Sashe 36
Buzu Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Mahmoudu ya waro ido ya ce "Dan zatin Allah daga nan, kar ka kuma É—aga maganar nan, ka san dai illar hakan, da abin da zai haifar"
Ya gyaɗa kai ya ce "Ba ina nufin zan auri baƙar ba, amma ni dai su na yi mini kyau sosai da sosai. Da Umma ta yi maka ƙanwa sai na aura"
"Dan Allah ka daina wannan maganar, in dai a Agadez ne, mu ba komai ba ne face masu yi muku hidima"
Hammad ya ce "Babu aya babu hadisi a kan hakan, ina fatan wataran wannan dokar za ta kau, kowa ya auri wanda yake so, kowane kalar fata ya rayu cikin 'yanci ba tare da bauta ba. Har na koma ga Allah ina jin zafin abin da aka yi muku Mahmoudu. Kuma abin da ya faru da ku, yana daga dalilan da ya sanya nake matuƙar son baƙaƙen buzaye, da ma sauran baƙaƙen fata, duk farin nan namu fa, duk sunanmu 'yan Afrika kuma baƙaƙe to mene ne na ƙymar junan"
Mahmoudu ya ce "Ai komai ya wuce ma, dan Allah ka daina wannan maganar kar ma ka sake É—aga ta dan Allah"
Ya É—an yi shiru sannan ya ce "Na so a ce zan iya ce wa Abie ba zan auri yarinyar nan ba, amma ba zan iya ba"
"Dan Allah ko da wasa, kar ka gaya masa haka, ka yi haƙuri dan Allah. Kuma ni gara ka ce ba ka son ta, da dai ka yi waccan kataɓorar da ka faɗa da farko" Hamamd ya gyara kwanciyarsa, ya ce "Da wasa nake yi maka, kawai dai na gaya maka abin da yake raina ne. Fararen matan duk ba ga su nan ba, duk inda na kalla su ne ba. Amma ina son baƙa a ce matata ce, baƙa me kyau tubarkallah ka ga da ka na da ƙanwa, mai kama da Umma, na aure ta baƙaƙen mata su na yi mini kyau ma sha Allah"
"Dan zatin Allah ka daina zancen baƙar nan"
Yayi murmushi ganin yadda Mahmoudu da gaske baya son zancen, ya juya masa baya yana murmushi.
Asal ce zaune a gaban Tafawa, yana zaune daga kan kujera. Ya ce "Ki na ji na ko? Na ba wa É—an uwanki ke a matsayin matar da zai aura, Imam Hammad dan haka ki shirya a kowane lokaci za a iya É—aura muku aure".
Zabura Asal ta yi ta ce "Aure, kuma da Hammad?"
"Eh da shi, mene ne?" Ta sunkuyar da kai tana girgizawa cikin matsananciyar damuwa.
"Dan haka ki je zan sanar da mahaifiyarki a yi shiri"
Tana barin turakarsa ta saka kuka, ta shiga sashen mahaifiyarta. Cikin damuwa ta ce "Kyakykywata Lafiya kuwa?"
"Ammi, Abbu ne ya ce wai aure zai yi mini, dan Allah ban yi ƙarama da aure ba? Kuma wai Imam Hammad zai aura mini"
Ta tsuke fuska ta ce "Ban gane ba saboda me? Dama haka ake yi"
Asal ta ce "Dan Allah ni ki roƙe shi ya ƙyale ni, kar ya aura mini shi ba na son shi"
"Ki kwantar da hankalinki, babu wanda zai yi miki auren dole ina raye".
Mahaifiyar Asal ta tashi ta tafi turakar Tafawa, cikin takaici ta ce "Amma meyasa za ka yanke wannan hukuncin ba tare da amincewar yarinyar nan ba, ba ta ƙaunar auren nan fa"
"Saboda 'ya ta ce na isa da ita"
"Amma rayuwarta fa? Ta yaya za ta zauna da mutumin da ba ta so?"
"Ta zauna da shi koma ta yaya ne"
Asal ta din ga bori a kan ba ta son Hammad, ba za ta aure shi ba, dan sam ba ta shiryawa aure a lokacin ba, duk da tana da ƙarancin shekaru amma yadda take tsara wa kanta rayuwa sai ta ci Duniyarta da tsinke sannan za ta yi aure.
Can kuma Sultan ya saka Hammad a gaba a kan lalai ya je su gaisa da Asal, duk da sun san juna akwai buƙatar su ƙara samun shaƙuwa a kuma tsara yadda biki zai gudana. Da to kawai Hammad yake amsa wa Sultan.
Tare da Mahmoudu suka je gurin Asal, sai dai a ƙalla sun shafe awa ɗaya da rabi, Asal ba ta fito ba. Idan ya yi niyyar tafiya, sai Mahmoudu ya hana shi.
Daga ƙarshe shi kansa Mahmoudu gajiya ya yi, suka tafi gaba ɗaya.
Sai dai washegari, Sultan ya kira Hammad, ya ci masa mutunci abin da bai taɓa yi ba, wai girman kansa zai sanya ya lalata musu zumunci da ɗan uwansa. Yarinya ta gama shiri tana jiransa yana zuwa ya yi tafiyarsa. Abin ya yi wa Hammad ciwo, amma ya daure ya bawa Sultan haƙuri, ya tashi ya tafi. Sai da ya yi zuwa uku, sannan Asal ta zo. Kallo ɗaya ya yi mata ya tuna abin da Sultan ya yi masa saboda ita, ransa ya ƙara ɓaci ya ji wata irin tsanarta ta mamaye shi. Sam Asal ba ta da ɗa'a. Duk da kasancewarsa yaro ƙarami girman sarautarsa ya sanya yana da kamewa da son girma. Amma bai ga hakan a tattare da Asal ba, sai harare-harare da take yi. Ga shi a lokacin shi har cikin zuciyarsa yana son mace mai mamora, Asal kuwa ga yarinta ga babu alamar wani abin kirki a tattare da ita.
Haka Tafawa ya din ga haɗa shi da Sultan a kan Asal. Tafawa ya lura idan bai yi a hankali ba, Asal za ta jiƙa masa aiki, ga mahaifiyarta sai bala'i take yi ba za a yi wa 'yarta auren dole ba.
Ya same ta da daddare a ɗakinta, ya kifa mata wani uban mari, da sai da ta ga taurari ya ce "Ke kalle ni da kyau, idan ma babarki ce take ziga ki, to ki shiga hankalinki tun da wuri. Ban haɗa auren nan dan ki so ko kar ki so ba. Na haɗa auren nan ne domin cikar muradina. Za ki taimaka mini ne, ina son ɗan uwanki ya gaji karagar mulkin Sultan, dan ba zan bari sarauta ta dauwwama a gidansu ba. Dan haka dole ki haƙura da duk wani abu da ki ke so, domin cikar nawa muradin. Zan aura miki Hammad ne, na wani ɗan lokaci na samu cikar burina, daga nan ki yi duk abin da ki ka ga dama." Asal ta sha kuka sosai da sosai. Ita ta san Hammad ba shi da wata makusa ko kaɗan da za ta nuna a matsayin aibun da za ta ce ba ta son shi, kawai gani take auren kashe mata rayuwa ne. Mussaman yadda Allah ya yi mata kyakykywar halitta.
Ko da ta gaya wa mahaifiyarta abin da Tafawa ya ce, zuwa ta yi ta same shi, tana faɗan ya za a yi ita ba da haifar ɗa ba, a tursasa wa 'yarta saboda cikar muradin wani, tun da yana da ƙanne mata a aura wa Hammad ɗin ƙannen Asadullah.
Gudun kar ta ɓata masa aiki, ya sanya ya yi mata bayanin ai idan ya aura masa a ƙannen Asad, nan da nan za a gano shi, amma wanda suke ba ciki ɗaya ba, babu wanda zai kawo wani abu. Ya din ga kwaɗai mata abubuwan da za su samu idan Asad ya zama Sultan.
Gimbiya Bilkisu ma har gida ta zo ta samu Tafawa, ta ce "Na ji labarin za ka aura wa Hammad É—anka, duk da na san inda ka dosa, na san dalilinka na yin haka, amma kar ka manta da sauran rina a kaba, tun da Zahradeen ma Imam ne, kuma É—an Sultan"
Tafawa ya ce "Haba Gimbiya Bilkisu, ai ke 'yar uwata ce, ki zo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe mu yi nasarar ganin Hammad bai mulki Agadez ba. Kuma kema kanki kin san alamu sun nuna Hammad yake son ya damƙawa mulkin"
Ta ce "Mu haɗa hannu, ka yi mini irin yadda ka yi wa wadancan mutanen da suka haɗa kai da kai. Kuma idan na haɗa kai da kai, waye zai haƙura ya bar wa wani tsakanin Asadullah da Zahradeen iya ruwa fid da kai kawai" Ta ƙarasa maganar tana dariya.
Ta shiga gurin mahaifiyar Asal da niyyar su gaisa, amma ta ce mata "Ina fatan idanunki a buɗe suke,a kan auren nan da z a a yi wa 'yarki? Idan burinsa ya cika Asadullah ya zama Sultan Asal ba ta da wata makoma. Ita dai mace ce ba sarauta za ta yi ba. Ki bar ganin shi ya haife ta, buƙatarsa na biya zai ajiye ku gefe"
Haka aka din ga É—auki ba daÉ—i a kan auren nan, Hammad ya din ga fuskantar kalubale daga Sultan saboda yadda Tafawa yake haÉ—a su, har sai da Matawallen Agadez mahafin su Hasna da Al-Husssain ya ankarar da shi, Tafawa haÉ—a shi kawai yake yi da Hammad.