← Book details Dr Khaleel Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 95

Sashe 13

Dr Khaleel Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

sauri dae dae gabanta ya ja burki yana mata mugun kallo yace "Ki dinga kiyayata fa" dauke kai tayi yyi kwafa ya ci gaba da tafiyarsa ta shiga binsa tana masa mugun kallo har suka shigo falonsu, sama ya nufa ita kuma tayi xaman ta kan kujera fuskarta a daure, ko ba a gaya mata ba ta ga alamar kmr gidansu ya kawota, ba a dau lkci ba ya sakko tare da mum dinsa da wasu yan uwanta suka shigo falon, kallo daya Ashnaah tayi masu ta dauke kai, suka xaxxauna suna mata sannu da xuwa taki ko da kallon inda suke, momy ce tayi karfin hali tace "ina yini amarya" Ashnaah ta dan kalleta ta maxa ta dauke kai snn tana wasa da xoben hannunta tace "lfya lau" Khaleel ji yyi kmr an Sara masa guduma a ka, ya kasa daina kallon Ashnaah ga wani kunya da ya ji kmr ya nutse, yan uwan momy suka mike kowa ya nufi sama, momy kam bata fasa cewa ya bakunta ba, ba kunya ba tsoron Allah Ashnaah tace "da gdya" momy ta mike tace "bari a kawo maki ruwan sanyi" Ashnaah tace "to" kuma ko ba a gaya mata va tasan mahaifiyar Khaleel ce don ga kama, kitchen momy ta nufa, Khaleel ya taso da sauri ya isa gabanta yace "ita mum din tawa kika ki gaidawa sbda ba a maki tarbiya gidan Ku ba" Ashnaah tayi tsaki tace "a hka ka gan ni ka aura ae, bnyi niyyar gaidatan ba sae me" ta ja dogon tsaki tana hararansa ta maida hankalinta kan kallon da take, ransa yyi mugun bace ya mike da kyar ya dunkule hannayensa ya haura sama Ashnaah ta bi sa da harara ta tabe baki, momy ta dawo falo rike da farantin Ashnaah ta mike ta dan Risina ta karba tace "dama kin bar shi momy daga gida Muke ae" momy tace "shine kuma baxa a sha ruwa ba don daga gida ake" sae da momy ta xauna snn Ashnaah ta sauko har kasa ta gaisheta, momy tace "lfya lau Fateemah ya kewan gida" Ashnaah ta dan yi murmushi bata ce komae ba, momy ta kira Rukayya ta sakko snn suka wuce sama da Ashnaah, tsaf momy ta kare Ashnaah gaban yan uwanta dake ta mitan ba yar gidan mutunci Khaleel ya auro va, bbu ynda suka iya da Yayar tasu duk suka ja bakin su suka yi shiru, karfe biyar da kusan rabi duk bakin dake gidan tun biki suka watse kowa ya kama gabansa, Khaleel ya kai kanwar mum dinsa da suke daki daya gida, ssae yaji kunyar fadan da take masa wae ya je ya auro yarinyar da va yar gidan mutunci va don bata da kunya surkarta ce xata gaisheta kuma ta amsa, in ma su baxata mutuntasu ba ae ya kamata ta mutunta uwar mijinta, har muka bar gidan ko sallama bata fito tayi mana ba sbda rashin kunya, ta girgixa kai tace "me ya kai ka Khaleel, a ina ka samo ta, kai ynxu kaji ddin abinda tayi ma uwarka, yarinyar da bata wuce xama jikarta ba idan da kae mace ne" Khaleel ya kasa cewa komae xuciyarsa sae tafarfasa yake yana tunanin me xae ma Ashnaah ya ji sanyi, irin fadar da mum din Meenah tayi masa knn jiya da daddare wae yaje ya auro ya Mara mutunci wato fitsara xata dinga yi ma danginsa ko, Khaleel yyi murmushi xuciyarsa na raya masa irin abinda xae ma Ashnaah, har ta gama bambaminta Khaleel Bae ce komae ba, bayan driving din kusan minti talatin ya isa gidanta ya ajiye ta ya bata hkuri ssae snn ya kama hanyar gida xuciyarsa na tafarfasa. 45 mins · Khaleesat Haiydar...
Chapter 13 · 0% Book details