Sashe 52
Buzu Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Sardauna ya ce "Haka ne kam, Imam Hammad" Hammad ya ɗaga kai ya kalli Sardauna. "Duk da mun san aurenka da ita wannan 'yar Nigeria, ƙaddara ne daga Allah, Amma ina fatan ka sanar da ita matar taka, sharaɗin ƙasar Agadez na rashin auren bare?".
Gaban Hammad ya faÉ—i, Nana kuma ta kalle shi suka yi ido huÉ—u.
Sardauna ya dubi Nana ya ce "Ina fatan ya yi miki bayani?"
Nana cikin girmamawa ta ce "Eh ranka ya daÉ—e. Ya yi mini na sani"
Sororo ya bi Nana da kallo.
Tafawa ya yi caraf da zancen, ganin ana neman a ɓata masa lokaci.
"Amm dama na nemi a yi wannan zaman ne, domin na san mene ne makomar 'yata, sannan wane hukunci za a É—auka a kan Hammad, bisa karya dokar Agadez"
Hammad ya numfasa ya ce "Ai ni ba ni da wata matsala da Asal, ban sake ta ban kuma yi wani abu da...
"Kai dalla rufe wa mutane baki, ai na san baka saketan ba, amma mene ne matsayinta? Zaka zauna da ita ne? Ka saki waccan yarinyar ko kuma mene ne?"
Hammad ya tsuke fuska ya yi shiru.
Matawalle ya ce "Amma mai girma Tafawa, bai kamata a je ga wannan maganar ba. Kana neman sanin matsayar Asal ne?"
Tafawa ya ce "Ka bari mu yi magana da shi ka daina saka mini baki"
Hammad ya ce "Makomar aurena da Asal, yana daga gare ta, idan tana son zama da ni, ba wani abu dama ni ban ce ba zan rayu da ita ba. Amma ina mai neman afuwarku ina shirye na É—auki duk wani hukunci da za ku yi mini, amma sau É—aya a rayuwata, nima ina neman ku yi mini alfarmar nan, ba zan iya sakin Nana ba, mussaman da rabo ya shiga tsakanina da ita. Ba zan iya sakinta ba".
Sak suka yi su na bin Hammad da kallo.
Sultan ya numfasa ya ce "Hammad, ba kai ka ke da ikon yanke wannan hukuncin ba, sai abin da muka yanke maka. Mai girma Tafawa muna mai baka haƙuri, Hammad ya tabattar da cewa aurensu yana nan daram, dan haka yakamata ta kwantar da hankalinta."
"Babu batun kwanciyar hankali a nan, sai zuwa yaushe zamu san matsayarta, yarinyata tana wuni ta kwana babu bacci. Kuma da haka ku ke shashantar da duk wani laifi da zai aikata ba tare da an hukunta shi ba. A wannan karon dole a bar doka ta yi aiki a kansa, kuma a zartar da duk wani hukunci da yakamata a kansa. Ya saki matar nan a yanzu ya bata É—anta ta tafi inda ta fito shi kuma a hukunta shi"
Hammad ya girgiza kai ya ce "Zan karɓi kowane irin hukunci, amma ba zan rama sharri da alkhairi ba"
Asal ta rushe da kuka tana rirriƙe Gimbiya Bilkisu.
95
1k ne via 0069685771
Aisha Adam stanbic
08081012143
Tafawa a fusace ya ce "Kun gani ko? Abin har ya kai raini ya shiga tsakaninmu ya faɗi duk abin da ya ga dama. Kamar yaya ba za ka rama sharri da alkhairi ba, waye ya yi maka sharrin waye ya yi maka alkhairin?. Ya yi wa dokokinmu karan tsaye. Kuma dolensa ya yi murabus a gaban majalissa, a ba wa wani tun da ga taka mana doka, ga kuma rashin zobensa sannan wannan ɗan da yake tutiya da shi, babu wanda yake da yaƙinin na halal ne tun da babu waliyyinsa ko ɗaya a lokacin da aka ɗaura auren."
"Zan jura komai amma ni ba mutumin banza ba ne ba, kuma kar ka sheganta mini ɗa, ban san da wace kalmar za a yi mana bayanin halin da na shiga har na auri Nana ka yarda ba. Tsawon shekaru ina yi muku biyayya, ko ina so ko ba na so, dokar Agadez ba dokar Allah ba ce ku bari na samu nutsuwar zuciya mana, idan ba so ku ke ku wayi gari ku ga na bar muku duniyar ba. Ta yaya zan yi wa Allah butulci akan abin da nake nema? Yarinyar da ta rayu da ni a lokaci mafi tsananin da babu wanda zai iya zama da ni ina hauka, na haɗu da larurar da hatta najasata ita take gyara mini da hannunta ba tare da ƙyama ta ba. Babu biyayya ga abokin halitta gurin saɓawa mahalicci, Asal na da zaɓin zama da ni ko ta ƙi na bata wannan damar, amma ba zan saki Nana ba ko zaku rataye ni"
Sultan ya miƙe tsaye a fusace ya ce "Hammad!"
Imam Zahradeen ya miƙe tsaye shi ma, ya dubi Sultan ya ce "Ya kai Abbanmu abin alfaharinmu, a duniya ba na tunanin ka taɓa son wani abu kamar yadda ka ke son Imam Hammad, kuma bana tunanin akwai wani wanda yake yi maka biyayyar da yake yi maka. Tun da ta kai shi ga yin sa in sa da ku, to tabbas ya kai bango. Amma ko sau ɗaya yakamata a ce mai girma Tafawa ya yi maka kara a kan Imam Hammad, amma duk lokacin da wani abu ya faru tsakaninsa da Asal, ƙarara yake goyon bayanta a turasasawa Hammad yin abu dan faranta mata, sau ɗaya ko dan saboda shi yakamata a yi wa dokar Agadez kwaskwarima.
Gimbiya Bilkisu ta ce "Zahradeen kana da hankali kuwa? Waye ya sanya da kai?"
"Ummi ki yi haƙuri, kina duba mafitar ɗan uwanki da 'yarsa, nima ta nawa ɗan uwan nake dubawa."
"Ni ka ke gaya wa haka Zahradeen?"
"Ina neman afuwarki, amma dan Allah kar ki yi mini mummunar fahimta Ummi."
A fusace Sardauna ya ce "Ya isa haka, ya isa, kun manta a gaban wa ku ke ne? Ya za a yi kowa ya din ga magana yadda ya ga dama, babu É—aa da girmamawa?" Kowa ya yi shiru.
Nana cikin ladabi ta ce "Ina mai neman afuwarku, na san wannan hatsaniyar ta faru ne duk a dalilina. Amma da na san wannan al'amari zai faru, ko haka dokar ƙasar nan take, ba zan yi gangancin auren Sayyid ba. 'yan uwansa ba su yi mini wannan bayanin ba. Haka zalika ban faɗi haka dan a ga laifinsu ba, kamar yadda suka gaya mini shi ya nemi a biya sadakina ya aure ni. Amma kamar yadda wannan shugaban ya faɗa" Ta yi maganar tana kallon Tafawa.
"Na amince zan ɗauki ɗana na koma Nigeria, idan ma kun ce ba ku da alaƙa da shi, na yarda zan zame masa uwa na zame masa uba.."
"Babu inda za ki je mini da É—a, kuma kema babu inda za ki je" Ya katse Nana yana maganar cikin É—aga murya.
Cikin kuka Nana ta ce "Sayyid babu abin da ya fi ahali daɗi da muhimmanci, sai da na baro nawa na fito nemanka na gane hakan, ni na baro nawa ahalin kai ga ka cikin gata, sun baibaye ka da soyayya da ƙauna. Dama gudun rasa ahalin ga Muhsin ne ya sanya na fito nemanka da tsohon cikinsa." Ta saka hannu a hijjabinta ta ciro zoben da ya bata ta ce "Wannan zoben ina kyautata zaton shi ne zoben da ake ta magana a kansa, tun mu na Nigeria Sayyid ya bani shi kyauta, domin jaddada soyayyarsa a gare ni. Muhsin kai wa Abbanka zobensa, kuma ina fatan ba za a ƙwace kujerarsa ta shugabanci ba, sanyin halinsa zai zamo ƙwarin gwiwa ga talakawan da ba su da ƙarfi. Na gode matuƙa da kulawa amma kar ku raba ni da ɗana dan Allah" Kuka Nana take yi sosai da sosai.
Imam Zahradeen ya dubi Nana ya ce "Ɗauki yaronki ki koma, za a neme ki" Nana ta durƙusa ta ɗauki Hammad da ya riƙe zoben da Nana ta ba shi yana zura wa a baki. Ta karɓi zoben za ta ajiyewa Hammad shi, amma ya haɗa ya karɓe Muhsin.
Asal kamar ta haÉ—iyi zuciya ta mutu haka take jin yadda a gaban mutane ya nuna wa duniya ita zai iya rabuwa da ita, Nana ce ba zai rabu da ita ba.