← Book details Hayateeey Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 40

Sashe 14

Hayateeey Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bud'e idon ta take a hankali, bin d'akin take da kallo cike da mamaki. Ganin mutum zaune a kan kujera yana bacci wanda gashin kansa bai bari ta kalla fuskan meh kyau ba dan ya d'an rufe masa ido hanci da baki kawai ake hangowa. A razaneh tayi wani irin ihu. Issam atake ya tashi yazo daf kusa da ita yace
"Fido lafiya?"
A hankali incidence d'in ya dawo mata, a tsawace tace
"Where the hell is this place?"
"Don't shout Fido, bakida lafia. Easy gurl calm down"
"WTF! Bansan inda nake ba and kana ce I should calm down???? Anki ayi calm down d'in" ta fad'a a tsawace.
Fita yayi a cikin d'akin, bayan minti biyar ya shigo da tray. Zuwa yayi kusa da ita yace
"Kici abinci kisha magani gobe da safe In Shaa Allah sai na kaiki gida"
"Allah wlhy bazan ci ba" kokarin tashi take amma ta kasa, da kyar dai ta iya ta tashi tacigaba
"Wlhy Allah bazan ci ba, Allah ya isa tsakani nah da kai kuma wlhy yanxu zan tafi gida"

"Kiyi hakuri kici please" ya ajiye mata tray d'in a stool na gaban gadon. Wulli da tray d'in tayi sai gashi su Tea da potatoes duk sun zube plate da cups duk sun fashe. A tsawace tace
"Wlhy Allah yanxu zan bar gidan nan kuma baka isa ka hanani ba kayi kad'an"

Shuru yayi yana kallon ta, da kyar ta iya ta tashi akan gadon, a hankali take iya takawa duk da ciwon kan dake addaban ta, Issam yace
"Haba Fido please kibari sai gobe as you can see ana lightening akwai hadari sosai"
"Ba hadari wlhy koh ruwa ake sai na bar gidan nan"
"Toh ni kuma bazan bud'e miki kofa ba kingani nan" tareda nuna mata keys
"Ga keys na gidan nan a hannu na sai naga ta yadda zaki fita"
Kuka take sosai tana ihu amma duk da haka yaki ya kulata, sai can koh mei ta tuna tace
"But gobe da sassafe zaka kaini gida koh?"
"Eh In Shaa Allah gobe da sassafe bayan kin wanke mini kayan da kika b'ata"
"Zan wanke, yanxu bacci nake ji"
"Yawwa toh kwanta"

Kan gadon ta koma ta hau ta kwanta, tace
"Kai baza kayi bacci baneh koh zaka sakani a gaba kana kallo na neh?"
"Ohk bara naje d'aki na na kwanta, good night" Murmushi ta masa tace

"Night"

Fita yayi a d'akin yana murmushi a zuciyan shi yana cewa "Lalle wai yarinyan nan wayo zata mun"
Kujera ya d'auko ya ajiye a gefen kofan d'akin ya zauna yana gadin ta. Ita kuma Fido ta rantse da Allah a daren nan zata bar gidan. Tana jin motsin sa a kofan d'akin wanda ya tabbatar mata Issam bai shiga d'akin sa ba. Sai can kamar karfe d'aya bayan taji shuru ta tashi a hankali, a wajen kofan d'akin taga Issam yana bacci akan kujera, hannu ta saka a cikin aljihun rigan sa ta d'auki key holder. A sanda ta fita a gidan har takai bakin gate, wani tsoro taji dan garin ana wani irin iska tareda lightening hadari ya had'u sosai. Duk keys d'in take gwada wa har Allah yasa ta bud'e. Tana fita ruwa mei karfin gaske yafara saukowa. Wani sound na thunder akayi da karfi wanda ya tsorata ta, sound na thunder shi ya tada Issam daga baccin da yake, a take yashiga cikin d'akin to his very own surprise yaga wayam ba kowa a ciki.

Fido gudu sosai take cikin ruwan, ga wani uban tsoron da takeji, wani irin haske tagani kan ta ankara taji an buge ta, Issam dake baya yayi Ihu yace "HAYAATEEY" Kan ya iso wajen motar daya bugeta yayi ribas da gudu yabar wajen..

Issam a guje yazo wajen yana jijjigata, dukda karfin ruwan da yake sauka bai hana ganin jinin da yake fitowa a goshin taba, Hawaye yake kamar ba Issam namiji mei ji da kansa ba yana cewa
"Hayaateey dan Allah ki tashi kece RAYUWA TA, dake nake kwana dake nake tashi. Believe me, you are the one,Whom my heart finds,Whom my mind reminds me of,Whom my destiny wants,Whom I love the most! KECE MY HAYAT!!!Dan Allah ki tashi"

Ganin bata koh numfashi ya d'auke ta cak ya kaita gidan sa ya kwantar da ita a kan gado. Gashi da mota d'aya yazo dashi Katsina kuma motar d'azu sunyi accident dashi. Saka hannun sa yayi cikin dogon gashin kansa ya furta "Ya Salaam". Nan take kuma ya tashi ya d'au First aid box yafara mata treating inda ta buga goshinta. Take yayi traating ya manna mata bandage.
D'aukan wayar sa yayi yayi dialing number Dr Naeemah ya ji number a kashe. Duba time yayi yaga karfe ukun dare. D'auko kujera yayi ya zauna yana kallon ta koh Allah zaisa ta tashi a haka har karfe biyar yayi bai runtsa ba. Ganin ana kiran Sallah a take ya k'ara dialing number Dr Naeemah Allah yasa yashiga. Ringing d'aya ta d'auka tace
"Issam lafia kuwa?"
Muryan sa yana shaking yace
"Naeemah ba lafia ba, jiya da daddare ta fita mota ya bugeta and she lost alot of blood, nayi treating nata gashi har yanxu bata farka ba"
"Ohk ka jirani yanxu zanzo"
"Ohk sai kinzo nagode sosai"

"No thanks anything for you dear"
"Ohk" yace kawai tareda katse wayan...

Nan da minti goma sha biyar sai gashi Naeemah tashigo idan, data shigo a lokacin ya idar da sallah subh. Bayan sun gaisa ta d'auka jinin Fido tace
"Zanje Lab nayi PCV ta, idan har jinin ta low sai mu gwada naka a saka mata but for now zan saka mata drip"
"Ohk toh ba matsala"

By

Nana Fa'ad
*HAYATEEY*

Pure Moment Of Life Writers(p.m.l)

[We don't just entertain, we touch the ❤ heart of the readers]

In Dedication To Fido Sodangi

{July,2016}

```Page 24```

Aliyu a daren yaje yata kiran number ta baya shiga, daga baya yayi deciding ya buga musu kofa. Bayan ya buga kofa Faruq ya bud'e mishi kofan, bayan sun gaisa Aliyu yace
"Ummm sunana Aliyu, brother Fido"
"Ohh Allah sarki, ya gida?"
"Alhamdulillah lafiya kalau, Fido nake nema kuma I tried calling her but her number was switch off kuma munyi da ita akan zanzo na d'auke ta"
"Ohhh ayyah kasan daman ba wanda zai kwana a gidan and d'azu naji kamar Eesha tana cewa zaka zo ka d'auke ta. Lemme talk to her"
"Ohk Nagode"

Faruq ya shiga ciki sai kusan bayan minti biyu ya fito tareda Eesha, Eesha tana ganin sa tayi murmushi tace
"Ango kasha k'amshi, baka had'u da amaryar kaba?"
Aliyu ya d'an sosa kansa yace
"Wallahi kuma munyi zanzo na d'auke ta"
"Kuma wallahi haka ta fad'a mini har tace bara ta fita da wuri dan bakasan actual gidan nan ba, ka kirata?"
"Yeah na kirata but her number a kashe"
"Ya Salaam! Ohk give me some seconds let me call my sis koh ta koma gidan mu, mushiga daga ciki"
"Aiit nagode"

Bayan sun shiga ciki suka zauna a parlour.

Shiga d'aki tayi ta d'au wayarta tafito parlor, number Anty Halima tayi dialing, bayan ya shiga ta saka a loudspeaker
"Hello amarya lafiya kuwa?"
"Anty Halima ina Fido? Tana gida neh?"
"A'a Fido fa bata nan, tace mun Yayan ta zaizo ya d'auke ta a gidan ki, mesa kika tambaya?"
"Wlhy Yayan tane yazo kuma batanan and number ta akashe"
"Ikon Allah, toh ina tashiga? Allah sa lafiya"
"Ameen Anty Halima"
"Ki kira wasu koh Allah zaisa kiji labari"
"Ohk toh nagode, bye" ta katse wayan.

Eesha ta kalla Aliyu tace
"Kaji bata wajen, but bara nakira Anty Rif"
A take tayi dialing number Anty Rif itama yayar Eesha ce, tana d'aga wa tace
"Amarya lafiya kika kirani hope baki manta komai a gida ba?"
"Lafiya kalau wallahi, amm daman Fido nakeson na tambaye ki koh kin ganta da zaki bar gida nah"

"Ohh Fido, da zan wuce na ganta tsaye da Issam abokin Faruq. Har naji yana maganan zai kaita gida"
"Ohk toh Nagode" ta katse wayan.

Zuciyan Aliyu neh yake bugawa, tabbas ya ganeh Issam dan da akayi posting pictures nasu a Facebook yaga an saka sunan sa. Take yace ki kiramun number Issam d'in.
Take Eesha tayi dailing amma shima switch off. Tace
"Yaya Aliyu number sa akashe, inaga ya kaita gida neh. Tabbas ba inda Fido zata wuce gida ya kaita"
Faruq yace
"I trust my friend ba inda zai kaita sai gida, kaje gida In Shaa Allah tana gida"

Aliyu duk yadda yaso ya b'oye b'acin ransa amma sanda suka gane. Yayi murmushin dole yace
"Ba komai nagode"

Tafiya yake a cikin motar sa amma zuciyan sa yana me bugawa, tsananin kishi ya rufe masa Ido, buga siterin motan yayi yace "Auren mu saura one week amma tana kula wani, wallahi Allah sai ta ganeh kurenta"

A haka har ya isa gida, yana shiga cikin gidan wani irin parking yayi ya fito a motar da sauri, direct b'angaren Inna ya wuce. Yana shiga ya ganta da Shamcy suna kallo a parlour. Inna tace
"Aliyu lafiyan ka kuwa? Har yanxu baka wuce gidan ka ba?"

Bai bata amsa ba yace
"Inna ina Fido?"
"Kaji ja'irin yaro, toh Fido bata gidan nan gidan auren k'awarta zata kwana"
"Inna kina nufin Fido bata dawo gidan nan ba?"
"Toh karya zan maka neh?"

"Kee Shamcy ina Yayar ki?"
"Yaya Aliyu bata dawo gida bafa, ka manta yau ana auren k'awar ta Eesha? Sai gobe zata dawo"
"Bata dawo gida bafa kukace?"
Inna ta harare sa tace
"Ka fara zautuwa neh? Sau nawa zamu fad'a maka bata gidan nan tana gidan aure"
"Inna bata wajen auren dan daga can nake, ance wai an ganta tareda wani"
"Kaga Aliyu bana son shirme, toh Fiddausi d'in binshi zatayi gidan sa sabida an gansu tare? Maza ka tashi ka tafi gidan ka dare yayi"
"Inna baki yadda dani ba kenan?"
"Ban yadda ba, kuma idan ka k'ara cewa Fido ta fita da wani toh ban yafe ba duniya da lahira, kai Allah ya isa ma"

Tsantsan mamaki neh ya cika Aliyu, yace
"Shikenan Inna sai da safe"
Tura d'ankwalin ta gaban goshi tayi ta nuna masa kofa tace
"Otttt"
Chapter 14 · 0% Book details