← Book details Dr Khaleel Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 95

Sashe 6

Dr Khaleel Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

~Dr Khaleel~ 12 By Khaleesat Haiydar
Khaleel yyi murmushi hangota da yyi tana Tahowa daga layin da ke ranan lahadi ne layin shiru bbu mutane, mayafi ne yafe jikinta yau, ya kafa mata ido har ta karaso titi ta tsaya daga gefen motarsa ta tsayar da abun hawa ta hau, tada motarsa yyi ya hau kan titin ya bi bayan napep din da ta hau. Bae wani sha wahalan bin napep din ba don bbu motoci ssae kan titin, Tafiyar minti kusan goma suka yi keken ya sha kwanan wani layi shima ya bi bayansa, dai dai gate din wani duplex mai napep din ya paka, Khaleel yyi parkin dan nesa da gidan, Ashnaah ta fito ta mika masa kudinsa ta shige gida abunta. Khaleel ya fito yana kallon mai gadin dake xaune bakin gate ya karasa ya gaishesa snn yace "wnn yarinyar da ta shiga nan ne gidansu" mai gadin yace "eh nan ne" Khaleel yace "ok, mai gidan na ciki ne?" Mai gadin yyi shiru snn yace "da matsala ne" Khaleel ya girgixa kansa yace "ko daya, kawae na xata sa ni a kwana tayi da tace nn ne gidansu, ynxu dae ka min sallama da mai gidan in yana ciki" Mai gadin ya mike ya shiga ciki, Khaleel ya xauna yana murmushi, ba a dau lkci ba mai gadin ya dawo ya masa iso har balcony ya nuna masa kujera ya xauna snn ya koma bakin aikinsa, bude kofar falon aka yi wani mutumi da baxae wuce shekaru hamsin ba ya fito yana kallon Khaleel ya basa hannu Khaleel ya ki amsa ya sunkuyar da kansa snn ya gaishesa da ladabi, Mahaifin Ashnaah ya xauna snn ya shiga tambayarsa daga ina, Khaleel yyi shiru yana kkrin tuna sunan da ya gani jikin receipt din Ashnaah snn da sauri ya maxa yace "dama tare da Fateemah muke shine tace in shigo in gaida ka," shiru Abban Ashnaah yyi, sae kuma ya dan yi murmushi yace "to nagode" Khaleel yace "to ni xan koma Abba" Abba ya kuma masa godiya snn ya mike ya bar balconyn Abba ya wuce ciki. Dakin mum din Ashnaah ya nufa ran sa a bace, Ashnaah na kwance tana danna waya, mum dinta kuma na kallon wani program ita da Ashraf, ya tura kofan duk suka juya da sauri, Abba na nuna Ashnaah yace "lallai kin rika Fateema, har ni xa ki turo ma wani ya xo ya gaida ni ko, wato ni kika raina, to daga yau na yanke xuwan ki makaranta a gidan nn, in fact ko nn da gate bana son ki sake fita, wayar Hannun ki kuma Ki kai min shi Daki ynxun nn" yana kai wa nn ya fice daga Dakin, kuka Ashnaah ta fashe da tana kallon mum dinta dake kallonta da mmki, "Ashnaah wa kika tura ma Abbanki" cikin kuka ssae tace "wllh ban sani ba mum," Mum dinta tace "to daga ina kike ynxu" tace "daga gidan inna wllh nake mum, ni ban turo kowa ba" ta karashe maganar tana kuka ssae, mikewa Mum tayi ta fice daga Dakin, sae kuka Ashnaah take, usman ta kira bugu biyu ya daga a fusace ta fara magana "kai ne ka xo gidanmu yau?" Ya dan yi shiru snn yace "ni kuma?, kin manta ina Abuja?" Kashe wayar tayi ta kuma saka kuka don cikin samarinta Usman kadae ne yasan gidansu, kashe wayar tayi gaba daya don ma kar ya kuma kiranta, mum ta dawo ranta a bace tace "ki bar dauko min mgna Ashnaah, mahaifin ki gani yake kmr ni ke xuga ki ni fa ba ruwana ynxu gashi ni ma kin ja min, in kuma auren kike so to ae shkkn." Kuka kawae Ashnaah take duk jikinta yyi sanyi, to waye wnn yyi mata hka, gashi Abba ya dakatar da ita daga xuwa makaranta. Har Khaleel ya isa gida murmushin dake dauke a fuskarsa tun bayan fitansa gidansu Ashnaah Bae bace ba, falonsu ya shiga ya tarda Abbansa xaune a falo da wani abokinsa, ya karasa cikin falon ya gaishesu, Abokin Abban nasa yace "har yau dae ka ki aure ko Khaleel ga Ma'aruf ynxu 'ya yansa har uku, Khaleel yyi murmushi yana shafa kansa yace " ni ma na kusa Abba, in Allah ya yrda watan da xa mu shiga" Abbansa ya sace kallonsa , Khaleel yyi dariya yace "Allah kuwa Abba na samu mata ynxu" Abban nasa yace "to Allah yasa" mikewa yyi ya masu sallama xae haura sama announcement din da ya ji ana yi a Tv yasa ya juya da sauri yana kallon tvn, murmushi yyi ganin hoton Zeenah boldly kan screen din Tvn snn ya haura sama. Satin Ashnaah biyu a gida bata je makaranta ba duk ta fice hayyacinta ta xama abun tausayi ga shi Abba ya amshe mata waya, duk irin lallaba Abba da mum dinta ta dinga yi tana basa hkuri hkn vae sanya ya canxa hkuncin da ya yanke ma Ashnaah ba don Bae yrda bata san daga inda mutumin yake ba, wani amininsa mum ta kira tayi ma bayanin komai don har inna ma yaki saurarenta, ranan da safe aminin nasa ya xo, bayan sun gaisa aminin yasa a kira masa Ashnaah, ta shigo falon da hijab dinta har kasa ta durkusa ta gaida abokin Baban nata, shi dae Abbanta Bae ko kalleta ba, Alhaji Salisu yace "Ashnaah me yasa Baki jin maganan iyayen ki ne?" Kasa cewa komai tayi kanta a Kasa, fada ya shiga yi mata daga karshe yace bbu ruwanta da ko wani saurayi daga ynxu har sae ta gama karatu, tace "to Abba ngdd" Abbanta yace " Allah yasa ya shiga kunnenta, so nawa Mike yin hkn da ita, Alhaju Salisu yace wnn kuma tsakanina da ita na Alhaji, tashi ji tafi gobe ki shirya ki tafi makaranta, Ashnaah taji ddi ssae, kuma tayi vow a xuciyarta daga ynxu bata sake kula saurayi, har usman ma ta bar kulasa don bbu abinda take so kmr karatu a rayuwarta. Karfe biyar na yamma Khaleel ya shigo falonsu Meenah, mai aiki kadae ce a falon tana shara, ya xauna bayan ya amsa gaisuwarta yace "masu gidan basa nn ne" tace "Anty Amina da bakuwa ce kadae a gidan, Momy ta fita, sama ya nufa ya bude kofar Dakin Meenah, Zeenah ce xaune gaban madubi tana comb din gashinta da ya kusa bayanta, ta juya da sauri sae kuma ta mike ganin Khaleel ne ta dauki hijab dinta ta rufe kanta tace "ina yini ya Khaleel" yyi murmushi ya amsa yana kallon ta, Meenah ce ta fito daga bayi tace "haba meye hka Ya Khaleel xaka shigo ma mutane Daki ba sallama in mutum bbu kaya jikinsa fa" Khaleel yyi shiru yana kallonta, hararansa tayi ta koma bayi da sauri ta sa key don tasan me xae biyo baya, yyi murmushi a xuciyarsa yace"Allah ya taimake ki yarinya" waya ya Ciro a aljihunsa ya mika ma Zeenah yace "gashi xa mu dinga magana, hope ba matsala dae" ta gyada masa kai ta karbi wayan snn yyi mata sallama ya wuce. Ashnaah ta karasa gun da motar usman yake da sauri a dan tsorace tace don Allah ka dinga rufa min asiri ya usman,ba na maka bayanin komae ba wae, ynxu idan wani ya ganmu ya je ya gaya ma Abbana fa" da dan damuwa usman yace "to ya kike son in yi Ashnaah yau fa sati uku Rabon da in ganki ga shi ke ba waya ba, to a ina xan ganki in ba nn ba" Ashnaah na kalle kalle kmr munafuka tace ka ga mu hadu a eatryn da ka taba kai ni ranan" yace to da yaushe?" Tace "karfe hudu xan bar makaranta sae mu hadu a can kawae, ki ban xo ba ka jirani" yace to ynxu me kike da baxa mu tafi ba, tace tutorial Muke, tana kai wa nn tayi gaba da sauri, shi ko yyi reverse ya bar wajen.
Chapter 6 · 0% Book details