← Book details Dr Khaleel Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 95

Sashe 49

Dr Khaleel Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
68.....
Da sauri Ashnaah ta bar jikin kofar jin yana bubbugawa ta bude handbag dinta ta saka takardan a ciki snn ta shige bathroom, komawa khaleel yyi bedroom dinsa ya dauko spare key din dakinta snn ya dawo ya bude kofar, bin ko ina na dakin yake da kallo snn ya nufi bathroom ya murda ya ji shi a rufe, daga ciki tace "wae meye ne hka ni ka kyaleni wanka xan yi" bae ce Mata komae ba ya jingina jikin bangon kusa da kofar bayin duk da jirin da yake gani, ya kusa minti sha biyar tsaye a wajen Ashnaah taki fitowa, ita kam bbu abinda take sae hawaye, ta rasa meyasa kuka ya ki tsaya mata, jin shirun yyi yawa yasa ta bude kofar bayin a hnkli ta fito don a tunaninta ya bar dakin, ba karamin kara ta saki ba da ta gansa ta juya da sauri xata koma yyi saurin rikota ya rungunmeta lkci daya, sakar masa kuka tayi ta shiga kkrin kwace kanta yaki saketa yana kallonta yace "me kika dauka a drawerna? ina yake" ta hade rae har lkcn tana kiciniyar kwace kanta tace "da'alla ni ka ka sakeni bn dauki komae ba" kallon cikin idonta ya tsaya yi ta dauke kanta da sauri, ya saketa a hnkli ya juya ya fita daga dakin, Ashnaah ta bi sa da kallo snn ta sulale kasan dakin ta shiga rusa kuka kmr warce aka aiko ma da sakon mutuwa. Har kusan shidda Ashnaah bata mike daga inda take ba sae dae ta daina kukan da take, sae da ta fara jin kiraye kirayen sllhn magrib snn ta mike da kyar ta nufi bathroom ta wanke fuskarta ta fito ta xauna gefen gadonta, duk ta rasa particular tunanin da take a xuciyarta, tana jin an tada sllh ta mike da sauri ta ciro hijab dinta snn ta dauko handbag dinta ta nufi kofa, a hnkli ta tura kofar ta fita ta sauka downstairs, bbu kowa falon hkn ya bata damar fita da sauri, gate a rufe yake bbu ko wani mai gadi a nn, tasan suna masallaci, ta shiga bude gate din da sauri snn ta fice, sauri sauri gudu gudu ta nufi bakin titi ta sayar da adai daita sahu ta gaya masa inda xata snn ta shiga. Bakwae da kusan rabi Ashnaah ta isa kofar gidansu, ta fiddo kudinsa ta mika masa snn ta nufi gate dinsu, a sanyaye ta karasa cikin gidan tana kallon motar Abbanta da ke Parke, a hnkli ta tura kofar falonsu ta shiga bata samu kowa falon ba ta nufi sama da sauri ta bude dakin mum dinta ta shiga, xaune ta sameta kan darduma caxbi a hannunta, da mmi take kallon Ashnaah, Ashnaah ta sakar mata murmushi tace "sannu momy bari in yi alwala" bathroom ta nufa da sauri tayi alwala ta fito snn ta tada sllh, sae da ta idar snn momy ta juya tana kallonta da mmki tace "daga ina hka" Ashnaah ta kirkiro murmushi tace "ya xo gun wani frnd dinsa ne a nn wajajen shine nace ya bar ni in karaso gida" momy bata ce komae ba, Ashnaah ta gaisheta amsa tana kallon yar tata, ko kadan Ashnaah bata Bari momynta ta lura da komae ba, tace "Abba na nn ko momy" momy tace "yana dakinsa" Ashnaah bata tambayi yar uwarta ba don tasan tana gidan inna, tambayarta momy tayi ko ta ci abinci Ashnaah tace ta ci, don bata jin cin komai, har tara da rabi, momy bata ga Ashnaah na cewa xata tafi ba, momy ta shigo dakinta tana kallonta tace "wae ba yau xaki koma bne, kinsan Abbanku fa bae san kin xo ba" Ashnaah tayi shiru snn tace "sae gobe momy" momy tace "to tun da kwana xa kiyi ki tafi ki gaida Abban ku kar ya gan ki gobe ya xame min abun mgna" Ashnaah ta gyada ma mum dinta kai kawae, momy ta juya ta fita, kuka Ashnaah ta shiga rerawa a hnkli tana tunanin ynda iyayenta xasu dauki xancen da ta kawo masu. Khaleel kam na dawowa daga masallaci ya nufi dakin Ashnaah, bae sameta a ciki ba hkn yasa ya nufi bathroom nn ma bata nn, fitowa yyi ya shiga dakin Ameesha ya sameta xaune kan darduma, yace "fateema fa" Ameesha tace "tun hudu ta hau sama, tana dakinta" juyawa yyi ya fice daga dakin, bbu inda bae duba ba a gidan amma bae ga alamar Ashnaah ba hnklinsa yyi mugun tashi, to ina ta tafi da daren, masu gadi ma suka ce basu ganta ba, sama ya koma ya dauki makullin motarsa ya sauko, rasa inda xa shi nemanta yyi, lkci daya ya shiga tunanin to takardar meye ta gani daxu ta ki ba sa, gidansu ya nufa kawae goma saura qtr ya isa kofar gidansu, ya fito ya nufi gun mai gadi, bayan sun gaisa ya ke tambayarsa ko Ashnaah ta xo, yace masa eh, sae da ya fara sauke ajiyar xuciya snn yace "to ka min mgna da ita don Allah" mai gadi ya nufi cikin gidan, Abba ne ya bude kofar yana kallon mai gadin yace "ya aka yi Musa" mai gadin yace "wae mai gidan fateema ne ke jiranta a waje" Abba yace "wace fateemar" Mai gadin yace "fateema dae" juyawa Abba yyi ya nufi sama ya bude kofar momy fuskarsa a daure yace "me yarinyar nn ta xo yi gidan nn yau ba tare da na sani ba" Momy ta hade rae tace "bn gne me ta xo yi ba" fada ssae Abba ya shiga yi yace "ta xo ta fice masa daga gida mijinta na jiranta a waje" Ashnaah da ke jin duk abinda abbanta ke cewa ta shiga kuka a hnkli tasan dole ta fada masu me ya dawo da ita gida, mikewa tayi tun kan ya shigo inda take ta dauki hijab dinta da takardan sakin da ta gani ta fita a sanyaye don xuwa jin me ke tafe da Khaleel kuma. Yana tsaye jikin motarsa ta fito daga gate dinsu, kallonta kawae yake har ta karaso inda yake snn ta rungume hannayenta fuskarta daure tace "ina jin ka" kallonta kawae yake har lkcn ya ma rasa me xae ce mata, ganin hkn yasa tace "in baka da abin cewa xan koma cikin gida pls" a hnkli taji yace "me nayi maki Fateema" ta daga kai tana kallonsa don bata ma san ya san sunanta ba, sunkuyar da kanta tayi da sauri don kar ya ga hawayen dake kkrin taruwa idonta tace "me kuwa ka min baka min komae ba" shiru taji yyi bae ce komae ba hkn yasa ta fashe da kuka ssae ta mika masa takardan hannunta, karba yyi yana kallon takardan, cikin sakwannin da ba su wuce sha biyar ba ya gama karanta content din, lkci daya komae nasa ya tsaya ya sake takardan hannunsa ya fadi kasa yana furta innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Ashnaah ta duka ta dauki takardan tana share hawayen fuskarta lkci daya tana murmushi tace "nd am very happy coz I have been lookn fwrd to a day like dis, am vry glad I saw it, dama baka so na bana..." Kasa karashe mgnr tayi sbda kukan da ya ci karfinta, da kyar Khaleel ya iya bude bakinsa da yyi masa nauyi murya can kasa a sanyaye yace "wllh summa tllh bni na rubuta takardan nn ba fateema" da sauri Ashnaah ta juya ta nufi gate dinsu, kiranta ya shiga yi don kasa binta yyi har ta shige gate dinsu, hade kansa yyi da mota yace "No! no, waye yyi min hka" lkci daya hawaye ya cika idonsa. Ashnaah na shiga falon su ta nufi falon Abbanta jiki ba kwari rike da takardan a hannunta, xaune ta same sa da momy, ta durkushe nn tsakiyar falon tana kkrin mayar da hawayen da ke neman xubo mata tana kallon iyayen nata, kasa daurewa tayi ta fashe masu da kuka ssae.
Chapter 49 · 0% Book details