← Book details Buzu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 82

Sashe 48

Buzu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ki yi haƙuri Asmyna, ki yi haƙuri ki yafe mini, ni kaina ban san abin da ya same ni ba, ban san yaya aka yi na gaza tunawa da ke ba. Ban yi miki adalci ba amma kk yi haƙuri rayuwata" Ya din ga yi mata surutai ba tare da ta san yana yi ba, saboda wani irin nannauyan bacci da take yi.
Duk da yadda burki ya so ƙwace masa, kasancewarsa da Nana a wannan yanayi, da ya din ga tariyo masa irin rayuwar da suka yi ta tsantsar soyayya da ƙauna. Ya yi iya ƙoƙarinsa gurin sarrafa kansa da kyar gurin ganin bai aiwatar da wani abu ba. A ganinsa yin hakan tamkar rashin adalci ne kai tsaye a gare ta.
Kamar wani zai ƙwace ta, haka ya matse ta a jikinsa, yana zubar da hawaye, yana sake jin wani abu na ratsa lungu da saƙo na gangar jiki da kuma ruhinsa a game da ita.
A duniya ba ya jin yana da wani abu da zai iya aikata wa Nana ya yi ko kwatankwacin saka mata a kan abin da ta yi masa.
Har gefin Asuba yana rungume da ita, hawaye kuma bai bar kwarara daga idanunsa ba, lissafi yake yi ko za ta yarda da shi, ta sake ba shi dama ta biyu. Ko kaɗan, tunaninsa da hankalinsa ba sa lissafa masa kalubalen da yake gabansa, na auren wata ƙabila baƙar fata da buzuwa ba.
Da kyar ya iya raba jikinsa da ita, ya ɗan yafa mata zaninta, ya gyara mata kwanciyarta, ya durƙusa ya sumbace ta, ya ci gaba da kallonta, daga bisani ya tashi da kyar ya fice ya bar ɗakin.
Ko da Nana ta farka ta sha mamakin yadda ta ga jikinta, ita dai ta san ta yi mafarkin tana tare da Sayyid, amma da ta farka ta ga alamun kamar an taɓa ta.
Ga shi a iya saninta ninkin kaya take yi, amma ta farka ta ganta rabin tsirara, ta yi tunanin ko Ƙaisar ne, amma cikin hanzari ta kawar da wannan tunanin daga ranta da take jin tamkar saɓo ta aikata, dan ta san Ƙaisar bai taɓa yi mata yawo da hankali a abu makamancin wannan ba.
Ta yi iya ƙoƙarinta ta kawar da tunanin komai daga ranta, ta shiga banɗaki ta yi wanka, ta yi alwala ta dawo ta yi sallar asuba tana ta istigfari saboda yadda ta makara.
Gari yana yin haske, ya shirya ya tafi gidan Mahmoudu, duk da yadda jikinsa yake a mace.
Kallo É—aya Mahmoudu ya yi masa, ya gane a rikice uban gidan nasa yake.
"Mahmoudu, wallahi na gane ta, na tuna ta Nana ce matata ce, to amma yaya aka yi komai ya shafe a cikin kaina na manta da ita?"
Mahmoudu ya ce "Ka nutsu ka kwantar da hankalinka, yanzu aiki ne ya ganmu jawur, sai dai ba wannan ba dole mu tsananta bincike a kan abubuwan da suke faruwa da kai."
"Ni kaina abubuwan sun ɗaure mini kai Mahmoudu, ji na nake yi wani iri, kamar an ƙwance wani nannauyan dutse daga kaina. Yanzu ta ina zamu fara, ni fa duk abin da za a yi ko Agadez za ta tashi, ba zan rabu da matata ba"
Mahmoudu ya ce "Ban gane Agdez ta tashi ba, a'a gaskiya sai dai ku ku tashi kai da ita"
Hammad ya ce "Mahmoudu ka daina wasa mana"
"Na daina wasa shugabana, amma yanzu ka tuna su Sule?"
"Na tuna shi, yanzu ina iya tuna komai fa a cikin ƙwaƙwalwata."
"To ma sha Allah, albishirinka"
"Mene ne?"
"Wallahi sai ka saya, ba zan faÉ—a a sadaka ba"
"FaÉ—i ko me ka ke so, wallahi zan baka"
Mahmoudu ya yi murmushi ya ce "Zan yi tunanin me nake so, amm yanzu yi sujudar godiya ga Allah tukuna"
"Zan yi amma fara gaya mini"
"Ta tabatta yaron nan, ɗan Nana ne, kuma a bincikena, da Gimbiya ta zo Niger, a hannun Ummana ta sauka. Al-Husssain ya turo mini komai nata, kamar yadda ka sanya shi bincike. A zahirin gaskiya da naje Maraɗi na gano yaron nan a gurin Ummana, shiyasa na damu da matsa bincike. Na kira Umma mun yi magana ta tabattar mini da ɗan Nana ne, kuma ɗanka ne yana daga dalilin da ya sanya ta turo ta Maraɗi aiki gidan cin abincinku, kuma ta ƙarfafeta ta taho Agadez ɗin"
A rikice ya damƙi hannayen Mahmoudu a gigice ya ce "Dan Allah da gaske ɗana ne? Ina da ɗa? Mahmoudu? Mahmoudu dama zan haihu zan ga ɗana a Duniya. Subhanallahi wa bi hamdihi subhanallahil Azim. Allahumma lakal hamdu wa laka shukur. Mahmoudu dan Allah da gaske ka ke?"
Cikin tausayawa Hammad, mussaman sanin irin ƙalubalen da ya fuskanta na rashin haihuwa da jarabtar da Allah ya yi masa na son 'ya'ya, aka hana shi ƙara aure, kuma Tafawa ya din ga ƙalubalantarsa da hakan yana nemana a sauke shi.
Mahmoudu ya dube shi ya ce "Nutsu ka kwantar da hankalinka, ka san ka na da matsalar zuciya kar ciwonka ya tashi, amma ka san ba zan yi maka ƙarya da abin da ka daɗe kana nema ba. Ina da tabbaci a kan abin da na gaya maka, dan sai da na gama bincike na tabattar sannan na gaya maka.
Hammad ya saki Mahmoudu, ya yi sujuda yana yi wa Allah godiya, sannan ya tashi fuskarsa sharkaf da hawaye ya ce "Yanzu mene ne abin yi? Ko ka zo mu je ka yi mata bayani, ban yi burus da ita ina sane ba"
"A'a kar mu kuskura mu sanar mata komai yanzu, sai mun gama daidaita komai da shirya yadda zamu tunkari jama'ar Agadez da wannan babban al'amari"
Ya share hawayensa ya ce "To tashi mu je MaraÉ—i na ga yarona"
"Mu bari sai gobe in Allah ya kaimu"
Hammad ya ce "Ba zan iya jira ba, kuma kar wani abu ya same shi, dole na dawo da shi kusa da ni, ko na ajiye su a wani guri keɓantacce, idan yana hannuna sai ta fi tsayawa ta saurare ni. Na san halinta akwai sauƙin kai amma akwai kafiya ba za ta saurare ni ta daɗin rai ba"
Mahmoudu ya yi murmushi ya ce "To shikenan, amma ka jira kaÉ—an Sule ya zo, ku gaisa sai mu je MaraÉ—in tare da shi"
Haka kuwa aka yi, ba a jima ba Sule ya shigo, ya risuna yana kwasar gaisuwa gurin Hammad. Ya rungume Sule tare da yi masa godiya, a kan É—awainiya da kuma gudunmuwar da suka ba shi a lokacin yana Nigeria.
Suka shirya suka tafi MaraÉ—i gidan Nene, ko da Hammad ya ga Muhsin, ya kasa zaune ya kasa tsaye, ya rungume shi yana kuka, da gode wa Allah da ya sanya yana da rabon haihuwa a Duniya.
Duk da sun kai ruwa rana da Nene, ta ce ba zata ba su Muhsin ba, dan ba su yi haka da Nana ba. Hammad ya ce ba É—aukar Muhsin zai yi ba yana son ya nesanta su da gurin da suke na É—an wani lokaci, kamar yadda Hammad ma ya yi tunani haka ita ma Nene ta tabattar masa da muddin ya jewa Nana kai tsaye babu abin da zai hana Nana zuwa ta É—auki Muhsin ta gudu, dan ta san halinta dole ya bi komai a hankali.

A hankali Hammad ya É—ago Nana daga jikinsa ya ce "Asmy bacci ki ka yi?".

"Idona biyu" Ta ba shi amsa.

"Kin yi shiru, Asmy ba da gangan na ganki na ƙi kula ki ba, kin san muddin ina cikin hayyacina babu yadda za a yi na share ki. A lokacin ina ta shirye-shiryen yadda zamu ɓullowa lamarin, Tafawa kuma ya sanya ni a gaba da da haƙilon ba zan yi mulki ba, ni juya ne, ga rashin lafiya ga hauka ga babu zobe. Ya daɗe yana jifana da kalmar juya, abin yana yi mini zafi da ciwo shiyasa na fallasa komai a lokacin da shirin duk abin da zai faru ya faru."

Nana ta yi ajiyar zuciya ta ce "Yakamata mu tashi, an kira sallar Asuba".

Hammad ya ce "Haka ne, amma ba ki ce komai ba" Ta ce "Zan ce ne, ina jin bacci ne sosai ka ga kwana muka yi ba mu yi bacci ba" Ya ce haka ne. Suka tashi suka koma ɗakin nan zai rufe amma ya tsaya ganin Nana na ƙara kallon ɗakin.
Ya ce "Wannan ɗakin tun zamanin Sultan Azhar yake, duk Sultan ɗin da ya zo a nan ɗakin ne turakarsa. Kowane zamani akwai canji da kuma yadda ake ƙawata ɗakin. Kafin daga bisani a daina amfani da gidan gaba ɗaya."

Nana ta jinjina kai ta ce "Ni yanzu abu ɗaya nake son ka gaya mini, ina da ciki ko ba ni da shi?" Ta yi maganar a ɗan shagwaɓa tana marairaice fuska. Ya yi murmushi ya ce "A cikin labarin kin ji inda wani abu ya faru ne?"

"Eh mana, tun da kana zuwar mini É—aki ba tare da sanina ba"

Ya jinjina kai ya ce "Sosai kuwa, dan tun da na gano ke matata ce, kusan kullum tare muke kwana, ya yi maganar yana rufe ɗakin. Ya damƙi hannunta suka yi gaba, ja ta yi ta tsaya tayi shiru sannan ta ce "Sayyid ba ka nuna mini mene ne a cikin ɗakin can ba" Ya kalli ɗakin ya ce "Hanyar tsohuwar prison ce, inda daga baya ake aikin sarrafa gold a ciki, amma yanzu babu abin da ake yi da gurin"

"Ina son ganin mene ne a ciki" Ya ce "To shikenan" Ya ja hannunta zuwa ƙofar gurin, amma suka tarar da ƙaton kwaɗo a jikin ƙofar. Ya ce "To ai gurin a rufe yake ma"

"Ya aka yi sauran ƙofofin ba a saka mukulli ba sai wannan? A tambayi mai tsaron gidan ya buɗe mini zan gani"

Hammad ya ce "To ai lokacin salla ya yi"

Ta ce "Na sani gani kawai zan yi mu tafi"

Ya tsaya yana kallon Nana da rikicin tsiya, ya ce "Zo mu je sai mu yi wa mai gadin magana, ya zo ya buÉ—e mana" ta bi shi a hankali jikinta cike da kasala ga kuma bacci da take ji.
Chapter 48 · 0% Book details