← Book details Dr Khaleel Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 95

Sashe 45

Dr Khaleel Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
64.....
Khaleel ya dago kai yana kallonsa yace "hka nn kawae me xan je in yi kmr wani mara aikin yi" Najeeb yace "ohh six months bck da kayi birthday dinka baka da aikin yi ne ko?" Khaleel yyi murmushi yace "bani da iyali ne a lkcn, da ina da baxan yi ba" Najeeb yace "cum on, kar kayi mana fuck up guy, kasan Maska won't be happy, ynda kuke da shi kace baxa ka birthday nasa ba is nt fair" Khaleel yyi tsaki ya ci gaba da abinda yake yace "ina ga kai gama aikin da ke gaban ka Yau shi yasa kke interruptn dina" Najeeb ya mike ya fice daga office din yana tunanin ta inda xae ja ra'ayin Khaleel su je birthday din abokin nasu. Karfe takwas da rabi Khaleel ya shigo gida, Ameesha da ke kitchen tana wanke wanke ta fito tayi masa sannu da xuwa xata karbi briefcase din hannunsa yace "don't bother je ki ki ci gaba da abinda kike" sama ya nufa har xae shiga dakinsa sae kuma ya nufi dakin Ashnaah tana kwance tana Duba handout din Chem, kallo daya tayi masa ta mayar da idonta kan abun hannunta, juyawa yyi ya rufe mata kofar ya nufi dakinsa, kasa bacci Ashnaah tayi ranan sae tunanin ynda usman xae yi ya sa Khaleel ya saketa take, ita dae ta ga ynda xa ayi wnn abun. Washegari da safe Khaleel ya xaune dinnin Ashnaah ta sauko da shirin sch, ta nufi dinnin din ta hade fuska tace "na shirya" wani mugun kallo yyi mata yace "kin ma raina ma kanki hnkli yarinyar nn, shi lecture din kullum ake yi da safe" hararansa ta shiga yi tace "da baka sani ba" yace "to bbu inda xa ki yau har sae kin kawo min timetable din ki" da sauri ta bude jakar hannunta ta fiddo timetable din ta ajiye masa gabansa, dauka yyi yana kallo, can ya ajiye ya ci gaba da shan tean gabansa, juyawa tayi ta koma falo ta xauna. Ameesha ta fito daga kitchen din ta nufi dinnin ta ja kujera ta xauna tana kallon Khaleel, daga kai yyi yana kallonta yace "lfya?" Ta dan yi murmushi tace "dama ina son ka bar ni in koma aiki ne plss" ajiye cup din hannunsa yyi ya hade rae yace "amma baki da hnkli, keep dis at d bck of ur mind dat as far as u remain in dis house bbu aikin da xa kiyi, Kinga nayi kama da irin maxa masu barin matansu su yi aiki" hawaye ne ya ciko idonta, ya Mike ya dauki wayoyinsa ya bar dinnin din, Ashnaah da ke xaune falo tayi dariya ta mike tana kallon Ameesha tace "sae kuma kika yi shiru kmr wnda aka dinke ma baki" juyawa tayi ta fice daga falon Khaleel ya bi ta da kallo. Khaleel na haraban hsptl yana xaune da wani patient dinsa suna hira najeeb ya karaso shima ya jawo kujera ya xauna bayan sun gaisa da patient din, patient din ya Mike yyi ma Khaleel sallama ya nufi cikin hsptl, Najeeb yace "Maska ya daga birthdayn sa sbda Kai, I told him u re very busy dis wk ba lallai ne ka samu xuwa ba, nd he decided to let it b on Sunday kaga wk end knn don hka baka isa kace baxa ka ba wllh" yau Sunday Ashnaah ta sauko falo rike da bucket dauke da hijjabanta da ta wanke a bayinta, Khaleel ya juya yana kallonta yace "ina xa ki" tace "shanya xan yi mana" ya mike da sauri yana kuma kallon dan ves din jikinta yace "a hka xa ki fita" ta hade rae tace "to su waye a gidan" wani tsawa ya daka mata ya nufi inda take ta ajiye bucket din da sauri ta bar gun tun kan ya iso tana hararansa, daukar bucket din yyi ya fice daga falon, Ameesha dae na kitchen tana lunch, yana fita da kmr minti biyar aka bude kofar wata mata ta shigo falon da sallama, Ameesha ta fito da sauri daga kitchen ta rungumeta cike da murnan ganinta suka karaso cikin falon, Ashnaah dae sae kallon matar take ko ba a gaya mata ba ta ga alamar uwar Ameesha ce, Matar tace "me kike yi a kitchen" dae dae nn Khaleel ya shigo falon rike da bucket, da mmki yake kallonta yace "Mama ke ce a gidan namu sannu da xuwa" a takaice ta amsa masa ya karaso cikin falon ya gaisheta da ladabi ta amsa bbu yabo bbu fallasa, Ameesha ta juya tana kallon Ashnaah tace "mum dita knn" Ashnaah tace "ae na ga alama ina yini mama" kin amsawa hajiyar tayi, Khaleel ya Mike ya nufi stairs ya ajiye mata bucket dinta snn ya haura Sama. Ashnaah ta tabe baki tace "ikon Allah" juyawa tayi ita ma ta nufi sama, hajiya ta mike tana kallon Ameesha fuskarta a daure tace "mu tafi daki" mikewa tayi suka nufi sama xuwa dakinta, Ameesha tayi shiru tana sauraron irin hudubar da uwar tata ke mata tana digestn, har ta Kai aya snn ta xuge Jakarta ta fiddo wani abu kulle a fallen xani ta hade rae tace "saura kuma don ubanki ki ki yi" Ameesha ta marairaice tace "amma fa ni momy tsoro nake ji" ta ja kunne ta da karfi tana huci tace "don ubanki ki xauna takaicin namiji da matarsa ya kashe ki tunda ke kince yar wahala ce," Ameesha tayi shiru tana kuma nazarin abubuwan da mum dinta ta gaya mata, kuma fa hka ne kila Ashnaahn ma ba xaune take ba don tana mmkin ynda duk irin tsiwan da take na Khaleel baya Mata komae sae dae yyi ta kallonta batun kuma yace mata baya sonta. Karfe biyar na yamma hajiya ta bar gidan, Khaleel na jin fitar ta ya shigo dakin Ameesha yana Mata mugun kallo yace "bna toleratin wnn a gidana in ganin juna kuke son yi to ki dinga shiryawa kina xuwa can gidanku kina samunta," hade rae Ameesha tayi bata ce komae ba har ya juya ya fice daga dakin ta dan yi murmushi a xuciyarta tace xaka gane kuranka. Karfe shidda da yan mintuna Khaleel ya shirya cikin nml dressing dinsa na 3qtre da farar polo ganin ynda abokansa ke ta damunsa da kira, ko kadan bae son ko wannensu ya xo gidansa shi yasa yyi deciding ya tafi kawae, ya fito dakinsa rike da car key dinsa har xae sauka sae kuma ya kuma juyawa ya nufi dakin Ashnaah, bacci ya sameta tana yi, durkushewa gabanta yyi yana kallon fuskarta ya daura hannu a hnkli kan shafaffen cikinta ta bude ido da sauri yyi saurin cire hannunsa ya mike tsaye, mikewa xaune tayi tace "meye hka" juyawa yyi ya fice daga dakin ta bi sa da kallo, ta koma a hnkli ta kwanta tare da lumshe ido. Ko kadan Khaleel bae ji ddin ynda ya tarar abokanan nasa ke partyn ba duk da yasan yyi abinda ya fi hka, mata ne cakude da maxa ana ta tsiya wasu kuma na ta rawa, ga hayakin cigarette ko ta ina, wutan gun very dim, Najeeb da yyi mugun farin cikin ganin khaleel ya nufe sa da sauri yace "welcm frnd dama kai ake jira " Maska ya nufo sa shima yana yar dariya yace "har na fara shirya irin rashin mutuncin da xan maka wllh" Khaleel yace "ae tun da nace xan xo xan xo, but ban ji ddin gayyatar mata da kuka yi ba nn" hararansa Maska yyi ya bar wajen, Najeeb yace "to in ba a gayyace mata ba meye amfanin partyn. Cum on wani wine xa a kawo maka" Khaleel yace "no, soft drink ma ya isa bana shan wine a waje kai ma ka sani" Najeeb ya hade rae yace "cum on b ur self mana ina kaga alamar soft drink a nn," Najeeb bae jira cewarsa ba ya nufi gun in da drinks suke ya dauko masa wani wine ya kawo masa, Khaleel yace "
Kai! So kke in kasa xuwa gida yau ko, ae kasan bana shan irin wa ennan bae kamata ku siyo irin wnn wines din ba ma, sae ku haukatar da mutane cikin daren nn ae, just get me a bit cool one, bana son disgracing kai na yau" Najeeb yyi dariya ya koma ya dauki wine din da yasan Khaleel na sha, ya bude ya tuttulal cikin tumblers din dake ajiye wajen snn ya bude wnda Khaleel yace baya so ya xuba cikin kwalban ya rufe ya kai masa, Khaleel ya karba ya bude ba tare da ya bukaci cup ba ya kafa kai, cire bakinsa yyi da sauri yace "taste din ya canxa, kasan na dde bn sha wnn ba" Najeeb ya daga kafada ya bar gun yana murmushi a xuciyarsa yace "forever xan raba ka da damsel din nn coz she is nt meant for yhu, Khaleel ya ci gaba da shan wine din.
Chapter 45 · 0% Book details