← Book details Dr Khaleel Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 95

Sashe 92

Dr Khaleel Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

117.....
A tsorace Ashfah ta farka tana kkrin mikewa ya koma baya da sauri yace "No nace ki kwanta ne" mikewa tsaye tayi ta koma jikin gado kanta a kasa, ya juya da sauri ya nufi kofar xae fita, da sauri tace "yaran fa" ganin bata gansu kan gadon ba, ba tare da ya kalleta ba yace "suna daki na" yana kai wa nn ya kulle mata kofarta. Washegari Ashfah ta gama shirin ta da safe ta gyara dakin ta snn ta sauka downstairs don hada break fst, ko da ta gama har tara yyi, ta haura sama don komawa dakinta taji kukan su sultan, kasa shiga dakinta tayi ta tsaya bakin kofa, don da taji kukansu hnklinta ke tashi ta rasa sukuni barin ynxu da tasan ba su ci abinci ba tun wayewar gari, can dae ta gaji da tsayuwa ta shiga dakinta, ta fi minti biyar da shiga amma har lkcn sae karuwa kukansu yake, ta kasa daurewa ta mike kmr xata yi kuka ta fita da sauri ta nufi dakin, tana shiga dai dai lkcn da Khaleel ke fitowa daga wanka knn daure towel a waist, da sauri ta juya masa baya a mugun tsorace sae kuma ta nufi kofa ta fice daga dakin da sauri har tana tuntube, Khaleel ya dauki yaran yana lallashinsu har suka yi shiru snn ya xaunar da su tunda sun fara iyawa ynxu cikin kekunansu da fanz suka kawo masu as gift ranan da aka rada masu suna bayan rasuwar uwarsu duk da ba ayi wani taron suna ba, cikin minti sha biyar ya gama shirin sa ya kwashi yaran ya kai mata ba tare da ya kalleta ba yace "anjima xa mu fita, ki hada masu kayansu," yana kai wa nn ya juya ya fita, Karfe sha daya suka bar gidan gaba daya da kayan sawansu da ta harhada masu da madaransu da feeder, bayan mota ta xauna da yaran a jikinta, ga mmkinta gidansu ta ga Khaleel ya nufa, yana gama parkin suka shiga a tare, sae murna take xata ga Abbanta da momy, momy tayi farincikin ganinta hka ma Abba, inna ma na gidan ranan, inna ta rungume jikartata tana mata sannu da xuwa da daya daga yan biyun hannunta, sae da Ashnaah ta rasu da sati biyu aka sanar da inna da ke can katsina lkcn, ba sae na fadi tashin hnklin da ta shiga ba don dagewa tayi kan Abba ne ya kasheta ba kowa ba wllh, da kyar dae aka samo kanta don sae da ita ma tayi yan kwanaki a gadon asibiti don ba karamin girgixa ta mutuwar tayi ba, Khaleel da ya biyo bayan Ashfah rike da Sudais a hannu ya duka har kasa ya gaida innar da ba wani sake masa take ba don a xaton ta shine sanadin faruwan komae, sae da duk suka bar falon ya rage shi da Abba snn yace "dama Abba sultan na kawo maka, na baka shi kmr ynda ka bukaci inyi hkn idan Allah ya yrda," Abba yyi murmushi yace "Ma'sha Allah, Allah yyi maka albarka Khaleel na gode kwarae da gske" Khaleel ya dukar da kansa yace "Ameen Abba, Sudais kuma xan kai sa can gidanmu gun Ummina" Abba yace ",Allah sarki, Allah dae ya raya su ya albarkaci rayuwarsu" Khaleel yace "Ameen Abba" Ashfah duk a tunaninta karatu xata koma shiyasa aka maido yaran gidansu amma har suka fara shirin tafiya bata ji Abbanta yyi mata mgnr karatu ba, hkn yasa hnklinta ya tashi, Karfe biyu suka bar gidan, Khaleel ya kai Sudais can gidansu kmr ynda yace, dad dinsa ya kira sa har bedroom dinsa yace "alfarma daya nake son ka min ynxu son" Khaleel ya daga kai yana kallonsa, Abba ya nisa yace "ko sati ba ayi ba da xuwan Alhaji Mukhtar wajena, so nake kayi hkuri ka mance duk abinda ya faru ka koma bakin aikin ka, shi ya nemi wnn alfarman daga gareni kan cewa in maka mgna xaka fi ji" Khaleel yyi shiru bae ce komae ba, ko kadan badan mahaifin sa ne yyi masa mgna ba bbu abinda xae maida sa asibitin nn, but he vowed never to disobey his father till his lst day on earth, a sanyaye yace "to xan koma In'sha Allah dad, nagode" Dad yyi murmushi yace "toh Allah yi maka albarka, ya raya maka yaran ka ya albarkaci rayuwarsu, ya baku xan lfya da hkuri da matar ka" Khaleel yyi murmushi a sanyaye yace "Ameen Dad" snn ya mike yyi ma Dad dinsa sallama yace xa su tafi, dakin Ummi ya tarda Ashfah yace ta taso su tafi, Ashfah ta mike da kyar tana kkrin mayar da hawayen idonta ganin Sudais ma nn xa su bar shi, ita kuma abu kadan ke sa ta kuka ba kmr Ashnaah ba, sallama tayi ma Ummi, Ummi ta rakosu har downstairs Ashfah tayi ma dad ma sallama suka fita Khaleel na biye da ita a baya, rasa inda xata xauna a motar tayi, ta bude bayan motar a hnkli ta shiga, shi dae bae ce mata komae ba ya shiga driver seat ya tada motar suka bar gidan, Karfe goma saura suka isa gida, Ashfah ta nufi dakinta da sauri ta dinga rusa kukan rabata da su sultan da aka yi, shknn ita kadae xa tayi ta xama kmr mayya a gidan bbu me debe mata kewaye, gajiya tayi da kukan ta mike xaune a sanyaye ta cire kayan jikinta ta daura xani ta shiga wanka, ko da ta fito gown din baccinta kawae ta xura ta kwanta ta ci gaba da kukanta, sha biyu saura Khaleel ya tura kofar dakin a hnkli tare da yin sallama ya shigo, Ashfah ta mike xaune da sauri tana share hawayen fuskarta lkci daya ta shiga dudduba inda hijab dinta yake amma ta kasa mikewa ta dauko don kayan baccin jikinta karami ne, bata taba tunanin shigowarsa dakin a lkcn ba, Khaleel ya karaso kusa da ita ya xauna gefen gado yana kallonta, sunkuyar da kai tayi da sauri gabanta na faduwa, ya dago kanta a hnkli yace "kukan me kike khadija" da ganinta kasan a tsorace take, ta saukar da idonta muryarta na rawa tace "su sultan...." Sae kuma ta fashe da kuka, Khaleel ya lumshe ido ya rungumeta murya can kasa yace "kiyi hkuri xa su dinga xuwa maki hutu" Ashfah da ta gama tsorata don tun da take bata taba jin ta a kirjin Namiji ba ta shiga kkrin kwace kanta, ya saketa da sauri ya mike kmr wnda ya tuno abu juyawa yyi ya fice daga dakin yana kkrin mayar da hawayen idonsa.
Washegari da safe Ashfah na gama hada break fst ta dawo dakin ta kwanta, Karfe goma saura ta ji fitar motar Khaleel, sae da ya fita da kusan awa daya snn ta sauka downstairs, dinnin ta nufa don sae yyi break ita ma take yi, taga yyi ba laifi, ta ja kujera ta xauna ta shiga hada tean ta, Khaleel kam clinic ya nufa don amsa kiran da dad din Ameesha yyi da safe ba don ransa ya so ba sae dan darajar mahaifin sa. Da kyar ya iya shiga asibitin jikinsa a sanyaye tunowa da yyi a cikin nn wife dinsa ta rasu, tunanin hkn yasa kwalla taruwa cikin idonsa ya nufi office din boss din nasa bayan sun gaisa da nurses da ke reception, Da farko hkuri dad din Ameesha ya soma basa kan abubuwan da suka faru a baya snn ya bukaci da ya koma bakin aiki a ranan, Khaleel yace "Dad sae dae ko gobe, bn sanar da iyalina xan tafi gun aiki ba," dad din Ameesha yace "toh bbu matsala, Allah ya kai mu goben" Khaleel ya mike yyi masa sallama ya fita, a haraban asibitin suka hadu da Ameesha, ta gaishesa da fara'arta ya amsa yana murmushi snn tace ya gaida mata Yara ta nufi cikin asibitin.
Chapter 92 · 0% Book details