← Book details Hayateeey Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 40

Sashe 33

Hayateeey Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Hayateey ki kwaso abincin muci a k'asa tare"
Ba musu tace masa "Toh" ta kwaso abincin zuwa k'asa. Zama sukayi Fido tayi serving nashi, Issam yace
"Ni zan baki da hannu nah Mss Contour"
Murmushi tayi tace "Ba komai My Qalb"
Haka ya ringa feeding nata itama tana basa abincin a baki, bayan sun gama ci yace
"Zanje masallaci ki shirya zamu fita"
"Fita kuma zuwa ina?"
"Kedai ki shirya" Yayi pecking nata. Yana fita ta kwashe food flakes d'in takai kitchen ta wanke su tas, daga nan tayi alwala tayi sallah. Tana idarwa sai gashi yashigo d'akin da sallama yace
"Mss Contour sai yanzu kikayi sallah? Maza tashi toh ki shirya"
Ba musu ta tashi tace
"Ohk excuse me zan canza kaya"
Murmushi yayi ya matso kusa da ita yace
"Ni nakeso na zan canza miki kaya yau"
"Ohhh I will love that Dear ka canza". Take ya d'aga ido ya kalle ta cox that shocked him to his very core yace
"You sure?"
Tace "Very sure"
Shi da kansa ya cire mata kaya a wardrobe superwax d'inkin riga da zani, tana ganin zani tace
"Gaskia ka maida kayan nan bazan saka ba"
"Mesa?"
"Baka ganin zani neh? Nidai banso kuma ban iya d'aura wa ba"
Murmushi yayi yace "Don't worry Hayateey zan d'aura miki"
"Nidai ban yarda ba"
"Shhh nace zan d'aura"
"Ohk toh"
Murmushi yayi yana sosa suman kansa yace
"Yanzu zan cire kayan first koh?"
Ita abun ma dariya ya bata tace
"Eh koh akan kayan jiki na zaka d'aura?"
Ya girgiza kansa yana mai sosa suman kansa, matsowa yayi kusa da ita yace
"Ummm ta ina zan fara?"
Tayi dariya tace "Ko ta ina ma"
Da yake doguwar riga ce ya d'aga ta sama yace "D'aga hannun ki" Ta d'aga, haka ya cire rigan ta sama ya rage daga ita sai bra da pant ajikin ta. Komawa baya yayi yana mai k'are mata kallo, juya masa baya tayi tana murmushi tace
"I hate that look"
Matsowa yayi yayi hugging nata ta baya yace
"Mss Contour I Love You So Much"
Juyota yayi suna facing juna yana kallon cikin idon ta yace
"My heart says that you like me, My eyes says that you feel something for me, My mind says that you think of me, But till now you are quiet why?"
Ba shiri kawai yaga hawaye suna sauk'a akan kuncin ta nan take ya rikice yace
"So sorry Hayateey, fad'a mini meke damun ki, koh maganar da nayi neh ya b'ata miki rai?"
Girgiza kanta tayi tace "A'a"
"Then please tell me the truth, meke damun ki?"
"Babu"
"Are you sure?". Ta d'aga kanta, hugging nata yayi yana panting na bayan ta yace
" Banson na ganki kina kuka, yana breaking heart nawa idan baki sona neh ki fad'a mun"
"Idan bana sonka zaka sake ni neh?"
"Bazan iya ba, but if you'll be happy zan sake ki dan farin cikin ki shine nawa. Is rather na zauna cikin kunci kina farin ciki than ni ina cikin farin ciki ke kuma kina cikin kunci, I can't take that because your happiness means the world to me"
Hugging nasa tayi sosai ta fashe da wani irin kuka wanda ya k'ara rikita shi, sai sannu yake mata har ya samu tayi shiru, bayan tayi shiru tace
"Baza saka mini kayan ba koh mun fasa fitan?"
"Bamu fasa ba"
Rigan ya d'auko ya bud'e zip ya saka mata ya rufe zip d'in. Zanin ya d'auko sai faman ya d'aura mata yake amma ya kasa haka yata zagaye-zagaye sun kusan minti biyar yana abu d'aya ita kuma sai dariya take masa, haka suka kusan minti goma sha biyar suna abu d'aya ya kasa d'aura wa. Duk suka zube akan gado suna sauke numfashi take kuma suka fashe da dariya tace
"Shine wai ka iya?"
Sosa suman kansa yayi yace
"Wallahi before na iya mantawa nayi"
Dariya tayi tace "Lies ba wani, tsaya kaga na d'aura"
Tasowa tayi itama haka tayi ta k'okarin d'aura wa da k'yar dai ta iya ta d'aura gaba dogu baya guntu. Tsaki taja tace
"Nidai zan cire kayan nan"
"A'a karki cire ya miki kyau ki d'aura d'an kwali mu tafi"
Ba yadda ta iya haka ta d'aura d'an kwali ta shafa powder ta yafa gyale tace
"Done"
"Good to go?"
"Yeah!"
Kama hannun ta yayi suka fita haraban gidan yace
"You drive or I drive?"
Murmushi tayi tace "You drive"
Bud'e mata gaban motar yayi ta shiga ta zauna ya rufo kofan yadawo driver seat ya zauna ya tada motar. Gidan su Aliyu first ya fara kaita, Inna ba k'aramin farin ciki tayi ba ganin Fido ta k'ara kyau tayi haske tayi jiki, haka suka shiga koh wani side suna gaisuwa. Mami ce ta karb'e su da fara'a su Umma da Hajja koh kulasu basuyi ba dan bak'in ciki. Sai bayan magrib kuma suka je gidan Eesha, Eesha tana ganinta ta rungume ta suka shiga ciki suka bar Faruq da Issam a parlour. Suna shiga cikin d'aki Eesha da k'aton cikin ta tace
"K'awata naga kamar kema fa kun samu k'aruwa"
Fido tayi dariya tace "Hmm ciki a ruwa ake sha neh?"
"Kardai har yanzu bai tab'a kiba?"
"Ba abunda ya shiga tsakanin mu ke har yanzu kuma bana fata wani abu ya shiga tsakanin mu"
"But why Fido? Wallahi kina b'oyewa your eyes revelled that kina son Issam so stop pretending"
"Mu bar maganan nan please". Haka dai suka ta hira har sallah'n isha'i su basu koma gida bai sai k'arfe tara na dare. Tun a mota Issam yake ta mata magana amma hankalin ta yana wani waje daban har suka iso gida. Kowa d'akin shi ya shige, Fido tana shiga d'akin ta wayarta ya soma ringing, hannun ta yana shaking tayi picking call d'in tace
"Kunzo neh?" Can kuma muryan ta yana shaking tace "Ohk toh ku shigo". Tana katse wayan ta fashe da wani irin kuka, yi take kamar wanda za'a yanka kanta...

_One hour Later_

Da hankali take takawa zuwa d'akin Issam dan kafarta ya mata nauyi da k'yar take iya d'aga wa. Ganin Issam tayi kwance akan gado an d'aure sa da kafa da hannu ga manya manyan 'yan daba akansa. Zuwa tayi tana kallon sa, murmushi ya mata yace
" Hayateey nasan dama kina shirya mun something like this, koh mai na fad'a miki baza ki tab'a yarda ba amma inaso ki sani no matter what you did to me I'll always love you"
"Ka fad'a mini waye neh ya cewa ogan ku a kashe Dad nah?
" Komai yana cikin safe da nasan kinsan dashi"
Juyawa tayi tana hawaye ta bud'e wardrobe nasa ta d'auka safe d'in tazo gaban sa tace
"What's the password?"
"Fiddausi"
"Duk da yadda kake sona Issam bazan iya rayuwa da mutumin dayayi sanadiyar mutuwar Dad na ba, ni bazan kashe kaba but zan maka abunda har ka mutu baza ka tab'a mantawa ba. Kasan me zan maka? Za'a yanke gaban ka shikenan naka ta k'are, bakai ba k'ara aure, bakai ba jin dad'in rayuwa, bazaks tab'a ganin jinin ka ba"
Ba k'aramin mamaki yayi ba, shi duk a tunanin sa kashesa zatace ayi but jin maganganun ta that shocked him to his very own core, Murmushi yayi yace
"Nagode"
Ta juya ta kallesu tace "Kuyi aikin ku".

Tana fita a d'akin taji yayi wani irin k'ara mai firgitarwa

Nana

Fa'ad

#MunaMugunTare
*HAYATEEY*

Pure Moment Of Life Writers
[We don't just entertain and educate, we also touch the ❤ hearts of the readers]

Written By Nana Fa'ad

_In dedication to Fido Sodangi_

{Sept., 2017}

Follow me on Wattpad @Nana_Faad. Do read my write-ups and please don't forget to SHARE/VOTE!!!

```Page 46```

Da gudu tashigo parlour'n tana wani irin kuka a lokacin Inna tana parlour tana dama fura ta rungume Inna, Inna hankalin tane yayi masifan tashiwa ganin irin kukan da Fido takeyi, Inna tace
"Fiddausi lafiya? Meya sameki kike kuka haka?"
Girgiza kanta Fido tayi tacigaba da kukan, Inna tace
"Koh Issam neh?" Nan take ta d'aga kanta, Inna hankalin ta ya k'ara tashiwa tace
"Mutuwa yayi?" Nan ma ta girgiza kanta. "Bashida lafiya neh?" Still ta k'ara girgiza kanta, a tsawace Inna tace
"Toh dan ubanki ki fad'a mini dalilin kukan ki bayan da magriba kukabar gidan nan"
"Inna Issam yacuce ni, yaci amanata. Could you imagine bayan mun dawo gida naga wata arniya a gidan wai sunan ta Rita harda yaro a hannun ta, na tambaye sa wacece kinsan bud'an bakin sa abunda yace?"
Inna tayi salati tace "Meya ce?"
Tana wani irin kuka tace
"Wai budurwarsa ce kuma yaron nasa ne, shine nace sam toh bazata zauna a gidan nan ba ya zab'a koh ni koh ita. Ya mini dukan gaske yace nafita nabar masa gidan sa"
Inna tayi salati ta godewa Allah tace
"Ikon Allah! Haka kukayi dashi? Ashe daman haka Issam d'in yake bashida mutunci? Gobe In Shaa Allah zan ma Sanusi magana ya kirasa yaji ta bakin sa"
"Ku barsa kawai Inna ni na hak'ura dashi"
"Sai muce ya aiko da takardan saki toh"
Nan kuwa kukan ta ya tsaya cak, ita tama manta ashe bai saketa ba, a hankali ta furta "So stupid of me". Inna tace
"Me kikace?"
Cusa hannu tayi cikin sumar kanta wani irin jira na d'aukar ta, Inna tace
"Idan bakiso ya sake ki toh zamu kirasa ayi sulhu karki damu kinji jikalle"
Chapter 33 · 0% Book details