Sashe 73
Buzu Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Fadila ba zan iya gaya miki ba, ku yi haƙuri kawai, Allah ya sanya mu dace" Haka ta gaji da rarrashin ta ƙyale shi.
Shukura kuwa Sagir da Yusra ba abin da suke yi sai aikin rarrashinta, da bata haƙuri, Yusra ce take kula da Haidar da jaririn da ta haifa aka saka masa Ahmad Annur.
Sai dai ta kasa yin lafiya, kusan kullum tana kwance, Alhaji Fatuhu duk kwana biyu sai yaje gidan ya rarrashe ta, ya bata haƙuri tare da kwantar mata da hankali.
****
Da sassafe Asal ta nemi Hammad ta rasa, ta tashi ta fita falo, ta hango shi a kwnace a kan kujera yana video call da Nana.
Ta tarar da shi yana cewa "Ba fa na ganin komai ma vie, dan Allah ki cire bargon nan"
"A'a nifa bacci zan yi ka ke takura mini"
"Zan rama ne Asmy, me za ki dafa zan shigo anjima in ganki in sha Allah"
"Ba zan dafa komai ba, ai yau kana gurin matarka ta dafa ta baka"
Ya marairaice ya ce "Ni ko? Shikenan tun da kin daina so na. Ɗan yi kissing goshina" Yayi maganar yana kara screen ɗin a fuskar sa. Da sauri Asal ta koma ɗaki, wani irin abu yana taso mata kamar za ta fita hayyacinta. Ji ta yi tana neman yin danasanin biyo shi ta dawo gidansa, amma ta tuna damarmakin da ya bata bayan da ya aure ta. Amma ta din ga muzguna masa, saboda hure mata kunne da Imam Omar ya din ga yi. Bai san daɗin aure ba sai da ta fara hankali ta fuskanci ba ya tanka duk rashin mutuncin da za ta yi masa. Idan zai yi magana a dankwafe shi. Sai a gaɓar da ta dawo hayyacinta ta gane shayi ruwa ne, take sonsa a lokacin ta fara karɓar sakamakon abin da ta aikata. Yanzu ba ta da wani abin cewa sai abin da ta gani kawai. Ta sha kukanta ta gode wa Allah.
Nana an kai mata hadimai, duk da ba komai ta sakar musu ba. Har gida aka kawo mata dalleliyar motar da aka bata a gurin bikinsu, wanda Imam Zahradeen sabon Tafawan Agadez ne ya ba ta. Banda uban gwala-gwalai da ta samu. Ta fuskanci gold ne kyauta mafi tsada da muhimmanci da suke ba wa mutum mai muhimmanci mussaman ma mace.
Lefenta kuwa, sai da ta din ga addu'a, saboda yadda mutane suka camfa duk auren da aka yi ɓarna a gurin yin sa ba ya ƙarko. Sai dai Hammad ya ce mata ai abin da aka yi mata kyautatawa ce, ba wai dukiyar aure ba. Kuma Allah ne ya tsamo ta ya bata rabonta ne. Ya kuma tuna mata a yadda aka yi auren su.
Nana abin har kunya yake bata, yadda manyan mata wasu ma sun haife ta suke zuwa gidan, wai sun zo su gaishe ta, kuma in dai za su zo sai sun riƙo abin bata.
Ta fara yi wa Nene ƙorafin ita wannan abin da ake yi mata ta gaji. Nene ta ce "Waye ya gaya miki ana shiga dawa dan ƙarya? Ai girma ne ya hau kanki, dan haka dole ki yi haƙuri. Ba kuma a yi wa masu mulki kyauta su mayar su ce a'a, dole ka karɓa. Kuma dole kema ki zama mai yawan kyauta. Sannan ki ƙirƙiro wani abu da zai amfani mata a ƙasar nan, saboda tabattar da za ki iya riƙe muƙamin da aka baki"
Nana ta ce "To Allah ya bani iko, abinka da ba a saba ba"
"Ke yi wa mutane shiru ke da ba a saba É—in ba, dole a saba yanzu"
Haka Nana ta din ga jin tamkar an É—aÉ—É—aure ta saboda takura.
Ranar da Hammad zai dawo, ya dawo tare da Muhsin, ta din ga murna dan har ta fara karaya Zahradeen ba zai bata É—anta ba, ga shi tana jin nauyinsa, amma ta fara matsuwa da son ta yi magana.
Nana ta ce "Sayyid amma ya dawo kenan ko?"
Sayyid ya ce "To gamu nan dai, babansa sai masifa yake yi, sai da Sultan ya kira shi ya ce ya bamu É—anmu. 'yan biyu sai kuka suke yi."
Nana ta ce "Ina ma zan iya bar masa shi, amma raba ni da É—ayanku kamar raba ni da rayuwata ne"
Hammad ya ce "Idan ma bayarwar ne, ba gara ki ba wa Asal ba?"
Wani mugun kallo ta yi masa, da ya sanya shi yin shiru, ta saɓa ɗanta ta yi ɗaki.
Baba gaba ɗaya ji ya yi kewar Nana ta dawo masa sabuwa fil, kamar a lokacin ta ɓata, daga ita har Imran, amma mussaman ma ita Nanan. Gaba ɗaya ganin da ya yi mata ya ji ɗanɗani haukaci ne. Kusan kullum sai sun yi waya ta what'sapp. Har yake gaya wa Nana an kai wa Gaddafi kuɗin aure. Ta din ga murna sosai. Ta ce "Baba Dan Allah ka yi wa Sarkin baka magana a kansu Suwaiba, dan Allah"
"Wallahi Nana a kan yi mini maganar yaran nan, zan daina kira mu yi magana"
Gaba ɗaya Nana ba ta jin daɗin hakan da Baba yake yi. Haka take kiran Ummanta ma, su yi waya da su Walida. Sai ga Iliyasu da karɓar waya, su gaisa da Nana yana neman yafiyarta a kan abubuwan da suka faru.
Har ga Allah Nana ta tsani mutumin nan, ba zata manta abubuwan da ya yi mata ba, amma ta duba matsayin da Allah ya kaita a yanzu, dan haka ta ga ba girmanta ba ne ma zaman jin haushin wani ba.
****
Kwanaki huɗu kenan, Alhaji Zailani kamar wanda aka yi wa asiri, ya kasa barin gidan, ga shi dare da rana tsorata shi kawai ake yi a gidan nan. Banda ihu marasa daɗin ji, a ɗauke shi a yi ta bugawa da ƙasa.
Ko ya yi ta maƙabarta waɗanda ya bayar a ƙungiyar asiri, suna ta kokowa da shi za su danna shi a cikin kabari su rufe, yana ihu yana ƙoƙarin fitowa, ko kuma ya ga su na ƙoƙarin kashe shi. Duk yadda ya so sarrafa tunaninsa domin ya je gurin Malam Gambo neman mafita, amma ya kasa jin sa kawai yake yi a wata Duniyar daban.
Tsawon kwanakin nan ya galabaita, ba ci ba sha, ba wanka ga kufcewar hankali. Yaje kitchen ya ɗaukko wuƙa ya riƙe yana zazzare ido, da nufin yana ganin sun fito masa ya caka musu.
Sai dai Shukura ta bayyana, da wuƙar nan a hannunta, su na ta kokowa da shi, yana ƙoƙarin kar ya caka mata, saboda zuciyarsa na raya masa, itakaɗai ta rage masa yanzu. Kawai ya hango Alhaji Fatuhu na ƙyaƙayata masa dariya yana faɗin "Yanzu wa ya yi nasara? Ka rasa komai Zailani. Ba ka da kowa, ka kashe kowa naka, dukiyar kuma ba zata amfane ka ba. Ni kuma da ka yi niyyar hallakawa, komai nawa ya dawo, ga shi kuma dole mutuwa zaka yi" Ya saki Shukura ya nufi Alhaji Fatuhu yana faɗin "Na tsane ka, ba na ƙaunarka. Ba zan taɓa sonka ba kuma sai ka mutu, sai ka riga ni barin duniyar nan, na yi yadda nake so". Ya yi maganar yana cakawa Alhaji Fatuhu da yake gani wuƙar nan a cikin sa.
Jini ne ya fara fitowa ta bakin Alhaji Fatuhu, ya ce "Zailani wannan shi ne ƙarshen duk wanda ya gaza sarrafa ni. Ka kasa kula da ni a lokacin da na kamu da rashin lafiya. Ciwon ƙyashi ya kama ni, son duniya, hassada, mugunta, ƙeta na bushe na yi baƙi, har ka gaza sarrafa ni kullum burinka biya mini buƙatar duk da na bijiro maka, wanda ina bijiro maka buƙatuna ne, saboda samun sassaucin wannan ciwukan da suka kama ni, ka ƙi kulawa ka bani magani. Ga shi biyan buƙatuna ya sanya ka aikata abu mafi muni, ga ƙarshe mara kyau"
Alhaji Fatuhu ya sake caka wa Alhaji Fatuhu da yake gani a gabansa. Wata irin zabura ya yi tare da kurma wani uban ihu, jin wani irin gigitacciyar azaba da raÉ—aÉ—i ya ratsa cikinsa.
Abin da bai sani ba, da ya ɗauki wuƙar nan kansa y fara cakawa, ya fita waje yana tangaɗi, yana faɗin "Na kashe ku ɗin, na fi son duniya a kanku. A lahira rahamar Allah za ta saka na shiga aljanna a Duniya kuma ƙoƙarina ne zai tara mini abin duniya" Ya din ga surutu yana faɗar miyagun ayyukan da ya din ga aikatawa. Kafin a yi ƙoƙarin ƙwace wuƙar ya sake caka wa kansa a cikinsa, ya sulale ya faɗi ƙasa, jini yana zuba a jikinsa. Yana faɗuwa bakinsa a buɗe, Aljanin da ya mallaka ya bar gangar jikinsa.
(Ya hayyu ya Æ™ayyum ya zuljalalu wal ikram Ubangiji Allah ka sanya mu yi kyakykywan Æ™arshe, Allah ka raba mu da mummunan Æ™arshe, Allah kar ka sanya mu cuci kowaðŸ™ðŸ™ðŸ™ðŸ˜)