← Book details Buzu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 82

Sashe 34

Buzu Part 3 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Cikin kuka Sultan Jalaludeen ya ce "Yaya za a yi ina cikin jimami da alhinin rashin mahaifina, amma ku ta naɗin sarauta ku ke yi, ni ba zan iya karɓar wannan kayan ba"

"Dole ka karɓa, ya kai Sultan Jalaludeen Ansar, wannan wasiyyar mahaifinka ce, da ya nemi muddin mu na numfashi a cika masa ita, tun kan a binne shi ya nemi a naɗa ka Sultan a Agadez. Ka zuba ido wayewar gari da an binne mahafinka, yaƙi zai nemi ya ɓarke a Agadez, abin da ba a son faruwarsa a zuriyarku. Dan haka muddin ka na son masaruta ta ci gaba da tsayawa da ƙafafuwanta dole ne ka yi haƙuri, sai dai a wayi gari da sabon Sultan."
Haka su ka din ga tausar sa, da ba shi baki har ya yi haƙuri. Sannan suka ba shi wata ƙaramar jakar fata, wadda ta ɗara laya girma, amma ba ta kai girman a kirata jaka ba. Suka sanar masa tun Sultan yana raye, ya sanya bokansa ya yi masa ita, domin tsari da kariya daga miyagu. Kuma a matsayinsa na Sultan, zai iya amfani da ita, gurin sarrafa aljanun gidan Sarauta. Can gidansa kuwa tuni har an kame wasu daga cikin 'ya'yansa, ana ta nemansa ruwa a jallo, an tattare matansa an kame. Sai dai ko sama ko ƙasa aka neme shi a ka rasa. Washegari da sassafe tun kan a binne mahaifinsa aka wayi gari a kan ganshi an kan karagar Mulkin Agadez da duk wani abu da yake nuna shaidar shi ne Sultan a Agadez.

Ayshercool
08081012143

90
1K NE A BIYA KUÆŠIN KARATU KAFIN A KARANTA.
0069685771
Aisha Adam stanbic bank
08081012143
Mutane sun sha mamakin abin da ya faru. Babu wanda ya isa ya ce dan me? Aka kame waɗanda suka yi yinƙurin nemansa su kashe shi. A ka yi jana'izar Sultan Ansar. Gaba ɗaya Jalaludeen baya murna, saboda raɗaɗin mutuwar mahaifinsu, ga kuma wannan nauyi da ya hau kansa da ƙanan shekaru da ba su wuce Ashirin da takwas ba.
Sai dai duk zigar da Saifudden ya din ga yi wa Imam da 'yan uwansa, zamewa ya yi ya bar su, aka kama su sukaÉ—ai.
Mahaifiyar Jalaludeen ta yi masa nasiha sosai da sosai, a kan gudanar da sha'anin mulki.
Duk da ya san tarin ƙiyayyar da Saifudden yake yi masa, da wasu daga cikin 'yan uwansa, amma haka ya janyo su a jikinsa, ya basu sarautu domin ya rage musu raɗaɗin abin da suke ji, kuma ya ƙara musu zaman lafiya da fahimtar juna. Ya yi wa Saifudeen Tafawan Agadez, wanda yana cikin manyan 'yan majalisar Sultan, da suke faɗa a ji. Ya yi wa ɗan uwansa Turakin Agadez, ɗan wan babansa ya yi masa Sardaunan Agadez. Bayan mutuwar Matawallen Agadez ya naɗa ɗansa Matawallen Agadez. Ya saka aka saki Imam Imam ɗin da suka yi zamani tare da su, suka yi yinƙurin halaka shi, sai dai gaba ɗaya ya sauke su daga kan muƙamin ya kuma yi amfani da ƙarfin mulki gurin ƙwace duk zobunansu, ya ce daga lokacin duk wanda zai zama Imam sai ya tantance shi, kuma sai da sahalewar sa. Aka yo caaa a kansa kamar za a cinye shi, su na ganin zai canza musu tsarin Al'ada.
Duk gidajen da suke da gadon, suka bayar da wanda suka zaɓo. Hankalin Tafawa ya ƙara dugunzuma bayan da ya san cewa ba shi da makoma, ya san ba zai taɓa mulki a Agadez ba, haka 'ya'yansa, saboda rashin zoben, dan ya san Jalaludeen 'ya'yansa zai bawa.
Wata rana Sultan Jalaludeen ya aika aka kira masa ɗan uwansa, ya zo ya same shi ya dube shi ya ce "Ya kai ɗan uwana, na san kai ne gaba da ni,  kuma ka so ka yi mulkin Agadez sosai da sosai, amma Allah bai nufa ba, ina mai sanar da kai cewa zobe ɗaya da aka neme shi aka rasa ya ɓace a tsakanin zuriyarmu, yana nan bai ɓata ba. Dan haka zan damƙa shi a gare ka, ka duba wanda ya dace a cikin 'ya'yanka ka bawa. Wataƙila a bayana a iya samun wani ya yi mulki daga gidanka"

Cikin mamaki ya kalle shi ya ce "Amma yaya aka yi ka mallaki zoben da ake tunanin ya ɓace?"
Chapter 34 · 0% Book details