da ku taimaka ku masa abunda yake so"
Mum ji tayi kanta yana juyawa da k'yar ta iya bud'e baki tace
"In Shaa Allah Dr zanyi iya k'okarina"