← Book details Hayateeey Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 40

Sashe 11

Hayateeey Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Fiddausi no matter what learn to respect your elders you shouldn't have talked to her that way"
Fido jikinta yayi sanyi tasan tayi kuskure koh ba komai akwai mutunci tsakanin ta da S.A tace
"In Shaa Allah Abba bazan k'ara ba"
"Maza toh tashi ki tafi" jiki a sanyaye ta fita.

Inna ta fashe da kuka, tace
"Alhaji baga irinta ba, ni tun farko ba son auren nan nake ba, nace ka d'aura auren da Aliyu amma kayi kunnen shigo wato ni ban isa da kai ba koh?
" Haba Inna kiyi hakuri dan Allah ki daina kukan nan"
"Sai ka mini alkawarin zaka had'a ta da Aliyu"
"Na miki alkawari"
Inna atake ta share hawayen ta tace
"Amma kasan duk mei karya alkawari alaman munafiki ni koh, tam"
"Kai Inna mei yakawo maganan munafiki kuma haba, na tambaye ki mana Inna"
"Ina jinka"
"Of all mazan gidan mesa kika nace sai Aliyu bayan shi yanada matar sa, ga Khaleal, ga Ahmad duk basu da aure"
"Toh ai Aliyun neh yace yana son ta"
"Kin tabbata?"
"Aww toh karya zan maka?"
"Ohk bari zan mishi waya yazo naji ta bakin sa"

**********************

Mahaifiyar Issam ce zaune tana kallon News a Al-jazeera. Issam yashigo yana murmushi yace
"Mum come with me please"
Murmushi Mum tayi tace
"Ina kuma Isssaaam?"
"Kedai kizo ki gani"
Tasowa Mum tayi tace
"D'an rikici, muje koh"

Wani d'aki yakai ta a cikin gidan wanda batasan dashi ba tunda take a gidan, bud'e kofa yayi yace
"Mum She's the one!"

Mum bud'e baki tayi tana kallon cikin d'akin, zuciyan ta yana mei bugawa, tunda tasan d'anta bai tab'a son mace ba. Drawing na pictures na Fido neh kaf cikin d'akin, a kowani zanen hoto ya rubuta *Hayaateey*, wasu ya rubata *She's My Hayat*

Zuwa yayi koh wani zanen hoton yana shafa fuskan yana murmushi yace
"Mother ban tab'a tsanmanin i'm good architect sanda nafara sonta. Mother can you see how beautiful she is?"
Mum take ta goge hawayen da yake sauko wa kan fuskan ta kar yagani, tayi murmushi tace
"She's Beautiful!"
"Yeah she is, I so much love her Mother. Cant wait auren Faruq na fad'a mata that I've falling for her, na fad'a mata ina Sonta, ina kaunar ta, itace ruhina, jinin jikinah, itace RAYUWATA. HAYATEEY FIDDAUSI"

******************************

Aliyu kwance yake akan gado zuciyan sa yana bugawa, a yanxu ya tabbatar wa kansa lalle dagaske yana son Fido more than tunanin sa, So na hak'ik'a, bud'e wayan sa yayi, folder daban nagani wanda pictures na Fido neh zalla a ciki, wasu tana tafiya, wasu tana bacci, wasu tana cin abinci, wasu tana chat a waya. Murmushi yayi yana shafa kan screen na wayan yace
"Fido words can't explain how much I love you, ina sonki ina matuk'ar sonki, zuciyata ta gama kamuwa da sonki, kece numfashi nah, kece jinin jikinah, kece Qalbee nah, kece RAYUWA TA!!!!!!"
K'aran wayan sa neh yasa yayi firgit, atake yayi picking call d'in dan ganin Abba
"Assalamu Alaykum" sai can yace
"Ohk Abba In Shaa Allah anjima zanzo bayan Isha'i" ya katse wayan zuciyan sa na mei bugawa.

Fido zaune a kan gado laptop a gaban ta tana kallon wani series Game Of Thrones, k'arar message taji ya shigo wayarta a take ta d'au wayan duk a tunanin ta S.A neh dan yata kiranta bata kusa bata samu tayi recieving call d'in ba, ganin wani message new number yasa ta bud'e, message kamar haka
_Believe me, you are the one, whom my heart finds, whom my heart reminds me of, whom my destiny wants, whom I love the most! Believe me, idan nace miki Kece farin ciki nah, jin dad'i nah. Believe You are my HAYAT!!!_

Sau uku take karanta message d'in dan har aranta taji dad'in sa. Murmushi tayi sai can kuma taja dogon tsaki tace Maybe ma k'ananan 'yan iskan nan neh.. Batayi deleting ba dan ba karamin dad'i ya mata ba, wani message neh ya k'ara shigowa take ta bud'e tafara karantawa
_Kar kiyi kuskuren blocking d'in number ta kamar yadda kikayi a lokacin da kike UK dan kece zaki sha wahala, bazanyi k'asa a gwiwa ba dan ganin na miki messages kullum koh da zakina blocking every Sim card da zan na tura miki message dashi and plus don't think of changing your number sabida a ranar da kika canza zan samu!!! Stay Safe Hayateeyy_

Tunani tafara shin wanna waye neh? Duk yadda akayi ya santa or yasan someone very close to her. Jin k'aran wani message yasa tayi sauri ta bud'e
_And please Dan Allah kar kizo mini a mafarki nah kinji koh Hayaateey ? And my thoughts please!!!!!_

Murmushi tayi tace Lalle baka da aiki tareda jan dogon tsaki. Shamcy ce tashigo cikin d'akin tace
"Adda Fido Abba yana kira"
"Shammcyy you can't you say Assalamu Alaykum first! Wannan wace irin halin neh"
"Adda Fido nayi bakiji ba"
"Banson karya dallah b'ace mini a gaba"
Hijabinta ta d'auko wanda yake har kasa ta saka ta d'au wayarta da yake kan gado. Direct side na Abba ta wuce tayi sallama tashiga. Zuciyan tane ya tsinke dan ganin Matan sa uku da tayi, mahaifiyar ta da kuma Aliyu wanda yake zaune a kasan carpet kamar wani mutumin kirki. Waje ta nema ta zauna ta gaishe su.

Abba yace
"Fiddausi abunda yasa muka kiraki shineh kinga dai abunda mahaifiyar S.A tazo tayi a gidan nan, kuma daga baya Mijin ta Alhaji Abubakar Babangida ya kirani wai zai bani any amount dan mubar maganan auren, shine nace yabar kud'in sa nima na fasa. So yanxu munyi deciding zamu d'aura muku aure da Aliyu dan tun daman can dashi za'ayi kikace S.A kike so. Kin amince?"
Ji tayi abun yazo mata banbarakwai, ita a da taso Aliyu kamar ranta, shuru tayi, Abba yace
"Me kikace Fiddausi, idan bakison sa bazamu miki auren dole ba"

Fiddausi a hankali ta furta
"Na amince Abba, zab'in ku shine nawa"
"Yawwa Madallah, In Shaa Allah nan da wata d'aya za d'aura auren, ki tashi ki tafi Allah miki albarka"

A sanyaye ta tashi tabar parlor, ta rasa meh take feeling, farin ciki koh bakin ciki? Fashewa da kuka tayi tace "Allah gani gareka!"

By

Nana Fa'ad
*HAYATEEY*

Pure Moment Of Life (p.m.l)

[We don't just entertain, we touch the ❤ heart of the readers]

Written By Nana Fa'ad

_In dedication to Fido Sodangi_

{July,2017 }

*Words can't explain how much I love you babes😘. My kanwa Meenarh Parrot and my dear Teemerhlurv❤. Heart yhu gurls plus i dedicated this page to yhu both*

```Page 21```

A hankali tashiga cikin motan ta zauna, d'aga kai tayi suka k'ara four eyes dashi ya kashe mata ido d'aya a take ta sauke kanta dan ya mata bala'in kwarjini. Farar shadda neh a jikin sa mei kyaun gaske yasha zuben hannu bak'i, hulan kansa ma bak'i wanda ya dace da kalar fatan sa fari. Ga sajen sa bak'i wanda ya kwanta luguf a kyakkyawan fuskan sa, ya had'u more than farkon data fara kallon sa saidai yanxu ya d'an rame. "Kyaun maciji" tayi mumbling tareda jan dogon tsaki wanda yasa duk suka juya suka kalleta. A take Issam yaja wawan biriki wanda ya tsoratar dasu
Eesha tace
"Lafiyan ku kuwa?"
Issam yace
"Ask her, kinsan I hate tsaki and I hate anybody da yakeyi"
Wani dogon tsaki ta k'ara ja tace
"We are running late Mallam dan Allah muje haba"
"Kayi hakuri Issam haba yau ina cikin farin ciki abokinah bai kamata ka mini haka ba, please don't ruin it" cewar Faruq

Issam ya tada motar yace
"I swearit if she dare hiss again zan zubar daku a mota nah idan yaso kwayi waya a zo a d'auke ku"
Faruq yayi dariya yace
"Naji abokinah hakuri zakayi"

Fido dai shuru tayi bata k'ara cewa komai ba gani take ta kuma yin wani maganan aji down neh.

A Katsina Motel Hotel suka sauka, Cameras neh sukayi caaaa akansu suna d'aukan su hoto lokacin da suke fitowa a mota. Bayan Issam da Fido sun sauka a motar suka bud'e wa amarya da ango kofa suma suka fito. Eesha da Faruq suka shiga gaba, Issam d Fido suna binsu a baya suma kamar couples.
Issam matsowa yayi daf kusa da kunnen ta ya mata magana wanda ni kaina bansan mei ya fad'a mata ba. Wani irin kallo ta watsa masa tareda jan tsaki, murmushi yayi tareda shafa sajen sa.
Hall d'in yasha decorations Mashaa Allah yayi kyau sosai, high table sukaje suka zauna. An bud'e taru da addu'a, aka kira best friend na ango wato Issam ya hau kan stage ya bada history ango. Zo kuga yadda all eyes on him, Ramla da Teema wanda sunyi attending dinner suna gefen Fido suka ce
"Mashaa Allah"
Teema tace
"Ramlah kina ganin guy, wayyooo Allah nah yayi karshe"
Ramla tace
"Da a hanya na gansa sai na rantse da Allah ba mutum baneh, Kut! Hmm nama rasa mei zance"
Fido dai shuru tayi tana jinsu, Bayan ya gama aka kira Fido itama tazo ta bada history amarya.

A hankali take cat walking wanda a yanxu ya riga ya zame mata jiki, mazan nan duk ido a kanta dan ta had'u iya had'uwa. Tafiyan ta ma kad'ai abun kallo neh bare azo ga kayan jikin ta da kuma kyawunta. Tana cikin tafiyan ta mistakenly ta taka dogon rigan ta wanda yake jan kasa sai gata zata fad'i kasa. Rufe idon ta tayi gam jira kawai take ta fad'i tashiga kunya. Ji tayi an taro ta, a hankali ta bud'e idon ta tayi ido hud'u da Issam wanda ya zuba ido yana kallon ta. "Astagfirullah" ya furta a hankali tareda tsayar da ita dam. Zo kuga Hall kowa na kallon su kamar sun samu T.V. A hankali Issam yace
"Try to watch your steps next time gurl and plus if you can't walk with a shoe like this karki k'ara sakawa. Village gurl"
A ranta taji zagin amma ba yadda ta iya and yayi saving nata da yau taji kunya. A sanyaye taje kan stage d'in ta bada history amarya cikin harcin turanci sai ka rantse bata iya hausa ba...
Chapter 11 · 0% Book details