Sashe 11
Dr Khaleel Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar20....Cikin hanxari ta gama wanke bakinta ta kuskure da mouth freshner ta tube kayanta ta shiga gun wanka, sabon towel fari ta samu ta dauka ta goge jikinta snn tadaura ta fito ta shiga bubbude wardrobe din dakin don neman inda kayanta suke, undies ta fara ciro wa snn fito da wani lafiyayyen Holland dinta an mata Riga da skirt ta ajiye kan gado ta nufi gaban madubinta ta xauna tana duba man da xata shafa, ta gama shafe shafenta snn ta shiga yi m fuskarta make up lafiyayye, wani hadadden kyau tayi dama ga ta kyakkyawan karshe, ta Mike ta dauki kayanta ta saka, tana cikin daura dankwali gaban madubi aka bude kofar Dakin, duk da ba karamin tsorata tayi ba hkn Bae sa ta daga kai ta kalli wanda ya shigo ba ta wani dake tana kkrin daura dankwalinta, sallamar mace da taji yasa ta juya tana kallon warce xata shigo mata, Rukayya ce kanwarsa ta shigo rike da basket din abincin breakfst, da gani ba sae an gaya mata ba tasan kanwarsa ce don ga kama ta gani, ta wani tsuke baki ta hade rae tanaci gaba da daurin dankwalinta, rukayya ta karaso dakin da dan fara'arta tace "ina kwana Anty amarya?" Ba tare da Ashnaah ta kalleta ba can ciki tace "Qalau" Rukayya ta dan yi jigum inda take tsaye, Ashnaah ko sae faman daurinta take, Rukayya tace"Break fst na kawo" Ashnaah tace "to ae basae kin shigo da shi nn ba mana, ba sae ki barsa can falo ba" Rukayya bata ce komaeba ta juya ta fita jikinta a sanyaye, Ashnaah ta ja dogon tsaki ta shiga fesa turare abunta, Rukayya ta kusan cin karo da yayanta xae haura sama yace "ina xa ki"tace "ca tayi wae in saukar da shi kasa" Khaleel ya bata hanya ta sauka, snn ya haura sama ya nufi Dakin Ashnaah ya buga shi da karfi, har lkcn tana xaune gaban madubi ta gama sa jewelries dinta tana kare ma kwalliyarta kallo, kallo daya tayi masa ta dauke kanta duk da irin faduwar da gabanta yake, ya daka mata wani tsawa yace "a gidanku hka aka koya maki idan kin tashi da safe kar ki fito kiyi aikace aikacen gida" ta juya tana masa wani matsiyacin kallo tace "ae ba yar aiki aka kawo maka ba, sae ka jira ran da....." Wani ihu ta fasa ta mike da sauri ta nufi bayi ganin ya yo kanta, yyi saurin fincikota ya juyo da ita yana kallon fuskarta, ta hadehannayenta biyu jikinta na rawa tace "don Allah kayi hkuri ba da kai nake ba pls" mariya wanka mata ta fasa kuka ya buga bakinta snn ya shiga janta suka fita daga dakin har suka sauko downstairs snn ya jefar da ita tsakiyar makeken falon da ya shigo da ita yace "ki tabbatar every blessed day kin share ko ina na falon nn kin goge snn kin fita waje ma kin share duk compound din nn and dat shud b done every morning as early as possible, motata ma daga dis very moment ke xaki dinga wanke shi duk safiya, snn ki hada breakfast ki kai ma duk masu aikin gidan nn da masu gadi, kowa ki bi sa inda yake ki ajiye masa hka ma lunch da dinner, lastly daga yau ko mai bana son in kara ganin kin shafa a gidan nn bare hoda ko jan baki don ba gidan iyayenki bane nn, ko wa kike tunanin kike ma kwalliya da wnn kodaddiyar fuskar taki" Ashnaah ta mike tsaye tana masa wani matsiyacin kallo tace "Sannu ubana, to wllh bari ka ji, kayi kadan ka kawo ni gidan ka in maka bauta, ashe gidan ka xae rube ba gyara, motar ka kuma xae dafe ba wanki, masu gadin ka dama'aikatan ka kuma xa su mace da yunwa,kwalliya kuma ba sbda wani bnxa nake yi ba don bae isa nayi masa kwalliya ba, shi a su wa" kallonta kawae Khaleel yake da mugun mamaki, da ganin ynda take maganar kasan a tsorace take, ya juya da sauri ya nufi sama Ashnaah ta xaro ido ta bi sa da gudu xuciyarta na mugun bugu.