← Book details Dr Khaleel Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 95

Sashe 38

Dr Khaleel Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

56.....
Karfe shidda na yamma Khaleel ya tura kofar dakin Ashnaah, tana xaune bbu abinda take sae tunane tunane, fuskarsa a daure yace "in kin ga dama ki sakko kasa ki sameni" binsa da kallon tsana tayi har ya bar bakin kofar snn ta ja tsaki hade da tabe baki, mikewa tayi gudun kar ya dawo ta dauki hijab dinta tasa snn ta fesa turare ta sa takalminta ta sauka kasa, yana cikin mota yana jiranta, tana shiga ya ja motar suka bar gidan. Gidansu yyi parking ya fito ya nufi cikin gidan, ita ma ta fito tana biye da shi a baya, suna gama gaisawa da ummi Khaleel ya fita ya bar dakin, sae a snn ummi ta juya tana kallon Ashnaah tace "ya kawo maki kaya fateema" Ashnaah ta dan yi shiru snn tace "A'a" ummi ta tsaya kallonta, ta sunkuyar da kanta, ummi da tuni bacin rae ya bayyana fuskarta tace "kudi fa" girgixa mata kai Ashnaah tayi ba tare da ta dago ba alamar aa, ummi ta mike ta fice daga dakin, sae bayan kusan minti sha biyar ummi ta dawo, Khaleel ya shigo dakin yana kallon Ashnaah da mmki yace "ki ka ce ban kawo maki kaya ba ke" Ashnaah ta galla masa harara tace "ehh ni bn ga kaya ba" kallonta ya tsaya yi ya ma rasa me xae ce, ummi ta daka masa tsawa tace "dalla fice min a daki malam" juyawa yyi ya fice daga dakin, Ashnaah ta juya tana kallon ummi murya can kasa tace "momy don Allah ki taya ni yi masa mgna ya bar ni in ci gaba da karatuna, ni nayi masa ya ki yrda, kuma ya ki bari na in je gida har ynxu. Karfe goma saura suka bar gidan, gaban Ashnaah sae faduwa yake ganin ynda ya hade rae har suka isa gida bae ce komae ba ya nufi cikin gida ba tare da ya tsaya kulle motarsa ba, a sanyaye gabanta na ci gaba da faduwa ta bi sa, har ya shige falonsa kanta shigo falon, ta bude dakinta a hnkli ta shiga ko xama bata yi ba taji ya bude kofarsa ya fito, tayi still xuciyarta na bugawa, dakinta ya bude ya shigo ya nufi inda take fuskarsa daure ya fixgota yana huci yace "ki gaya min dalilin da yasa kike hada ni da ummi na" kuka ta saki tana kallonsa tace "to ni wani kaya ka bani don Allah" turata yyi da karfi yace "kuma da kike cewa xa ki koma makaranta uban wa xae dinga biya maki kudin makarantar, kin ban ajiya ne, in kin tafi gidan naku sae ki gaya ma mahaifin ki ke makaranta xa ki koma don baxan daura ma kaina wnn nauyin ba" juyawa yyi ya fice daga dakin, Ashnaah ta bi sa da kallo tana mmkin dukanta da bae yi ba, ssae jikinta yyi sanyi tuna furucinsa na karshe, to ynxu abbanta zae yadda ya ci gaba da biya mata kudin makaranta? A sanyaye ta nufi gadonta ta kwanta tana tunanin to ko dae usman xata yi ma mgna. Yau Sunday tana kwance daki taji an danna kararrawa, ta mike ta dauki hijab dinta ta sa snn ta sauka downstairs ta bude kofar, gaisheta mutumin yyi yace "oga ne yace xa a fita da ke anguwa yau" da mmki tace "ni? Ina yace xa ni?" Mutumin yace "cikin gari yace xa a kai ki" cike da murna tace to ka je ka dawo bari in shirya, da sauri ta koma sama, har wani bari jikinta yake ta shiga fiddo kayan da xa ta sa, ta fito da wani atamfanta England me kyau ta ajiye snn ta shiga gyara fuskarta don dama tayi wanka, ssae tayi kyau ba kadan ba, a karo na farko ta bude akwatunan lefenta ko xata ga jaka da takalmin da xae shiga da kayan don tana da mayafi, ta ko samu har ma da mayafi duk light yellow, ba karamin haduwa Ashnaah tayi ba, jan baki ya kwanta das das lebbenta me kyau, ita kanta tasan tayi ne, turarrukan da ke gaban madubinta ta feffeshe snn ta kuma kallon kanta a madubi ta fice daga dakin ta sauka kasa cike da jin ddin xata gidansu daga nn ma sae su hadu da usman dinta, xaune ta samu Khaleel a falon yana waya kallo daya yyi mata xae dauke kae ya kasa da sauri ya kuma juyawa yana kallonta, ko kallonsa bata yi ba har ta wuce sa xata fita ya daka mata wani mugun tsawa yace "ina kike tunanin xa ki da mayafi? Da aure na a kan ki xa ki shiga gari da wnn dan iskan mayafin" juyawa tayi tana hararansa tace "to me xan sa? Kana nufin in yaba hijab kan kwalliyar nn, tabdi lallai ma" mikewa yyi a fusace ya yo kanta ta jefar da heels din kafanta ta sa ihu ta nufi sama da gudu, bin ta yyi har cikin dakints ya fixge mayafin, hadiye kukan da ke cinta kawae take don kar ta bata fuskarta, da kansa ya ciro Mata hijab har kasa ya jefa mata snn ya fice daga dakin, bbu ynda ta iya hka ta sa hijab din kmr xata fashe da kuka ta fito, har waje Khaleel ya bi ta yana kallon drivern da ke jiran ta jikin mota yace "ba ni makullin motar Ahmad, xaka iya tafiyarka xan kai ta" Ashnaah ta juya da sauri tana kallonsa, ji tayi kmr ta fasa ihu, shi ko ya xagaya ya shiga maxaunin driver, dae dae lkcn da masu gadi suka bude gate sae ga babban mota dauke da lafiyayyun kayan daki na gani na fada, har su biyu suka shigo gidan, Bin motar da kallo Ashnaah tayi, Khaleel ya sauke glass din motar ya daka mata tsawa "wae kina hauka ne xaki bar ni xaune cikin mota"
Chapter 38 · 0% Book details