← Book details Buzu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 82

Sashe 19

Buzu Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ta yinƙura ta nufi wani jibgegen fridge da yake ɗakin, ta je ta buɗe. Ta ɗaukko ruwan roba ta zo ta zauna a kusa da shi. Ta cire masa rigarsa jikinsa. Ta ƙara shashasha masa ruwan nan. Ta lura da yadda jikinsa yake rawa, yake kallon ruwan hannunta da har raɓa yayi saboda sanyi.
Ta kalli ruwan hannun nata ta kalle shi, kamar yadda ta gan shi a bacci, ya rame sosai fatarsa duk ta bushe saboda rashin ruwa. Leɓensa har tsagewa yayi. Ikon Allah ne kawai ya raya shi zuwa wannan lokaci ba ci ba sha.
Ta ce "BuÉ—e bakinka" bakin yana rawa ya buÉ—e. Ta É—aga jarkar za ta zuba masa ruwan su Matawalle suka sake shigowa.

Sardauna ya ce "Ke, mene ne wannan za ki ba shi?"

Nana ta ce "Ruwa ne, a fridge É—in can na É—aukko"

Sultan kuwa sai da ya É—an rikice ya ce "Matawalle ya tashi"
Nana ta fara zuba masa ruwan a bakinsa, ya kai hannunsa biyu ya danƙe jarkar yana ɗaɗɗakar ruwan. Ƙoƙarin ƙwace ruwan Nana take yi, amma ya shanye. Yana shanyewa kuwa ya yi mata amai a jikinta har ta hancinsa haka ya din ga fitowa.

Matawalle ya ce "To ko Asibiti za a tafi a kai shi?"

Sultan ya ce "ÆŠan jira mu gani"

Yana gama aman ya kifa a kafaÉ—ar Nana. A hankali ta ce "Ka gani, saboda kar ka yi amai ya sanya na so na baka a hankali. Sannu" Ya yi shiru yana ajiyar zuciya.
Ta kalli Mahmoudu ta ce "Taimaka ka kuma ba ni wani ruwan" Da sauri Mahmoudu ya sake É—aukko ruwa ya kawo mata.

Ta ɗago shi ta ce "Yanzu a hankali za ka sha, kar ka kuma yin aman, za din ga zuba maka kana haɗiya" Haka aka yi, ta din ga zuba masa a hankali yana sha, yana yi yana ƙoƙarin kai hannu ya riƙe robar, tana riƙe hannunsa tamkar ƙaramin yaro.
Nana tana son ta sake da shi, amma idonsu Sultan, ya sanya ta din ga komai a É—arare gudun kar ta yi wani abu su yi mata wata fassarar ko sharrin. Ya jingina yana ta haki saboda duk ya galabaita.

Mahmoudu ya ce "Kuma ke bai shaƙe kin ba da muka fita?"

Nana ta yi murmushi ta ce "Ramin kura ai sai 'ya'yanta Habu. Ka samo mana ko kayan marmari ne da shayin Buzaye ya sha. Ai za ka sha ko?" Ta yi maganar tana kallonsa.
Ya ci gaba da kallon ƙwayar idon Nana, maganganu ne fal a cikinsa, amma babu halin furta su"
Su na ta jera masa sannu, amma babu wadda ya amsa a ciki.

Matawalle ya ce "Bari na yi magana, a sanya hadimai su kawo kayan marmarin ya ci"

Nana ta ce "A'a ranka ya daÉ—e, a saka Mahmoudu ya kawo" Duk suka tsaya suna kallon Nana, amma aka rasa mai magana.

Nana ta nuna masa Sultan ta ce "Ka san wannan?" Ya jinjina mata kai alamar eh. Wannan fa? Ta nuna Mahmoudu nan ma ya jinjina kai.
Ta ce "Ni fa?" Sai ya yi shiru, har ta fara karaya, da tunanin ko memory ɗin nasa ya sake ƙwacewa ya manta da ita.

Kawai hawaye ya fara zirarowa daga idanunsa.

AREWABOOKS
Cikin damuwa Nana ta yi masa murmushi ta girgiza masa kai.

Sultan ya ce "Hammad, me yake damun ka ne? Akwai wata matsala ne?"

Ya yi shiru bai kula Sultan ba, Nana ta yinƙura ta ce "Bari na je na wanke aman da ya yi"

Sardauna ya ce "Kar ki damu, za a kai ki inda za ki kwana, ba ma son kowa ya san kina nan. Za a baki wasu kayan ma sannan za a zo a gyara gurin. Kai kuma idan ka kawo Abincin sai a ba shi"

Nana ta jinjina kai, ta yinƙura da niyyar ta tashi, amma ya damƙe hannunta cikin nasa gam.
Ta dube shi ta ce "Mene ne?" Ya tsare ta da idanu.

Ta ce "Kar ka damu, ba nisa zan yi ba, zan dawo in sha Allah" Ya damƙe hannunta ya ƙi saki, yana murzawa a hankali.

Matawalle ya ce "Ka na ji Imam, zamu je a kai ta masauki ne, inda za ta zauna ta huta, kaima ka ci abinci kafin a san abin yi, an tafi samo mai magani da zai duba ka."

Kamar sassaƙe, haka ya yi shiru ya riƙe hannun Nana.

Sardauna ya ce "Ina ga mu bar ta tare da shi kawai, zuwa da safe sai mu san abin yi"
Haka suka mimmiƙe, ƙiri-ƙiri suna ji suna gani, suka kama hanyar fita, su bar shi da Nana.

Nana ta ce "Habu, dan Allah É—an tsaya ka taimaka mini" Ya ce "To"
Bayan fitar su Nana ta ce "Dan Allah ka kawo mini kayana, sannan ka kawo mini kayansa guda biyu. Ka kawo mini Alkur'ani. Sai kuma Abincin nan dan Allah duk yadda za a yi kai tsaye daga hannunka zai zo, kar ya biyo ta hannun kowa. Sai kuma ina son ka kawo mini habbatussauda da tazargade, da ganyen magarya sai almiski ja"

Ya ce "In sha Allah ranki ya daɗe, yanzu kuwa. Sai dai su abin da ki ka lissafa ɗin nan, sai dai na shigo da su a ɓoye kar su ce wani abin za a yi masa"

Nana ta ce "Idan da matsala ba sai ka kawo su ba, kawo mini Abincin da kayan kawai, kar na saka ka a cikin matsala. Amma lokacin da hakan tana faruwa da shi da muna Nigeria, idan na yi masa amfani da su yana samun sauƙi sosai"

Mahmoudu ya ce "Kina nufin a Nigeria, yana irin haka?"

Nana ta jinjina kai ta ce "Har ɓarin jikinsa sai da ya shanye, ka kawo mini Abincin da sauri na ba shi"

Ya ce "To" Ya kalli Hammad ya ce "Sannu Imam, Ubangiji Allah ya sanya kaffara"

Sai da Mahmoudu ya fita sannan ta kalle shi ta ce "Cika ni na je na wanke jikina, ka ga ka yi mini amai a jiki" A hankali ya saki hannunta, amma har ta shiga banɗakin nan kallonta yake yi. Ta wawwanke jikinta ta fito ta ƙara goge gurin da ya ɓata da aman.

Matawalle ya ce "Anya abin nan ba shiri ne yaran nan suka yi ba, saboda ya ci gaba da zama da yarinyar nan ba?"

Sardauna ya ce "Nima sai da na yi wannan tunanin"

Sultan ya ce "Bana tunanin shiri ne, babu yadda za a yi ya kwana takwas babu ci babu sha, a kwance a guri ɗaya a ce shiri ne. Kai Matwalle ka manta abin da ya din ga yi, lokacin da aka gano shi a Nigeria aka dawo da shi. Ba magana ba cin abinci a sume kawai kuma aka rasa abin da yake damunsa sai da muka je faransa sannan ya dawo hayyacinsa?" Ya yi maganar yana ƙoƙarin hana kansa, yi musu cikakken bayanin labarin da Mahmoudu ya ba shi, mussaman cewa da aka yi idan aka dawo da shi Nijar, zai iya haukacewa ko ma ya rasa ransa gaba ɗaya".

Sardauna ya jinjina kai ya ce "To ai ita kanta yarinyar abar tsoro ce, ba ku ga abin da take yi ba? Ni abubuwan sun É—aure mini kai sosai da sosai fa"

Sultan ya ce "Tabbas lamarin akwai É—aure kai, da ayar tambaya, dama Hammad ya gaya mini wani abu, amma dai bari mu ga abin da Allah zai yi, sannan mu jira zuwan mai maganin da aka tafi nema"

*****

Mama ce take kallon Jamila cike da baƙin ciki da takaici. Kamar ta danne ta ta yanka ta ce "Jamila, so ki ke sai duniya ta san halin da muke ciki? Kin zaɓi mutuncinmu ya zube a rasa wanda zai aure ki saboda wannan abin kunyar. Tun kafin ya riƙa mu je a cire shi kin ƙi, Jamila kin fi son asirinmu ya tonu ko?" Ta yi maganar muryarta na rawa.

Jamila ta girgiza kai hawaye na zuba daga idanunta ta ce "Mama ba zan iya zubar da cikin nan ba wallahi, ni tsoro nake ji, kuma kar zunubin ya yi mini yawa ba ki san adadin tarin zunuban da suke kaina ba. Ki bari na ji da wasu dan Allah, ki ƙyale ni kawai"

"Jamila ni ki ke cewa na ƙyale ki? Kin gwammaci ki durƙusa ki haife mana shege a gida, Duniya ta gani a shaida?"

Mama "Na duniya daga baya ne, Allah ya riga ya shaida ya ga komai, ni yanzu addu'ata Ubangiji Allah ya yafe mini. Wataƙila haifar ɗan nan ne zai sanya na samu nutsuwa ni dai dan Allah ki ƙyale ni"

Cikin takaici ta ce "Jamila kin san haihuwa kuwa? Kin san azabar haihuwar É—an sunna balle shege, tsaf za ki mutuwa fa"

Jamila ta goge hawayenta ta ce "Idan na mutu gurin haihuwa na yi shahada, wataƙila Allah ya yafe mini tarin kura-kuren da na aikata"

Cikin tsawa ta ce "Uban waye ya ce miki mai cikin shege za ta yi shahada"
Chapter 19 · 0% Book details