← Book details Hayateeey Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 40

Sashe 23

Hayateeey Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Komawa tayi ta zauna a wajen Issam wanda bacci yakeyi amma tana mai jin numfashin sa, rik'e hannun sa tayi gam tace "Habeebi ya zanyi? If only inada choice da bazan tab'a bari ka aura 'yar gidan mak'iyin muba, I don't know koh idan ka farka kaji labarin wacce kake so 'ya a wajen mutumin daka tab'a tsana neh, Ya Salaam!" tana meh zubda kwallah tacigaba "but ya zanyi? Tunda kana sonta dole na sota kuma laifin iyaye baya shafan yara"

Washegari

A garin Katsina da misalin k'arfe biyu na rana aka d'aura auren ISSAM BABANGIDA BADAMASI DA FIDDAUSI MUHAMMAD SODANGI a sadaki dubu hamsin!!!

Wanda ango still unconscious bai farka ba!

Fido ji tayi duniyan ya mata zafi, su Eesha, Shamcy Inna duk sai murna suke banda ita. 'Yan gidan kuma bak'in ciki kamar ya kashe su.

Wani zazzafan hawaye neh suka sauk'a akan kyakkyawan fuskan ta tace
"In Shaa Allah koh wata biyu bazan wuce a gidan shiba! Na rantse da Allah wallahi bazan barshi ba! Na rantse da Allah sai na masa abunda har ya mutu bazai manta ba!"

Toh fa masu karatu Fido rantsuwan da tayin nan yana tsoratani, shin me zata masa???????? Ku biyo ni!!!!!

By

Nana Fa'ad
*HAYATEEY*

Pure Moment Of Life Writers
[We don't just entertain and educate, we also touch the ❤ hearts of the readers]

_In dedication to Fido Sodangi_

{August, 2017}

Follow me on Wattpad @Nana_Faad. Do read my write-ups and please don't forget to SHARE/VOTE!!!

```Page 36```

Shamcy ce ta tab'a ta tace
"Lafiya kike kuka Adda Fido?
Share hawayen ta tayi tace
"Kukan farin ciki nake Shamcy"
"You sure?"
D'aga mata kai kawai, Shamcy tace
"By the way Yaya Aliyu yana miki magana yace ki same shi a d'akin Yaya Khaleal"
Zuciyan tane ya buga tace
"Yaya Aliyu kuma?"
Shamcy ta maraice fuska tace
"Eh shi, Dan Allah Adda Fido kije idan bakije ba bakisan me zai mini ba zaice ban fad'a miki baneh ya rankwashe ni"
"Karki damu zanje"

Mayafinta ta d'auka ta wuce boys quarters, d'akin Yaya Khaleal ta bud'e tareda sallama zuciyan ta yana mai tsinkewa, ganin sa tayi yana zaune akan kujera yayi crossing leg. Yana ganin ta take ya tashi yana wani irin shu'umin murmushi yace
"Bismillah zauna amarya" tareda nuna mata kujera, zama tayi zuciyan ta name bugawa kamar zai b'ullo. Bayan ta zauna ya d'auko kujera ya zauna daf kusa da ita yace
"Amarya kinsha k'amshi, wani irin gaggawa kukeyi da za'a d'aura aure haka? Koh dukkan ku a matse kuke? But kan a kaiki zan d'an sosa miki inda yake miki k'aikayi"
Jawo ta yayi ta fad'a jikin sa yana mai son had'a bakin sa da nata, damke bakin ta tayi gam, yayi iya k'okarin sa amma ya kasa a karshe wurgi yayi da ita sai gata ta fad'i akan kujera, wani irin kuka ta fashe dashi tace

"Mena maka a rayuwa neh Yaya Aliyu"

Rik'e hannun ta yayi gama kamar zai raba k'ashin ta yana huci yace
"Wato ma bakisan abunda kika mini ba koh? Kin amince zaki aure ni kawai dan ki tarwasa mini rayuwa koh? Kin amince zake aure ni bayan kinada wanda kike so, kin amince zaki aure ni sabida ki raba ni da abunda nafi so a rayuwata? Tuncan daman ina zargin dake da Issam, da kika kwana a gidan sa na tabbata ba irin jagolgolon da beyi dake ba. Da kika shigo gida nah kina saving jikin masa sai dai kash nariga na wanke rabo nah yanxu nabar masa fanko. Yaushe nema da rasuwar Basmah har zakiyi wani auren? Yaushe ma kika gama idda? Na tsane ki Fido! I hate you. Daman Meena tace zata kai k'ara court ina dakatar da ita but yanzu zance ta d'aura daga inda ta tsaya har sai kema kin rasa naki ran, Ki saurare sammaci very soon"

Ya fita yabar mata d'akin, wani irin kuka ta fashe dashi, nan tayi mai isarta ta tattara tafita a d'akin.
Aliyu direct part na Umma ya wuce, yaga basa parlour ya wuce d'akin Umma, tun a bakin kofa yake jin muryan Meena na cewa
"Mtswww nayi a banza wallahi, ai nice da asara gashi yanxu zatayi auren ta wanda yafi Aliyun ma kud'i. Ni wai nakai mata magani yayi destroying mahaifan ta gashi 'yata ta mutu, asara bibbiyu"

Nan yaji zuciyan sa ya buga, take yaja da baya a hankali yabar wajen. Fita yayi ya shiga motar sa amma ya kasa kicking, wani irin bak'in ciki yakeji, kifa kansa yayi akan siteri ya fashe da wani irin kuka.

A ranar aka d'auka Fido aka kaita Abuja, gida neh had'add'e yasha kayan alatu amma koh burge ta baiyi ba. D'akin da aka ce mata nata babban gaske neh, komai na d'akin foreign tun daga kan gado har carpet. Zama tayi tana k'arewa d'akin kallo, Mum ce tashigo d'akin tayi sallama, Murmushi Mum tayi ta zauna a gefen ta tace
"Daughter nah hope d'akin ki ya miki?"
D'aga kanta tayi tace
"Eh Mum yayi"
"Ohk, ki huta yau sai gobe na kaiki wajen mijin ki dan yanzu its late k'arfe takwas ma ya wuce"
"Mum zan iya zuwa yau"
"A'a kibar shi gobe da sassafe sai a kaiki"
"Your wish Mum ba komai"
Shafa fuskan ta tayi tace
"Saida safe, na saka a kawo miki abincin ki yanxu, ni zan wuce asibiti"
"Nagode"
"Ba komai, do take care! Goodnight"
"Night"

Mum fita tayi a d'akin, wani ajiyan zuciya tayi tace "Ina tausaya miki Mum, da kinsan abunda zanma d'anki da baki had'a auren nan ba"

Cire kayan jikinta tayi tashiga toilet tayi wanka, bayan ta fito ta saka night wear ta, knocking na kofan akayi tace
"Bismillah"

Wata yarinya ce 'yar kimanin shekaru goma sha bakwai tashigo da tray na abinci, bayan sun gaisa tace
"Sunana Dije, ni mai aikin gidan ce amarya"
Fido murmushi tayi tace
"Ki kirani da sunana Fiddausi"

"Haba amarya"
"Yeah nafison hakan"
"Toh shikenan amarya"

Bayan Dije tafita ta bud'e abincin, su fried rice, chips, chicken sauce, da pepper soup na kifi. Zama tayi tana cika cikin ta da abinci taji an bankad'o kofa, d'aga kan da zatayi taga S.A, wani irin mak'ure wuyan ta yayi fuskan sa ya canza kala yace
"Wato ni zaki munafurta koh? Wato kin maida ni wawa mara hankali koh? Harda cewa wai na turo iyaye nah dan kin maidani dak'ik'i koh"

Hawaye neh shar suke sauk'a akan kuncin ta tace
"You are hurting me"

Ta iya fad'a da k'yar, kare mak'ure wuyan ta yayi yace
"I'll hurt you even more"
Jin ana k'okarin bud'e kofan ya sake mata wuya da sauri ya lab'e a jikin kofa, Dije ce tashigo, Fido rik'e wuyan ta tayi tana wani irin tari, nan Dije ta zuba mata ruwa a cup tana mata sannu tace
"Amarya sannu, meya same ki haka"
Da k'yar Fido ta iya bud'e baki tace
"Kwarewa nayi"
"Ayyah sannu koh?"
D'aga kai kawai Fido tayi, Dije tace
"Amarya ga kunun madara na manta ban had'u miki d'azu gaba d'aya na kawo miki ba"

"Ayyah ba komai nagode"

Dije tana fita a d'akin S.A ya fito daga inda yake leb'e. Zuwa yayi daf da ita yace
"Tun lokacin auren k'awar ki naga pictures naku kaca-kaca dake da mijinki a social media, but sabida kin raina mini hankali shekaran jiya harda cewa na turo kuma a lokacin na ganku tare tsaban kin raina miki hankali zaki ce mini baki sonsa? A bakya sonsa neh kika aure sa? Me yake dashi dani bani dashi? Me Aliyu yake dashi dani bani dashi? Idan ma kud'i neh sanin kanki neh duk nafisu, wani irin so da kulawa neh ban nuna miki ba Fido?"

"Stop it Suleiman, bana son koh d'aya daga cikin su, ka yarda dani kaine zab'i nah"

Wani tsawa ya daka mata yace
"Just shut up!"
Zuwa tayi daf kusa dashi hawaye yana sauk'a akan kuncin ta tace
"Taya kake tunanin zanso mutumin da yake duka nah, mutumin da baya kula dani, mutumin da bai d'auke ni a matsayin komai ba, mutumin da bai yarda dani ba, mutumin da ya dake ni kuma yayi amfani dani ba tareda amincewa nah ba dukda yana miji nah?"

Shuru S.A yayi yace
"But kina son Issam, you can't lie to me, I can see that in your eyes that you love him"

Murmushi Fido tayi tace
"That's hatred you saw not love, do you really know how much I hate him? Na tsane shi, I hate him! A rayuwata ban tab'a tsanan wani ba kamar yadda na tsana Issam, do you know why?"
"Don't fake any story Fido, karki mini k'arya nasan kina sonshi"

"Idan kana fad'in ina sonsa wallahi wani bak'in ciki nakeji, tayaya kake tunanin zanso mutumin da shineh sanadin mutuwar mahaifi nah?"

S.A kanshi neh ya d'aure yace
"Ban ganeh abunda kike nufi ba?"

Nan Fido ta bayyana masa abunda yafaru, har kuma shine dalin ta na zuwa UK tace

"Bazan tab'a barin sa ba, just give me two months, wata biyu kacal zan rabu dashi, ZAN DAWO GAREKA I PROMISE!"

By

Nana

Fa'ad
*HAYATEEY*

Pure Moment Of Life Writers
[We don't just entertain and educate, we also touch the ❤ hearts of the readers]

_In dedication to Fido Sodangi_

{August, 2017}

Follow me on Wattpad @Nana_Faad. Do read my write-ups and please don't forget to SHARE/VOTE!!!

*Wannan shafin naki neh Maman Nasiba!!! Allah ya raya mana yaran ki*

```Page 37```
Chapter 23 · 0% Book details