← Book details Hayateeey Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 40

Sashe 21

Hayateeey Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin d'akin su tashiga lokacin Fido tana marking scripts na students nata, ganin Shamcy tayi tana fesa perfumes tace
" 'Yar yawo ina kuma zuwa da yamman nan"
Tana murmushi tace
"Anzo waje nane".
Fido ajiye Pen na hannun ta tayi tace
" Ikon Allah, waye haka"
"Idan kin fita zaki gansa"

Fita tayi ba tareda ta jira meh yararta zata kuma fad'a ba. Cikin zumud'i taje parlour tayi sallama, amsawa yayi yana murmushi yace
"Sister nah yakike"
Inna sai kallon ikon Allah take tace
"Ni Shamsiyya ai farko na d'auka baya jin hausa ashe har fultanci yanaji, d'auka wa nayi balarabe neh koh d'an India"

Dariya Issam yayi yace
"Inna mahaifina fulani neh mahaifiya ta 'yar Yemen"
Inna tace "Yawwa shiyasa"
"Shiyasa meh Inna?" Ya tambaye ta
"Kana da kyau sosai"
A dai-dai lokacin Fido tafito a d'aki, to her very own surprise taga Issam a parlour suna hira da Inna.
Issam yace "Inna toh ai kamannin mahaifina na biyo sai dai hasken Mum nah"

Inna ta washe baki tace
"Mashaa Allah, Yaro wajen Shamcy kazo, idan sonta kake da aure sai nayiwa Abban ta magana"

Murmushi yayi yace
"Inna ai Shamcy k'anwa tace"
Inna ta b'ata rai tace
"Me kake nufi? Toh me yakawo ka gidan nan"
"Neman aure" tareda d'aga idon sa ya kalla Fido
Inna tace "Neman auren wa?
" Yayar Shamcy"
Shamcy mamaki da kunya neh yacikata, Fido kuma nan take ta shige d'akin ta.
Inna tayi murmushi tace
"Kai amma gaskia nayi murna, ai kullum ina mata addu'a Allah bata mijin da yafi shegen Aliyun nan, yanxu zamuga idon mutanen gidan nan"

Issam murmushi yayi yace
"Inna zan wuce"
"Toh Shamcy shiga ki kira Fido ta rakasa".
Issam ya tsaida Shamcy yace
"No ki barta ba komai"
Cire kud'i yayi a aljihun sa ya mik'awa Shamcy yace
"Sister na gashi kisaya kayan makeup sauran ki sayawa Inna goro"
Duk yadda Shamcy tayi dan ganin bata karb'a ba yasata dole ta karb'a. Inna sai saka masa albarka take.

Tun daga ranar kusan kullum sai Issam yazo gidan, duk zuwan shi ba abunda ya tab'a had'a shi da Fido dan tana ganin sa zata b'ata rai. Inna har yakai ta gane kullum take masa nasiha akan In Shaa Allah Fido watarana zata soshi.

A ranar ba kowa a gidan Fido tana zaune tana karanta hisnul muslim Issam yayi sallama, nan take ta gyara gyalen ta tabashi izinin shigowa.
Neman waje yayi ya zauna, koh d'aga kanta batayi ba balle tasan yana yi. Kusan minti talatin ba wanda yace wa wani k'ala. Zuwa yayi ya zauna a k'asan carpet daf kusa da kafarta yace
"Fiddausi"

Mamaki abun ya bata dan a rayuwa zata iya k'irga sau nawa ya k'irata da Fido balle Fiddausi
"Lafiya?" Tana meh d'aga masa gira
Ya rasa ta yadda zai fara b'ullo mata zuciyan shi yana tsinke wa yace
" Inasu Inna?"

"Mtswww sai kazo gabana zaka tambaye su? Toh baso nan sun fita" tareda tashiwa ta barsa a wajen. Zama yayi ya rasa abunyi kuma ya kasa tafiya, sai can kusan minti goma tafito da cup da coffee a kitchin. Zaro idonta tayi tace
"Aww har yanxu baka tafi ba?"
Shuru yayi ya rasa amsar da zai bata, neman waje tayi can nesa da inda take zama na farkon ta zauna.
"Please mik'a mini laptop d'ina" ta fad'a masa dayake yana kusa dashi. Ganin bashida niyar mik'a mata yasa ta taso da coffee a hannunta ta tsuguna zata d'auka kawai Cup d'in ya kife coffee ya zube mata a hannu, wani irin ihu tayi tace
"Wayyoo Allah"
Nan take Issam ya rikice yana mata sannu yana mai hura mata hannun ta da bakin sa, sai cewa yake
"Does it pain, yana miki zafi koh?"
Tsawa ta daka masa tace
"Ina ruwan ka da if I am in pain, and what stupid question is that?
Kallon ta yake ido cikin Ido yace
" It will break my heart if you're in pain"
"What!?" Ta tambaye sa dan abun ya bata mamaki, cikin idon ta yake kallo with much tenderness yace
"If you were in pain, it will break my heart!"
Matsowa yayi sosai kusa da ita yacigaba
"And I will die if you ever In pain"

K'ara matsowa yayi sosai wanda suke jin numfashin juna yacigaba

Opppps be3 low

Ana complain ina pages kad'an kuyi hak'uri rashin time neh but In Shaa Allah cikin two weeks zan gama or even less than that!

#oneLove

Comment 07034419520
*HAYATEEY*

Pure Moment Of Life Writers
[We don't just entertain and educate, we also touch the ❤ hearts of the readers]

_In dedication to Fido Sodangi_

{August, 2017}

Follow me on Wattpad @Nana_Faad. Do read my write-ups and please don't forget to SHARE/VOTE!!!

*You yell at times and you lose your mind. You get wild and you throw a fit too. But all that is excused because today is dedicated especially to you! Happy birthday Meenarh Parrot and Sadnaf*

```Page 33```

K'ara matsowa yayi sosai wanda suke jin numfashin juna yacigaba

"Because there could be nothing left in me without you. Because if you were in pain, then my heart will would explode into a million pieces of broken glass. I wouldn't be able to breathe without you, I wouldn't be able to live without you. Because you are my HAYAT. Because i-i ----- Issam, I L-O-V-E yhu!!!"

Ya fad'a yana mai kallon cikin idon ta, Fido kuma ta kasa komai and she's speechless baki bud'e take kallon sa, lokaci guda mutuwar mahaifin ta yayi bouncing brain nata batasan lokacin data d'aga hannunta ta wanke sa da mari mai rai da lafiya ji kake "Tassssss"
Ba k'aramin girgiza yayi ba, a rayuwar sa bai tab'a furta wa mace yana sonta ba sai Fido, a rayuwar sa ba macen data tab'a d'aga hannu ta maresa harta mahaifiyar sa. Fido ta nuna sa da yatsa tace
"Har kai ka isa kace kana so nah? How dare you open your filthy mouth kana ganin kwayar ido nah kace kana so nah? Wallahi koh da maza sun k'are a duniya bazan tab'a sonka ba, na tsane ka, I hate you more than anything"

Muryan sa yana shacking yace
"Mesa bazaki soni ba, mesa bazaki tab'a so nah ba, mena miki a rayuwa Fiddausi, if I ever wronged you unknowingly please ki fad'a mini wallahi zan baki hak'uri! Tell me why"

Murmushi tayi tace

"Do you really wanna know abunda ka mini"
Da sauri yace

"Eh"

So take ta fad'a mishi gaskian kawai sai ta tuna idan har ta kuskura ta fad'a masa bazata iya d'aukan fansa akansa ba. Tace

"Nothing kawai bana sonka, jina nah sam bai had'u dakai ba"

A dai-dai lokacin wayarta tayi ringing, nan take tayi receiving tace

"Ka shigo ina ciki ba kowa a gidan" ta katse wayan.
Kallon Issam tayi tace

"Yanxu zaka san mesa bana sonka"

Sallama akayi sai ga S.A yashigo parlour, Murmushi Fido tayi tace

"Bismillah have a seat" tareda nuna masa kujera.
S.A yace "Thanks my love"
Issam wani irin kishi yaji, Fido tace

"Ammm Issam kaga mijin da zan aura koh? Sunan shi Suleiman"

Issam murmushin k'arfin hali yayi yace

"Happy for you". Ya mik'a masa hannu suka gaisa, S.A sai wani shan k'amshi yake yana b'ata rai. Fido ta juya wajen Issam tace

"Can you excuse us please idan ba matsala"
Murmushi yayi yace

"Sure why not? Bye take care"

Yana fita S.A ya b'ata ransa yace
"Waye kuma wannan?"

Fido zama tayi tace
"Karka damu wai sona yake"
"What?"

Dariya tayi tace "Karka damu bana sonsa"
Idan har bakya sonsa toh ki fad'awa Abba zan turo
"Hajiya zata barka neh?"

"Tun yaushe ta hak'ura"
"Matar ka fa?"

Murmushi S.A yayi yace
"Tana gaishe ki ma"

Dariya Fido tayi tace
"Hmm Allah sa dagaske neh, Kasan mata da kishi"
"Kibar maganan nan, yaushe zan turo?"

Fido gyara zaman ta tayi tace
"A gaskia bazan maka k'arya ba bazanyi aure yanxu ba, mutune zasuce koh shekara da mutuwar aure nah baiyi ba zanyi wani aure"

"Fido baki sona, idan har kina so nah toh ki mantar da maganan mutaneh"

"Ka turo toh"

Kallon ta yake da mamaki yace
"Are you serious?"
Murmushi tayi tace

"Yeah"

Manage this🙈

By

Nana Fa'ad
*HAYATEEY*

Pure Moment Of Life Writers
[We don't just entertain and educate, we touch the ❤ hearts of the readers]

_In dedication to Fido Sodangi_

*Gaisuwa na musamman Shamcy Dahiru, Mum Ikram, Mum barista da My Shamcy❤ ina kaunar ku sosai sosai and muna mugun tare*

{August, 2017}

Follow me on Wattpad @Nana_Faad. Do read my write-ups and please don't forget to SHARE/VOTE!!!

```Page 34```

Murmushi S.A yayi yace
"Beauty nagode, yanzu sunyi tafiya nan da three weeks zasu dawo gari, suna zuwa gari washegari zasu zo nan In Shaa Allah"

"Allah kaimu S.A"
"Ameen beauty"

Issam yana zuwa gida ya tattara kayan sa ya saka su a mota ya d'au wayar shi yayi dailing number, ana picking yace
"Akwai jirgin da zai tashi yau?" Sai can kuma yace "Ohk gobe by 6:00am ba, aiit thank you" ya katse wayan.
Wani irin zugi yakeji acikin zuciyar sa, ya rasa abunda ke masa dad'i, maganganun data fad'a masa ne suke yawo cikin brain nasa _Har kai ka isa kace kana so nah? How dare you open your filthy mouth kana ganin kwayar ido nah kace kana so nah? Wallahi koh da maza sun k'are a duniya bazan tab'a sonka ba, na tsane ka, I hate you more than anything_
Wani zazzafan hawaye neh suke sauk'a a kan kuncin sa, he just can't believe wai shine yake kuka akan mace yace "Ashe haka mata sukeji idan nace musu bana sonsu? Ashe haka abun yake so painful? Ashe haka sukeji idan na fad'a musu bak'ar magana? Ashe haka so yake?"
Wani irin kuka yakeyi mai tsuma zuciyan duk wani mai sauraro, ya rasa dalilin da yasa yake sonta, idan kyau neh dubu son fita amma zuciyar shi ita kad'ai keso. Share hawayen sa yayi dajin k'irar sallar magrib ya tashi yayi alwala yaje masallaci.

Da daddare ma same thing ya kasa bacci idan banda tunanin Fido ba abunda yake, daga k'arshe yayi nafila ya rok'e Allah daya cire masa sonta a ransa.
Chapter 21 · 0% Book details