← Book details Dr Khaleel Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 95

Sashe 42

Dr Khaleel Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
61....
Ashnaah ta gama feshe jikinta da turare snn ta
saka hijab dinta ta dauki yar Jakarta ta rataye a
kafada snn ta dauki dubu biyu cikin kudin da
momynta ta bata ta fito, dakin Ameesha ta nufa
ta sameta xaune gaban madubinta, Ashnaah tace
"na tafi sch" da sauri Ameesha ta juya tana
kallonta tace "da gske, ya bar ki ne" Ashnaah ta
tabe baki tace "kar ma ya bar ni mana, kinsan ne
xa ki girka mana yau" Ameesha tace "aa"
Ashnaah tace "jollof rice" Ameesha tace "OK
Allah ya kiyaye hanya amma ki fara gaya masa
kan ki fita kar kiyi laifi" Ashnaah tayi dariya tace
"ae ni bana laifi" juyawa tayi ta fice ta sauko
kasa, xaune ta same shi falo, ba tare da ta
kallesa ba ta nufi kofa, mikewa yyi da mmki yace
"ina xa ki?" Ashnaah ta hade rae tana kallonsa
tace "ba kace yau Monday Zan yi resuming ba"
tsayawa kallonta yyi ya ma rasa me xae ce mata,
can ya daka mata tsawa yace "to baxa ki ba, yar
rainin wayo" kmr jira take ta fashe masa da kuka
tace "amma kae fa kace min yau" yace "don
nace maki yau shine xa ki xo ki wuce ni ba tare
da kin ce xaki fita ba" ta dan marairaice gudun
kar ya hanata tace "to nayi xaton bacci kke ae"
tsayawa kallonta yyi ta sunkuyar da kai da sauri,
ya kauda kansa yyi murmushi, can ya kuma
kallonta yace "to a hka kike tunanin xa ki fita
fuskarki a waje? Ina nikaf din ki" juyawa tayi ba
musu ta koma ta sako nikaf snn ta sauko, daukar
makullin motarsa da ke kan center table yyi
fuskarsa daure yace "mu je" kmr xata fasa ihu
take kallonsa don bata so ya kai ta ba, amma
bata ce komae ba gudun kar yace bbu inda xata
kuma, ta bi bayansa, har cikin makaranta Khaleel
ya ajiyeta yana kallonta da kyau yace "na hane ki
da yi ma ko wani namiji mgna, Karfe nawa xa ku
gama lecture" tace "shidda" bata jira cewarsa ba
ta bude mota ta fice. Ba karamin farin ciki su
ummi suka yi ba ganin Ashnaah, ita kanta ta ji
ddin ganinsu togeda once again, Karfe uku da
rabi suka gama lecture dinsu na ranan, duk ta
karbi handouts tayi foto copy don saura sati biyu
exams dinsu, suna xaune karkashin wata bishiya
gaba daya da kawayenta wajen shidda saura sae
tambayarta ya mijinta suke ta ki basu amsa,
mota suka ga yyi parkn dai dai inda suke,
Ashnaah ta mike tana murmushi ta nufi motar,
duk suka bude baki suna kallonta don tunda suka
fito lecture ta kebe gefe guda tana waya basu
kuma san da wnda take ba, bude motar tayi ta
shiga, ya wara ido yana kallonta yace "waow my
Ashhyy I missed yhu a lot " Ashnaah tayi
murmushi tana kallonsa ita ma tace "same, sae
da shidda ya kusa ka xo ko?" Yace "wllh daga
xaria na taso sbda ke Ashnaah" tace "eyya to ya
aiki ya kwana biyu" Yace "Alhmdllh dear, kin
rame da yawa," murmushi tayi tace "ba dole ba"
ya dan yi shiru snn yace "kin san bae dace mu
xauna hka ba kina da aure Fateema, let move out
mu samu ko karkashin tree ne mu xauna sae mu
yi mgna" ta hade rae tana kallonsa tace "hka
nace maka," yace "no dats d reality" Ashnaah
tace "to na ji sae anjima" kiranta yyi a hnkli ta
juyo tana kallonsa yace "ba mgnan fushi bne
wnn its d fact," Ashnaah ta sakar masa kuka
tace "ni ban san ynda xanyi ya sake ni ba, bana
son shi, na tsanesa ya cuce ni, ya raba ni da
kowa nawa" kuka ssae ta shiga yi, usman yyi
shiru ya rasa abun cewa, can yace "to ina kika
san shi Ashnaah" bata boye masa komae ba ta
fada masa abun da ya faru tun daga farko har
karshe, usman ya kasa daina kallonta da mmki, a
hnkli yace "to ynxu ya kike so ayi" xata yi mgna
ta hango motar Khaleel, cak komae na ta ya
tsaya ganin dan nesa da su yyi parkin, tana
kallon usman tace "na shiga uku gashi can ya
xo" juyawa yyi yana kallon motar Khaleel, a
tsorace Ashnaah tace "kasan me ka dan koma ta
can sae in fito" bbu musu yyi ynda tace masa, ta
bude Jakarta ta ciro nikaf da sauri ta sa snn
tace "sae mun yi waya" ya gyada mata kai ta
bude motar ta fice kmr munafuka. Da sauri da
sauri ta isa gun da motar Khaleel yake tun daga
nesa ya hangota ya kafa mata ido, tana iso wa
ya hade rae yace "Daga ina kke" ita ma ta hade
rae tace "cafe mana, na je foto copy" fito masa
da handouts din Jakarta tayi da sauri tana nuna
masa, bae ce komae ba ta xaga ta bude motar
ta shiga ya tada suka bar wajen. Karfe takwas
da rabi Khaleel ya shigo gida daga masallaci,
Ashnaah na xaune falo da Ameesha suna kallo
suna cin abinci, kallon abincin Khaleel ke yi yana
yatsine fuska yace "meye wnn" Ameesha tace
"jollof rice ne" yyi mata wani mugun kallo yace
"kin ga ina cin sa ne da xaki girka," ta dan yi
shiru snn tace "Ca tayi muyi jollof ne shi yasa
nayi" Tsawa Khaleel ya daka mata yace "ita wa?
Ita ta ajiye ki ko ni" Ameesha tayi shiru, Ashnaah
ta mike hade da yin tsaki ta nufi sama da plate
din abincin ta kmr xata tashi sama, masifa
Khaleel ya shiga ma Ameesha kmr xae maketa
ita dae bata ce komae ba har don kansa ya gaji
yyi shiru ya nufi sama, sae a snn Ameesha ta
fashe da kuka Ashnaah ta sauko a fusace tana
kallonta tace "sae ki xauna takaicin namiji ya
kashe ki, shi din wa da xae tsaya yana maki ihu
kmr wani ubanki, iyye? idan ya maki ba kya iya
ramawa sae da ki tsaya kiyi ta kuka, to wllh xa ki
sha wahala, hka kawae ya maida ki kmr baiwarsa
kullum cikin masifa, to wllh gwara ki canxa halin
ki in xa ki ji ta nawa idan ba hka ba kina da
wahala, kuma ko gobe abinda ran mu ke so a
gidan nn xa mu girka, da da bae auro ki ba wani
ke masa girkin ba eatry yake xuwa ba, to ynxun
ma sae ya koma can" ynda kasan wata uwa da
'yar ta hka Ashnaah ta sa Ameesha a gaba tana
mata fada, Khaleel da tun saukowar Ashnaah shi
ma ya fito ya tsaya daga stairs yana kallonta
yana murmushin courage dinta.
Chapter 42 · 0% Book details