← Book details Buzu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 82

Sashe 2

Buzu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yi mini shiru, kai har ka na da zarafin da ina magana da babanka ka din ga sanya baki? Ni na gaji da wannan bambanci da ka ke nunawa, sai ƙoƙari ka ke lallai sai ka tura ɗanka kan kujerar Sultan ta ƙarfin tsiya, bayan bai cancanta ba. Shi ba cikakkiyar lafiyar zuciya ba, ga rashin lafiyar ƙwaƙwalwa, kalli yatsunsa babu zobensa na tambari, ga shi tsawon shekaru da aure ba shi da magaji, ta yaya ka ke tunanin makaho ya jagoranci mai idanu? Ta yaya mutumi  da shi kansa ba zai iya tsayuwa da ƙafarsa ya yi rayuwa ba za a ce ya wakilci masarauta kamar Agadez a harkar kasuwanci"

Cikin tsawa Sardaunan Agadez ya ce "Wane irin lafazi ne wannan ka ke yi Tafawa? Kar ka manta da wanda ka ke magana, babu ruwan masarauta da gaba ka ke da Sultan, zamu iya sanyawa a warware rawaninka a hukunta ka. Hammad ba É—anka ba ne kai ma? 'yar ka fa yake aure, kuma É—an É—an uwanka ne, kai ba mai rufa masa asiri ba ne idan ma hakan ne? Batun zoben sa zamu yi bincike a kai, haihuwa kuma Allah ne yake bayar da ita, bai zama hujjar da za a ce an hana shi wata dama ba. Ko yana da É—a ko babu idan Allah ya nufi ya yi mulkin Agadez wallahi sai ya yi" Gaba É—aya gurin suka yi tsit.

Ya mayar da idonsa ga Sultan cikin girmamawa ya ce "Ina neman afuwa ya shugabana bisa É—aga murya da na yi a gaban sarki"

Hammad ya dubi Sultan a tsanake ya ce "Ina neman a yi mini izini, zan ɗan fita" Da ka Sultan ya yi masa alama, ya yinƙura ya tashi ya fita.
Zuciyar Sultan tamkar ta kama da wuta saboda damuwa da jin zafin kalaman É—an uwansa ga É—an nasa.

Kai tsaye Imam Hammad ya koma gida, zuciyarsa na yi masa wani irin zafi na maganganun da Tafawa ya faÉ—a a kansa.
Ɗakin saukar baƙinsa ya wuce, da nufin ya zauna ya kaɗaice a ciki. Kawai ya tarar da Mahmoudu a ɗakin.
Bai kula shi ba kawai ya nemi guri ya zauna idanun nan jawur.
Mahmoudu ya tashi ya koma kusa da shi, ya kalli yadda idanunsa suka yi jawur ya ce "Imam, lafiya kuwa?"
Yayi shiru kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya ce "Mahmoudu, ina son na roƙi Sultan ya cire ni daga duk wani abu da ya shafi harkar mulkin nan ba na so"

Mahmoudu ya waro ido ya ce "Saboda me? Kai ma ka san abin da ba zai yiwu ba ne ai. Ka riga ka kai matsayin Imam kuma ka san me hakan yake nufi"

"A cire ni a maye gurbina da wani, tun da akwa masu so. So nake na yi nesa da gidan nan, na samu nutsuwa na yi rayuwata cike da 'yanci yadda babu wanda zai dame ni ya takura mini. Gidan nan ji nake yi tamkar a kan wuta nake. A kan abin da bai taka kara ya karya ba an ci mini mutunci ana ce mini juya. Ni Tafawa yake ci wa mutunci saboda kawai Sultan ya ce na je faransa na wakilci masarauta? Wallahi wataran za su neme ni su rasa"
"Mahmoudu a ransa ya ce wancan karon ma da ka gudu ni ka saka a bala'i'

A zahiri ya ce "Dan Allah ka yi haƙuri, duk inda ka je ma ba zaka iya zama ba sai ka dawo, dan Allah ka yi haƙuri"

Ya yi wa Mahmoudu shiru, ya lumshe idanunsa.

Yana kwance a kan cinyarta, ya zuba mata idanu yana kallonta. Sai shafa gashin kansa take yi tana yi masa murmushi mai ƙayatarwa. Bai yi mata magana ba, ita ma ba ta yi masa ba, amma yanayin ya yi masa daɗi sosai da sosai.

Wata babbar mace ce a zaune, tana ta huci tamkar za ta fashe, cikin takaici da ƙunar rai take kallon matashin saurayin da yake gabanta.
"Zahradeen wai kai wane irin mutum ne mara kishin zuci da bai san ciwon kansa ba? Ina nan na samu labarin ka na cewa Sultan wai a tura Hammad wakilci kai da shi duk abu ɗaya ne, a gidan uban wa ku ke abu ɗaya, ana ƙoƙarin nemo muku 'yanci, amma kai kana shirme da shiririta?. Ƙarara Sultan yake nuna bambanci a tsakaninku ammma kamar ya yi maka asiri ka zama nusari. To wallahi ni ba nusara ba ce, ban tsaya tsayin daka ka zama Imam ba, sai dan ka zama Sultan ɗin Agadez. Dan haka ba zan zuba ido shashancinka ya ɓata mini wahalata ba na gaya maka".
Zahradeen ya yi shiru bai ce komai ba, shi sam bai ga wani abu da Sultan yake yi na nuna fifiko a kan Hammad ba, kawai yana ba shi kulawa ta musamman ne, saboda yanayin matsalar hawan jini da yake da ita, da kuma rashin mahaifiya.
Aka ci gaba da dambarwa, a kan tafiyar sa Faransa.
Ko da aka koma zaman tattaunawa, Mayan 'yan majalisar Sultan ra'ayinsu ya kasu biyu, wasu su na goyon bayan a tura Hammad, saboda nagartarsa da jajircewa ya cancanta mussaman da duk ya fi sauran Imam Imam ɗin ilmi da mu'amala, ga yarurruka da yake ji. Ya yinda wasu suka goyi bayan Tafawa a kan Hammad ba zai ce wakilci Agadez ba, sai sun ji ba'asin zobensa, sai kuma sun ji matakin lafiyar ƙwaƙwalwarsa. Da rahoton lafiyarsa na tsawon shekarun da ya yi a faransa.
Wannan ƙa'idoji da suka shimfiɗa ƙa'idoji ne da sai an kwashe lokaci kafin cika su, wanda har lokacin taron ya zo ya wuce, ba a kammala cika su ba.

Ganin gurin zai sake yamutsewa, ya sanya Imam Hammad yin gyaran murya. Cikin girmamawa ya ce "Ina godiya matuƙa da wannan dama da aka so ba ni, amma zaman lafiya da kwanciyar hankalin Agadez shi ne a gaba da komai. Ina roƙon a yi mini alfarmar yi mini afuwa, ba zan samu damar yin tafiya wakilcin nan ba, sakamakon hali na rashin lafiya da nake fama, ciwo zai iya kama ni a ko ina, dan haka Tafawa ya yi gaskiya, ina buƙatar hutu"

Cikin tsawa Sardauna ya ce "Ba kai ka ke da wannan hurumin ba."

"Mai girma Sardauna, gaskiya Tafawa ya faÉ—a, ban cancanci duk wannan abubuwan ba, shugabancin Imam ma zan sauka na nemi lafiyata"

"Mun san ba ka da lafiya, amma ka ka na kan magani, dan haka larura ba za ta hana ka aiki ba"

"Larurar ƙwaƙwalwa, mahaukaci ba zai wakilci masu hankali ba, ina neman afuwarku"

Daga wannan maganar ya yi waje, saboda yadda idanunsa suka yi jawur, jikinsa ya fara tsuma.

Tsit gurin ya yi aka hau kallon-kallo.

Sardauna ya ce "Ka ga abin da ka janyo ko?"

"Ai ba ƙarya na yi ba, shi ya faɗi cewa ƙarya nake yi ɗan sa ba mahaukaci ba ne?" Ya yi maganar yana kallon Sultan.

AREWABOOKS

Har wani duhu yake gani a idanunsa, saboda matsanancin ɓacin rai da tashin hankali. Mutumin da yake uba a gare shi, shi ne ya yi masa wannan kausasan laffuzan a gaban jama'a.
Ya daɗe yana nuna masa ƙiyayya, amma lamarin bai fito ƙarara ba sai bayan da ya zama Imam.  Mussaman wannan dswowar da ya yi, dan ya matsa a kan lallai sai ya ji wani ciwon ne ya zaunar da shi a ƙasar waje har shekara biyu, kuma aka hana kowa zuwa duba shi?
Ya kawo kai cikin falo, Nana tana ta aikace-aikacenta. Ɗan turus ta yi bayan da ta tuna Asal ta ce mata ba yanzu zai dawo ba. Fuuu ta ga ya nufi uwar ɗakinsa. Ta ɗan taɓe baki ta ci gaba da aikin gabanta. Sai dai zuciyarta na kan abin da ya sanya shi cikin fushi da tashin hankali haka.
Duk da ba ta da wani kusanci da shi a wannan Duniyar tasa, amma mutum ne mara magana, amma yana da yawan fara'a.

Asal ta fito daga wanka ta gan shi kwance a kan gado. Ta kalle shi ta ce "Amour ya na ga ka dawo kuma? Lafiya kuwa?" Muryar Asal kawai ta fusata shi, saboda abin da mahaifinta ya yi masa a fitarsa. Dan haka ya yi mata banza.
Ta nufi gaban mudubi ta amsa wayar da take ta ringing, ta ajiye ta dawo ta dube shi ta ce "Sultan yana neman ka a sashen sa yanzun nan"
Ya yi mata shiru, bai yi magana ba, ta nufe shi ta zauna a kusa da shi, ta É—ora hannunta a kan kafaÉ—arsa. Ya tashi zaune a fusace ya ture hannun Asal, ya tashi ya fita.
Sororo ta tsaya tana mamakin me yake damunsa haka?
Gaba É—aya ya fita ya bar sashen.

****
Cikin matsananciyar damuwa Mama take kallon Jamila da ta yi wata irin rama mara fasali, duk ta bushe ta yi haske sai uban kai É—auke da gashi.

"Jamila ni fa na rasa gane kan ki gaba ɗaya, kalli yadda ki ka koma, dole ki shirya mu je gurin masu magani ko mayu ne suka kama ki, ki ke ta wannan wahalar duk kin ƙi lafiya"

"Ni babu wasu mayu da suka kama ni"

"To idan ba mayu ba wannan ciwon na mene ne haka? Fitar nan ma da ki ke yi gurin kasuwancin naku kin daina gaba É—aya"

"Ki ƙyale ni zan warke ne" Ta yi maganar cikin ƙosawa da maganganun Mama.

Su na haka Yaya Atine ta yi sallama, Mama ta amsa tana yi mata maraba.

Mama ta ce "Ke ki ke tafe a yammacin nan?"

Ta ce "Wallahi kuwa, na ga kwana biyu ban leƙo ba, na ce bari na shigo, Isan ba ya nan ne?"

"Eh ya fita baya nan"

"Ita kuma wannan fa?"

Cikin damuwa Mama ta ce "Ba ta da lafiya ne, nayi-nayi da ita, mu je gurin mai magani ta ƙi yarda, ga na Asibitin an yi ya ƙi jiki kullum ƙara rikicewa yake yi"
"To me yake damunta ne har haka?"
Mama ta ce "To gata nan dai, kullum zazzaɓi ba ta kuma son cin abinci ko fita ba ta yi, na Asibitin ya ƙi yi mata, mu koma na gargajiya ta ƙi"
Chapter 2 · 0% Book details