← Book details Hayateeey Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 40

Sashe 29

Hayateeey Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da misalin k'arfe goman dare Fido duk tsoro ya cikata gashi bataso taje d'akin Issam tace "Yanzu idan naje d'akin yaron nan sai ya raina ni ai, but ai na fad'a masa ya fitar da magen gidan nan nasan yanzu ya fitar dasu"
Kwanciya tayi akan gado tayi addu'oin ta tashafa, koh minti goma batayi da kwanciya ba tafara jin kukan mage, magen ma ba d'aya ba. Nan take ta taso akan gadon ta kunna wutan d'akin, ganin kukan su ya k'aro atake ta d'au wayarta ta kunna touchlight a guje tafita a d'akin. A guje taje zata shiga d'akin Issam taji a rufe, wasu hawaye neh su sauk'a akan kuncin ta lokacin da taga wani bak'in mage, bugun kofan takeyi kamar zata b'alla.
B'angaren Issam kuma dariya yake kamar cikin sa zai b'alle, sai can ya tashi yaje bakin kofan yace
"Waye neh?"
Nan take tace "Dan Allah dan annabi please open the door Issam"
"Why should I? Wani abu neh?"
"Cats!"
"Toh sai na miki me? Kije ki d'akin ki mana"
"Dan Allah Issam"
A tsawace yace "Kefa bazan bud'e ba"
Wani irin kuka ta fashe dashi dataga magen sun kai uku tsaye a gaban ta suna kuka, tana kuka tace
"Dan Allah Yaya Issam ka bud'e mini"
Wani irin dariya yayi data k'irasa da Yaya Issam, yace
"Yaya Issam kuma?"
Tace "Kayi hak'uri dan Allah, haba Yaya Issam! Haba Swthrt"
Wani irin dariya yayi yace
"Uhum"
"Dan Allah Nurul Qalb, Nurul Hayat, Miji nah kaina bud'e mini mana"
Ganin magen na neman hawwa kanta tayi wani irin ihu dayasa ya bud'e kofan atake, fad'awa jikinsa tayi tana wani irin kuka, ce mata yayi
"Zaki k'ara mini abunda kikayi d'azu, wai nashiga tricycle koh"
Nan take ta girgiza kanta tana hawaye tace
"Kayi hak'uri wallahi Allah bazan k'ara ba"
"Idan ma zaki k'ara repeating nasani na fitar dake a d'aki na su hau kanki daman sun jima basuci abinci ba kinga sun samu nama"
Kama sa tayi tace "Ka yarda dani wallahi Allah bazan sake ba, na maka alkawari"
"Shhhh toh shikenan yi shuru Hayateey". Yana mai bubbuga bayan ta ita kuma ta rungume sa sosai. A haka ya lallashe ta ya kwantar da ita akan gado sai kakkarwa takeyi, shima kwanciya yayi ya rungoma ta sosai yana cewa "Yi shuru Hayateey mijin kine" yayi wani shu'umin murmushi..

Da asuba ta farka tajita a jikin wani rungume da ita, wani irin ihu tayi dayasa ya farka yace
"Ke lafiya"
"Lafiya kake tambaya na? Who gave you the audacity ta touch me?"
"And who the hell gave you the audacity to enter my room har ki kwanta akan gado na ehhh?" Ya fad'a mata a tsawace.
Shuru tayi tana kallon sa dan bata tab'a tsammanin zai mata tsawa ba, sauk'a tayi akan gadon without uttering a word tafita a d'akin, wani tsoro tsoro takeji amma akan ta koma d'akin sa gwara magen su cinye ta, tana shiga d'akinta ta rufe kofan ta tana sauk'e numfashi. Duk da tana jin kukan magen haka ta dage tayi alwala tayi sallah, tana idarwa tabi lafiyar gado ta kwanta.

Da misalin k'arfe tara na safe Issam yashigo d'akin ya ganta har yanzu shakar baccin ta takeyi, bubbuga ta yake da hankali nan take ta tashi a firgice, kallon ta yake yace
"Wai ni ke baki iya tashiwa a bacci cikin kwanciyar hankali ba kullum a firgice kike tashiwa?"
Guntun tsaki taja tace
"Toh ina ruwan ka dani?"
Duba agogon da zatayi taga k'arfe tara da rabi, nan take ta taso akan gadon ta cusa hannu cikin sumar kanta tace
"Ya salaam! Muna da meeting k'arfe goma"
"Sai ki tashi ki shirya ai"
Fita yayi a d'akin ita kuma ta cire night gown nata ta fad'a toilet tayi wanka, fitan ta taga foodflakes da flakes na tea, kan gadon ta kuma ga kayan daya fito mata dasu. Murmushi tayi ta zauna ta shafo cream ta saka kayan daya ajiye mata akan gado, dogon habbaya neh bak'i da blue ,sai hijabi blue daya ajiye mata, zama tayi ta bud'e foodflakes d'in taga chips da kwai, had'a tea tayi taci da chips. Sanda taji ta k'oshi kan ta tashi tayi brush ta zura hijabin a jikin ta, wani dogon tsaki taja tace "Taya zan had'a abaya da hibaji kuma" gyale ta nema babba ta yafa ta fesa perfumes nata.
Zuwa tayi ta same shi a d'aki ya shirya yayi kyau abunsa kamar a sace shi a gudu. Suman kansa sai yalk'i yake yasha gyara, ga sajen fuskan sa wanda ya kwanta yayi luguf luguf, ita kanta tasan ya had'u iya had'uwa, murmushi ya mata yace
"Mss Contour kin shirya?"
"Yeah nayi latti ma"
Duba agogon hannun sa yayi rolex yace
"Gaskia kam yanzu past ten, koh da yake akwai african time, please ki ajiye ni a gidan mai na mana"
Kallon uku saura tara ta masa tace
"Bakaji nace maka nayi latti ba?"
"I know but tunda hanya d'aya neh ai ba matsala"
Kamar tace baza tayi dropping nasa ba sai ta tuna da abunda ya mata jiya da daddare tace
"Alright ka same ni a mota" tayi ficewar wa, abun ma dariya ya basa yadda take wani jin kai, girgiza kansa yayi ya d'au perfumes a wardrobe nasa ya fesa. Wani uban horn take danna wa sai gashi ya fito ya bud'e gaban mota yashiga, wani dogon tsaki taja tace
"Shiri sai kace mace Allah sawwaka"
"Dad'i na dake yawan tsaki kamar 'yar tasha"
"Ba yau kafara fad'an haka ba balle ya dameni yaro"
Wani dariya yayi yace
"Aww nine yaro? Daga Yaya Issam, Swthrt, Nurul Qalb, Nural HAYAT, Miji nah yanzu kuma yaro?"
Tsaki ta kuma ja tace "Whatever!"
"Tsaki sai kace 'yar tasha"
"Cikakkiyar 'yar tashan neh ai"
Da hakan har ta sauk'e sa a gidan mai, kallon ta yake with so much tenderness in his eyes yace
"Mss Contour hope zakizo ki d'auke ni?"
"Akwai lectures da zanyi 4-6 so idan ka gama ka hau a daidai ta tsahu"
"No ba damuwa zan jira ki Hayateey"
"Mtss sai kata jira ai kaga koh zanzo ni"
Murmushi yayi yace
"I know definitely you'll come"
"Mts kaga fita mini a mota nah nayi latti Mallam"
Kallon gefen ta take ji tayi kawai yayi pecking nata yace
"Take care Hayateey"
"Mtsw fita please"
Murmushi yayi ya fita a motar tareda d'aga mata hannu koh kulasa batayi ba ta fisga motar abun ta.

Tun k'arfe biyu tagama duk abunda zatayi a makarantan, driving take zataje ta gida tace "Naje gida ma nayi me? Bara naje wajen Mummy kawai". Reverse tayi da motar ta direct gidan baffa Umar tawuce, wan Mummy wanda a yanxu take zama a gidan sa, da sallama tashiga gidan lokacin Mum tana parlour tana shan fura, hugging na Mum nata tayi tace
"Mummy nayi missing naki"
Murmushi Mummy tayi tace
"I missed you too durling"
"So ya mai gidan ki?"
"Lafiyan sa kalau Mummy"
"Mutumin kirki, jiya ma yazo ya gaishe ni kuma kullum sai ya kirani a waya, Allah masa albarka"
"Hmmm Ameen"

Haka sukata hira taci abinci sai da can yamma Mummy tace
"Fiddausi yamma tayi ki tashi ki tafi gidan ki"
Ji tayi kamar karta tafi amma ba yadda ta iya dole ta tashi ta shirya, bayan ta shirya tace
"Toh Mummy ni zan wuce"
"Toh Mamana Allah miki albarka, ki zauna da mijin ki lafiya kinji? Kuma ki zama mai rik'e sirrin mijin ki"
"In Shaa Allah Mummy nagode"
"Ba komai ki gaida shi"
"Zaiji"

Driving take ta duba agogon motar taga k'arfe biyar da rabi, ji take kamar ta wuce gida ba tareda ta tsayawa d'aukan saba, har ta wuce gidan mai d'in ta k'ara reverse, a can nesa da gidan mai d'in ta tsaya tana mai kallon sunan gidan mai d'in wanda aka rubuta *ISAL* , tunani take tasan sunan shi Issam toh AL d'in me yake nufi oho? Wayarta ta d'au ta danna masa kira, d'auka wansa yace
"Mss Contour kinzo neh?"
"Mts kafito idan ka k'ara minti biyu wallahi tafiya ta zanyi"
"Yanzu zan fito please karki tafi kibarni Hayateey"
"Mts sai kayi sauri ai Mallam"
"Dad'i na dake yawan..." Bai k'arasaba ta tare numfashin sa tace
"Tsaki kamar 'yar tasha koh? Sau nawa zan fad'a maka cikakkiyar 'yar tashan nema ba kamar 'yar tasha ba"
"Ohk naji gani nan I'm on my way, banso kina masifa cox yawan masifa na tsufar da mutum and banso ki tsufa, dan idan kin tsufa zan auro wata neh ba ruwa na"
"Ka auro uku mu zama mu had'u bazai dame ni ba, yanxu kaci minti biyar wallah natafi" ta katse wayan, tada engine na motar tayi kawai taga ya bud'e kofa ya shiga. Nan take ta fisga motar tana wani irin gudu, tace
"Mesa zaka k'arar mun da credit na wayana bayan kana kan hanya"
"Sabida ban gajiya dajin voice naki kuma da kike maganar k'arar miki da credit na waya naga jiya jiya kika cire kud'i a bank"
Wani deadly look ta masa tace
"And so bloody what idan jiya naje bank? It's your responsibility ka d'au nauyi nah"
"Koh?"
"Hell yeah"
Cire wallet yayi a aljihun sa ya ciro ATM card kusan guda biyar, mik'a mata d'aya yayi yace
"Duk time da kike needing kud'i ki cire"
Karb'an ATM card d'in tayi a zuciyar tana cewa "Lallai yaro wallahi sai kayi dana sanin bani ATM card naka da kayi". Wani murmushi tayi tace
"Are you sure about this?", d'aga mata kai yayi without uttering a word, tace
"What's the password?"
"1987"
Murmushi tayi tace "Ohk"
Chapter 29 · 0% Book details