← Book details Buzu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 82

Sashe 23

Buzu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwanakin Nana uku tare da Hammad, jikinsa ya yi ƙalau abin sa, sai dai magana ce babu. Nana ta yi iya ƙoƙarinta gurin tana kauce wa duk wani abu da zai sanya faruwar wata mu'amala tsakaninsu. A ƙasa suke kwana, ba ta taɓa kwanciya sai ya yi bacci, sai dai wasu lokutan ta ji ya ƙanƙameta idan ciwon ya motsa
Sai dai tun da ya warware sosai, take ganin kamar ya canza mata, wani irin kwarjini yake yi mata yanzu, mussaman idan ya saka ta a gaba da kallo duk sai ta rikice. Ta kasa gane take-taken sa. Sai dai ta riƙi karatun Alkur'ani sosai da sosai. Sai dai tun wannan ganin na ƙarshe da ta yi wa Ƙaisar, ba ta sake ganinsa ba, ko a farke ko a cikin bacci ba. Duk ta damu shi ma ta na son sanin halin da yake ciki. Ga shi gaba ɗaya ta rikice, a kwana ɗayan da ta ga jinin nan, ba ta iya tantance wane jinin ta yi ba. Ɓari ko na haila.
Tuni aka ƙara ƙawata ɗakin da kayan alatu, da kayan wanka da shafe-shafe na Imam Hammad, da duk wani abu da za su buƙata.
Yana banɗaki yana wanka, ta gama cika cikinta da kayan marmari, dan ba ta fiye cin abincin da Mahmoudu yake kawowa ba, fruit take samu ta ci ta ƙoshi ta ci nama. Sai da ta fara tsorata kanta da tunanin anya ba cikin ne da gaske ba. Ta yi zurfi sosai da sosai a cikin tunani. Razana ta yi jin yadda ba ta ji alamun fitowarsa daga banɗakin ba, sai ji ta yi ya zagaya hannayensa a cikinta. Duk da ɗakin ƙato ne sosai da sosai amma duk ƙanƙantar motsi tana iya jinsa, amma sam ba ta ji motsinsa ba.
Tsigar jikinta ta hau tashi, ta ji jikinta ya fara tsuma, tana neman ta rasa nutsuwarta.
Ya ɗan yi murmushi ya cika ta, ya nuna mata gadon da yake ɗakin, alamar ta hau ta kwanta. Amma ta yi mursisi ta ƙame a gurin. Ya kama hannunta zai ja ta, amma ta ƙwace hannunta ta ja ta tsaya. Sai ya rabu da ita, yaje ya haye gadon ya kwanta.
Ta tsaya a gurin tana rarraba ido, sai da ta ga ya jima da hawa gadon, ta lallaɓa ta ɗauki fulo ta ajiye a ƙasa ta kwanta.
Kwanciyarta ke da wuya, ta fara jin sukuwar wasu halittu da ba ta san ko na mene ne ba, a cikin ɗakin. Hayaniyar  halittum ya ci gaba da yin amsa kuwwa a cikin kunnuwanta tamkar a filin yaƙi. Wani mutum ta gani ya shigo ta wata ƙofa, ba a iya tantance jinsinsa, ya rufe ko ina na jikinsa, yana shigowa ya nufi gadon da Sayyid yake kwance, ya ajiye wannan takardar, ya nufi wata ƙofa. Da azama Nana ta bi bayansa duk da yadda yake wani irin gudu kamar iska na kaɗa shi. Sai dai wannan sautin ƙarar ya hana ta ci gaba da bin sa.
Rungume ta ya yi a jikinsa, jikinta na ta rawa, duk ta toshe kunnenta da hannayenta biyu. Saboda yadda take jin hayaniyar kamar zata tarwatsa mata kai. Ta ɗaga kai ta kalli Sayyid, ta kalli ƙofar ta ce "Akwai wani abu a nan?" Ya ɗan yi shiru, sai kuma ya yi gaba, ya buɗe ƙofar. Ya riƙo hannunta suka ratsa hanyar da take baƙiƙirin mai ɗauke da duhu, kai ba ka ce a cikin wannan katafaren ɗakin mai ɗauke da hasken fitilu hanyar take ba. Babu tsammanni ta ga sun ɓullo wani guri kamar corridor.
ShimfaÉ—aÉ—É—en yashin sahara ne a gurin, gurin ya bayar da wani ni'imtaccen sanyi, ga tsilla-tsillar bishiyu da suke a bushe a gurin hasken farin wata ya haske saharar. Ta waiwaya É—aya gefen, ta hango wani irin gini, mai kama da tsaunin dutse, hasken wuta na ci na tashi ta wata kafa mai kama da taga a jikin ginin Dutsen.
Bakinta na rawa ta kalle shi ta ce "Sayyid na san gurin nan, tun kafin na sanka nake mafarkin saharar nan, har na zo na sanka, ina mafarkinka a cikin saharar nan. Kuma a nan nake yawan ganin ka tare da Giyaz. A waccan bishiyar ku ke zama da su Habu ku sha shayi da wasu mutane ma da ban san su ba.
Ina ne nan, kuma meyasa abubuwan da nake gani a bacci suke dawo mini a zahiri, haryanzu ina da ayoyin tambaya da dama a kanka"

"Yanzu kin yarda da nake gaya miki ruhinmu a haÉ—e yake? ÆŠaya ba zai iya rayuwa babu É—aya ba"

"Ba wannan nake son ji ba, haryanzu akwai wasu abubuwa ɓoyayyu da ban gama fahimta game da kai ba"

"Komai zai warware a hankali, za ki fuskanci komai rayuwata, amma ba na nufin cutar da ke ta kowace fuska, amma sannu a hankali za ki fahimci abin da ki ke kokwanto a kai."

Ta buɗe idanunta tana ƙarasa jin sautin muryarsa a cikin kunnuwanta. A kan gadon ta gansu tare, fuskarsa na kallon ta ta, yana ta yi mata numfashi a fuska a hankali, wanda hakan ya ƙara dagula mata lissafi dan kuwa ita ta san a zahiri abin ya faru, amma ya rikiɗe ya juye ya koma kamar mafarki. Ga shi yanzu Ƙaisar ba cikakkiyar lafiya ce da shi ba, balle ta ce ko shi ne yake wujijjigata, hakan ya ƙara hargitsa mata tunaninta.
Ta  tsura masa ido, kamar a fuskarsa za ta gano gaskiyar abin da take fata.

"Meyafaru?" Sautin muryarsa ya doki dodon kunnuwanta.
Ba ta ce masa komai ba, ta zame jikinta ta juya masa baya, tana ta tufka da warwara a zuciyarta. Sake matsawa ya yi kusa da ita, sai dai wannan karon bai yi magana ba, sai dai jin manufarsa, ya sanya ta zabura da sauri tana ƙanƙame jikinta.

AREWABOOKS

Ƙanƙance idanun ya yi, kasancewar fitilar ɗakin a kunne take, ya din ga bin Nana da kallo, yadda ta tsuke fuska ta sanya hannayenta tana kare jikinta.

"Nana" Ya kira sunanta kamar yadda ake kiranta. Sai ta ji wani iri gaba É—aya babu daÉ—i, ta kalle shi a tsorace.

"Me yasa?" Ya furta a hankali. Ba ta ce komai ba ta sunkuyar da kanta, tana ƙoƙarin matsawa kaɗan.

"Matata ce fa ke? Da gaske kin daina so na ko?"

Ta ce "Ko ina sonka, ba zai yi mini wani amfani ba. Kuma a da ne nake da cikakken 'yanci a matsayin matarka, a Duniyar da nikaÉ—ai ka ke kallo. Wannan duniyar kuma ka yi mini nisa, a yanzu ma na san da na gama amfani za a sallame ni, sake yadda da kai shi ne ganganci mafi muni da zan sake aikatawa"

Ya ɗan fesar da wata iska daga bakinsa ya ce "Ki yi mini alfarma ki bani dama, na san tun da ki ka yadda ki ka sake dawowa kina so na, idan ba kya so na ba za ki yarda ki sake zuwa inda nake ba." Ya riƙo hannunta yana murzawa a hankali ya ce "Ba kya yi mini kwatankwacin son da nake yi miki. Kar ki hukunata ni da abubuwan da ki ke gani a zahiri kawai"

A ɗan ƙufule ta ce "Ka ke son dai wadda ka ke so, ga matar so can kana da ita, wadda al'adarku ta amince ka so ka zauna da ita. Ai ni ina ga sai dai a saka ni a cikin bayi saboda baƙi da muni" Ta ƙarasa maganar tana tashi zaune. Shi ma tashi zaunen ya yi ya ce "A'a ai ni ban faɗi haka ba, ina da farar amma, nake ta bin ki ina lallaɓa ki. Dan Allah ni dai ki yi haƙuri, daga ni har ke mun yi kawar juna, wallahi ba ƙaramin kawaici nake yi ba kasancewata da ke a guri ɗaya" Baki buɗe take bin sa da kallon mamaki da rashin sanin abin yi.

Cike da son tura masa takaici ta ce "Idan ba ka ce ba, amma ai a gabanka ta bautar da ni, ta wulaƙanta ni. Ba ƙaramin tozarta na yi ba da abubuwan da matarka ta yi mini ba. Ka je gurin halattacciyar matarka, da ahalinka suka san da zamanta, ba ni matar ɓoye ba"

Ya ce "Haka ki ka ce?"

"Eh" ta furta cikin tsiwa. Ya zuba mata ido yana kallonta, shi wani irin kyau mata ƙara masa, zuciyarsa har wani harbawa take yi da sauri kasancewarta a kusa da shi. Shi kansa ba zai iya cewa ga adadin abin da yake ji a kanta ba.

A ransa ya ce "Ba komai ki yi yadda ki ke so, kin cancanta" A zahiri kuma sai ya sauka daga kan gadon, ya nufi hanyar fita.

A É—an ruÉ—e ta sauka daga kan gadon ita ma tana faÉ—in "Ina zaka je?"
Bai yi magana ba ya ci gaba da tafiya, bayansa ta biyo da sauri tana faÉ—in "Sayyid ba ka da cikakkiyar lafiya fa, ina za ka je?"

Ya rufa ta a cikin ɗakin, ya tafi. Ta jijjiga ƙofar amma ta ji ƙofar a rufe. Ta koma ta nemi guri ta zauna jikinta a sanyaye tana tunanin, kar wani abin ya same shi.

*****

Tun da É—an da ke cikin Shukura ya faÉ—o Duniya, ta fara ganin duhu, saboda wani irin bleeding da ta din ga yi. Matar da ta kawo ta Asibiti, gaba É—aya a ruÉ—e take, saboda tun da ta haÉ—u da ita ba ta yi magana ba. Ga shi ta kawo ta Asibiti har ta haihu ba ta yi magana ba.
Likitan ya ba ta shawarar ta kira jami'an tsaro ta sanar musu, saboda kar a je wani abu ya faru da ita.

*****
Doctor Sharif kuwa tun da ya farfaɗo ya tashi da shanyewar ɓarin jiki, saboda tashin hankalin yadda ya ci karo da gawar 'yarsa cike da tozarci.
Duk da maganarsa ba ta fita sosai, amma ƙoƙari yake yi ya tambayi ina matarsa, ya jikinta. Amma aka ce masa tana samun sauƙi, sai dai abin da bai sani ba shi ne, bayan tafiyarsa gurin 'yan sanda Allah ya yi mata cikawa.

*****
Chapter 23 · 0% Book details