← Book details Buzu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 82

Sashe 51

Buzu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata Nurse ce ta yi sallama, suka gaisa da su Shukura, ta yi wa Shukura allurai. Wata ce ta sake shigowa da sauri, ta kalli Shukura ta ce "Ke ce Shukura ko?"
Ta jinjina kai.
"Wasu mutane ne suka zo, wai 'yar uwassu ce ke dubiya suka zo, amma yanayinsu kamar marasa gaskiya, mun ce babu mai wannan sunan, saboda mun san case É—inki, amma ga shi can ana ta faÉ—a da su sun ce sai sun caje Asibitin nan, 'yar uwassu ce ke dole su ganki"
Tsoro ne ya bayyana ƙarara a fuskar Shukura.
Nurse É—in ta ce "Ki kwantar da hankalinki, ai an kore su ma, kar ki damu" Bayan sun fita a rikice ta kalli Yusra ta ce "Ina ga wanda suka sace ni ne suka biyo ni nan, dan Allah ki tashi mu tafi "

Yusra ta ce "Ai da tuni mun tafi ki ka dage, yanzu bamu san suwaye ba, idan muka fita ai sai a samu matsala. Dole mu jira zuwa anjima sannan mu saci jiki mu gudu."
Da ƙyar Shukura ta amince sai dai da aka jima suna tsaka da shirin guduwa, suka ji muryar mutanen a waje, Shukura ta rikice, Yusra ta yi dabarar janta su ɓuya.

*****

Bin su da kallo Nana take yi , Asal ta ƙaraso gaban Nana cikin huci da zafin rai, tana kallonta kamar ta kai mata duka.
"Munafuka, muguwa, na jawo ki jikina ashe haɗa baki aka yi da ke a cuce ni? Kin auri mijina kin haihu da shi ban sani ba, kuma da yake ke munafuka ce, ba ki taɓa gaya mini saboda ba kya tsoron Allah. Wallahi idan ba ki rabu da shi ba, sai na kashe ki, na kashe ɗan naki dole ki koma inda ki ka fito a yau ba sai gobe ba, 'yar matsaiyata ƙasƙantacciyar halitta"

Nana ta dubi Asal ta ce "Subhanallah, ai Allah kaɗai ya san ƙasƙantaciyar halitta ba ke abar halitta ba. Kuma ɗan ja da baya, numfashinki yana takura mini a fuskata, sai na baki amsar maganganun"

Asal ta rikice ta kalli Gimbiya Bilkisu ta kalli Nana, ita kanta Gimbiya ganin Nana da ta yi ta ɗauka sokuwa ce ba ta magana. Nana ba ta jira me za su yanke ba ta matsa daga gaban Asal ta ce "Wannan abubuwan da ki ke faɗa, duk ba ni za ki gaya wa ba, Sayyid za ki gaya wa domin igiyar aurena a hannunsa take. Sai ki ji amsar da zai baki. Kuma ni Allah ya bani haƙuri da na zauna ina kallonki da mijina ban nuna miki komai ba, na biki a yadda ki ke so zuwa lokacin da ya dawo hayyacinsa ya gane ni.
Dan haka yanzu da ki ka san komai, ni ba baiwarki ba ce, kuma ba kukun mijinki ba ce, matarsa ce wato kishiyarki"

Asal cikin ƙaraji ta hankaɗa Nana ta ce "Wallahi na fi ƙarfin na yi kishi da ke 'yar matsiyata ƙazama, baƙa mummuna. Wallahi sai na kashe ki na kashe abin da ki ka haifa." Gimbiya Bilkisu na ƙoƙarin riƙe ta, amma sai fizge-fizge take yi tana ihu.

"To Bismillah Asal, ki kashe ni idan har hakan zai sanya ki huce. Ba za ki taɓa canzawa tuwo suna ba, Hammad mijina ne, wanda na fiki ƙaunarsa"

"Ke ya ishe ki malama, dan kin ga na yi shiru saboda ba ki da kunya da mutunci sai ki tsaya kina gaya mata maganganun banza? To bari ki ji na gaya miki, sai kin bar gidan nan a yau ba sai gobe ba. Sai kin bar gidan nan buzayen jinin sarauta ba sa raɓar talaka, balle su aure su su rayu da su. Sai kin bar gidan a wulaƙance cikin ƙasƙanci kuma sai an hukunta Hammad kan laifn da ya aikata"

Nana ta ƙare wa Gimbiya Bilkisu kallo ta ce "Haba Mama, ke da ba da ke nake kishin ba? Nifa kamata ya yi a sara mini akan haƙurin da na yi. Kuma ko ba komai, dole sunan 'yar matsiyata ya shiga kundin tarihin Agadez, mace ta farko da ta karya tarihi bayan ɗaruruwan shekaru. Ku daina zagina dan ban yi muku komai ba, abin da na sani kawai na fi Asal son Hammad har Duniya ta naɗe, haka zalika ba ni da tsara a zuciyarsa ki yi haƙuri"

"Ƙarya ki ke yi, yadda na yi amfani da kuɗi na mallake ki ta ƙarfin tsiya, haka zan yi amfani da su na yi maganinki mummunan a bar ƙyanƙyami"

Nana ta ji zafin maganganun Asal, amma ta yi murmushi ta ce "Ke kin ga alamar muni a tare da ni, kalli da kyau Gimbiya Asal. Kodayake ba wannan ba ma; kar ki manta kina magana da matar da ki kai gidan da ki ke kwana kina shaye-shaye da kaɗe-kaɗe da ƙawaye a lokacin da ba ta san halin da mijinta yake ciki ba, kar kuma ki manta matar da ki ke bawa magani ta zuba a shayin Imam Hammad, haka zalika matar da ta san kina ajiye masa takarda mai hoton ƙwarangwal da yake ci da wuta, wanda shi ne yake burkita masa hankali da lafiyar jiki; wannan matar ita ce matar mijinki kuma baƙa mummunar da ki ke ta kushewa ki ke iƙirarin kashewa"

Dummm ƙirjin Asal ya buga da ƙarfi, ta ƙwalalo ido tana kallon Nana.

Nana ta ci gaba da cewa "Ni ba karabutin mutanen da ki ka saba wulaƙanwatawa ba ne, kasancewar Hammad mijina ya sanya na bar idanuna a buɗe ta kowace kusurwa a kansa, tunda na haihu da shi, har abada ba zan bari wani abu mummuna ya same shi ba"

Asal ta tattaro jarumta ta yi murmushin ƙarfin hali, bayan da mararata ta cika taf da uban fitsarin tsoro.

"Ƙarya ki ke yi, ba ki da abin da za ki kawo ƙarshena a masarautar Agadez, saboda ba ki za hujja a kan wannan soki burutsun da ki ke yi" Ta yi maganar tana tsare Nana da ido.
Nana ta ce "Kwantar da hankalinki, ba na buƙatar wata hujja ko wani abu, dan har gaban Abada ba zan taɓa tona miki asiri ba. Ai Hammad yana sonki kuma ko ba komai 'yar uwassa ce ke, dan haka ki kwantar da hankalinki, amma daga yau da rana mai kamar irin ta yau, muddin ina tare da Hammad da ke da duk wani abu da yake kawowa rayuwarsa wani tarnaƙi"

Gimbiya Bilkisu ba ta bari Asal ta sake magana ba, ta kama hannunta suka yi waje.
Nana ta ja numfashi tana bin bayansu da kallo, kafin tsunduma tunani.
Gimbiya Bilkisu ta kalli Asal ta ce "Ke, kina wani wawanci har ki ka bari ta san kina wannan abubuwan? Asal kina da hankali kuwa?"

Cikin kuka ta ce "Ammi yaya zan yi, wallahi ban san da wata alaƙa a tsakaninsu ba, ban sani ba. Kuma ban san za ta kawo wani abu ba. Na shiga uku ba zan iya rayuwa babu Hammad ba wallahi Ammi ina son mijina, kuma ba zan iya buɗe ido na gan shi da wata ba ki taimake ni"
"Nutsu ki kwantar da hankalinki, bari na yi wa babanki magana a san abin yi a yau ba sai gobe ba, dole a san yadda za a yi da yarinyar nan ki daina kuka" Da kyar ta din ga rarrashin Asal.

Nana na zaune na zaman jiran dawowar Hammad,furucin Asal ya tsorata ta, ta fuskanci da gaske kowa na iya aikata duk abin da yake so, a wannan gidan domin cimma burinsa.
Ita ba ta kanta take yi ba, ta ɗan jaririn ɗanta da ba ta san inda yake ba ta shi take yi. Ta ƙudurce a ranta, idan Hammad ya dawo, bori za ta yi masa sai ya fitar da ita daga gidansa komai zai faru, amma ƙasan zuciyarta yana ta azalzalarta a kan son a buɗe wannan dakin na gidan tarihin.
Bayan azahar ya shigo, sai dai yanayinsa ya nuna mata a cikin damuwa yake.
Ya nemi guri ya kwantar da kansa a kan cinyarta. Nana ta shafa kan a hankali ta ce "Lafiya kuwa?" Ya jinjina mata kai kawai.
"Ka ci abinci ne?"
"Na ci" ya amsa a hankali.
"To meyafaru?"
Ya ce "Babu komai"

Nana ta numfasa ta ce "To dan Allah ina son ka dawo mini da Muhsin, kuma nifa na damu na koma gida, Sayyid hankalina a tashe yake wallahi, na san iyayena sun gaji da nema na"
"Asmy kar ki ƙara mini damuwa dan Allah, ina sane da komai, a tsare nake yin komai in sha Allah zai wuce"
Cikin damuwa ta ce "Zai wuce yaushe? Shekera ta uku nake shirin yi a ƙasar nan, nima ina da ahali bai kamata na tare a nan ba" Ya tashi zaune cikin damuwa, ya kalle ta zai yi magana, amma bai yi ba ya ciro wayarsa da take vibrating"
Da to kawai ya amsa ya tashi ya fita. Nana ta koma ta nemi guri ta zauna cikin damuwa.
Da sallama ya shiga ɗakin, ya tarar da Asal ga Sultan, ga Matawalle ga Tafawa da Sardauna sai Gimbiya Bilkisu da take ta ƙoƙarin rarrashin Asal. Gefe ga Imam Asadullahi ga kuma Imam Zahradeen rungume da Muhsin. Asal ji take kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu ganin Muhsin, dan babu abin da ya banbanta shi da Hammad.
Yayi mamakin yaushe aka yi masa wannan gangamin har haka? Bayan bai jima da barin gidan Imam Zahradeen ba ya tsaya a gurin Mahmoudu.
Sardauna ya ce "Ka je ka zo da babar yaron nan" Babu kara ya karɓi ɗansa a hannun Yayansa Imam Zahradeen, ya tafi inda Nana take. Ya kai mintuna sha biyar, sannan suka dawo tare. Nana suka yi ido huɗu da Asal da idonta ya kumbura, Nana ta sakar mata murmushi ta kawar da kanta gefe. Guri ya tsit sai Muhsin da yake ta hawa jikin Nana yana yi mata surutunsa na yara.

Zahradeen ya ce "Imam Muhsin, ka yi shiru"

Sardauna ya yi murmushi ya ce "Har ya zama Imam shi ma?"

Zahradeen ya ce "Eh mana Allah ya taimake ka. ÆŠan Imam ai Imam ne" Suka yi murmushi.

Tafawa ya ce "Yakamata mu yi abin da ya tara mu, ba tare da ɓata lokaci ba."
Chapter 51 · 0% Book details