Sashe 62
Buzu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin mamaki Alhaji Fatuhu yake kallon Hajiya Sa'a, saboda yadda ta ƙure Muhsin da ido.
Ya ce "Yaya Sa'a, kin gane ni? Ko Muhsin ki ka gane?"
"Ba dole na gane wannan tsinannen yaron da Allah ya tsine wa albarka ba? In sha Allah sai ya mutu kuma kun rasa. Da shi ne ya mutu da Abbana bai mutu ba, É—an nawa guda É—aya na rasa shi, ku ga naku nan yana rayuwa "
Cikin rashin fahimta Alhaji Fatuhu ya ce "Yaya Sa'a kin san kuwa me ki ke cewa?"
Cikin tsawa ta ce "Na sani mana, na sani, ina sane. Yanzu ga Abba ya mutu a banza, ni kuma dodon ƙungiya ya shanye mini wasu sassan jikina."
Gaba ɗaya ya yi iya ƙoƙarinsa gurin ganin maganganun da take yi, ba su yi tasiri a zuciyarsa ba. Ya dubi Fadila da ta takure a gefe, tana zare ido ya ce "Fadila, kar fa ku damu ko ku ɗaga hankalinku, kun san ba a hayyacinta take ba, tana fama da matsalar taɓin hankali."
Hajiya Suwaiba ta ce "Duk da haka amma mutum ko ba shi da hankali, yana faÉ—ar abin da yake aikatawa ne, amma babu rami mai ya kawo rami?"
"Ƙaryata ni za ki yi kenan Suwaiba? Meye haɗin Yaya Sa'a da wani shan jini, kawai raɗaɗin mutuwar ɗanta ne yake damunta"
Fafur ya hana su magana, tare da kare Sa'a, duk da ƙasan zuciyarsa maganar Hajiya Suwaiba ta kama zuciyarsa, da ta ce babu yadda za a yi Hajiya Sa'a ta yi wannan maganganu idan bata da alaƙa da su.
*****
Imam Zahradeen ne zaune a gaban mahaifiyarsa Hajiya Bilkisu, cikin kuka take yi masa bala'i "Yanzu Zahradeen har zaka iya fifita bare a kaina mahaifiyarka, ka zaɓi ka tona mini asiri? Yanzu amfanin me hakan ya yi maka daga kai har ni. Duk fafutukar da na yi domin ka ne, amma a ƙarshe ka watsa mini ƙasa a idona. Ka lalata komai abin da nake harin ba zaka samu ba, saboda kai ne gwanin na iya da son burgewa, ka tona mana asiri ga shi kaima baka tsira ba"
"Ban yi duk abin da na yi, domin tozarta ki ba Ammi, duk abin da na yi, na aikata ne domin kaucewa faɗa wa fushin Ubangiji. Bawa bai taɓa isa ya yi wa bawa abin da Allah bai yi masa ba. Duk ƙoƙarin ku Ammi idan Allah bai ƙaddara mu hau karagar nan ba ba zamu hau ba. A yanzu hakan ku nawa ne ku ke fafutuka, ko da an kawar da Hammad, kuma ba zaku samu zaman lafiya da fahimtar juna ba, kowa na sa yake son ya hau. Ammi Hammad fa shikaɗai ne ɗan uwana namiji...
"Tashi ka bani guri, kafin baƙin ciki ya sanya na tsine maka, ka fita ka bani guri" Zuciyarsa cike da ƙuna ya tashi ya bar sashen ta.
Murmushin fuskar Nana ya kasa ɓoyuwa, Ƙaisar shi ma murmushin ya yi, kamar koyaushe gyaran litattafansa yake yi. Ya ce "A karo na babu adadi, ina sake taya ki murna ma a wannan karon, tabbas ko a iya haka kin yi nasara. Kuma aya ce ke mai zaman kanta ga mutanen Agadez ba Agadez ba kawai ga duk wani mai hankali ma. Jaruma ce ke ta gaske uwar gijiyata"
"Ƙaisar"
"Na'am"
"Ina yi maka kyakykywan fatan alkhairi na har abada "
Ya ajiye littafin hannunsa ya ce "Har kin mantan Allah ya isan da ki ka yi mini a baya"
Ta katse shi ta hanyar cewa "Duk wanda yake rinjayar da laifukan mutane, sama da alkhairinsu, to zai zama mara adalci"
Ya ce "To ai ni ba mutum bane"
Ta yi dariya ta ce "Ni a gurina kai mutum ne. Alkhairinka ya shafe laifukan ka Ƙaisar. Gaba ɗaya ji nake yi kamar ba ni ba, zan rayu da Hammad ɗina, da kuma Muhsin Allah abin godiya kamar komai ba zai wuce ba"
Ya zauna yana faÉ—in "Babu abin da ba ya wucewa sai ikon Allah"
Za ta yi magana ta farka daga baccin da ya É—an É—auke ta.
Da Sayyid ta fara tozali ya ce "Amarya"
"Ango" Ta amasa masa tana murmushi.
"Nene ta ce sai na mayar mata da ke, wai shirya ki za a yi, ba dai yadda zan yi ne, na fi son ta bar mini ke in din ga jin ɗuminki. Ke ba kya buƙatar duk wani gyara, a gyarenki Allah ya yi ki"
Nana ta tashi zaune ta ce "Allah ya shirya mini kai, Nenen zaka gaya wa haka ko? Ni sonake ma na gana da É—an uwana na yi kewarsa"
Hammad ya numfasa ya ce "Kin san Sultan sun samu matsala da Imam Zahradeen, ina ta girgiza miki kai É—azu, ki bari sannu a hankali zai saukko zan san yadda zan yi na shirya su. Amma da farko ji na yi kamar ba zan yafe masa ba. Amma na duba girman abubuwan da ya yi na alkhairi a gare ni. Kuma ni duk mutumin da zai yi abin da zai kyautata miki to ni ya yi wa, dan haka na ji zan mayar da komai ba komai ba. Kin san wani abu ma vie"
Ta girgiza masa kai alamar a'a.
"Wallahi idan na kalle ki, na kalli Muhsin, sai in ji zan iya yafe wa kowa ma, Duniyar guda nawa take? Allah ya yi mini tagomashi da abin da na san ba dabara ta ba ce ba. Ba zan fasa gode wa Allah ba"
Nana ta ce "Tabbas Allah abin godiya Sayyid. Amma ina da wani roƙo a gare ka; kamar yadda ku ka soke al'adar haramta auratayya tsakaninku da baƙaƙen fata, ina roƙon ku haramta duk wani nau'i na ta'amalli da Aljanu da shaiɗanu"
Ta É—an yi shiru tana satar kallonsa.
Ya ce "Ina jinki"
Ta ci gaba da faɗin "Ta'amalli da aljanu, da hana iliminku na addini tasiri a cikin rayuwarku, haɗi da riƙo da munanan al'adu su suka ƙara ta'azzara wasu abubuwan. Ga dai zobunanka masu ɗauke da hadiman aljanu, amma hakan bai hana a cutar da kai ba, cuta mai munin gaske. Su ba su baka kariya ba, su ba su hana a cutar da kai ba. Babu wata halitta da zata baka kariya ko ta hana faruwar wasu abubuwan a rayuwarka. Sai dai duk da wannan abin, ina girmama riƙo da ibadarka mussaman salla. Kai ma'abocin salla ne. Dan Allah Imam ka ƙara ƙoƙari gurin ganin an kakkaɓe al'adar amfani da aljanu a cikin harkar mulki. Ga saɓon Allah, ga gadar wa zuriya masifa da tashin hankali. Ni da kai ɗin nan mislai ne akan kanmu, ba zamu yi fatan ire-iren zuriyarmu su gaji wannan bala'in da muka shiga ba. Dan Allah Hammad ka yi ƙoƙari a yi yaƙi da ta'amalli da su, da kuma duk wani abu da ya shafe su. A ɗayanta Allah, a dogara da shi duk ba kwa buƙatar wannan abubuwan muddin kun riƙe Allah ".
Ya numfasa ya ce "Maganganunki duk gaskiya ne Ma vie, kuma tuntuni na fara ƙoƙarin neman maraba da su, ni kaina na daɗe ba na son harkar da muke yi da su, amma in sha Allah zan ƙara ƙarfafa hakan, har abada za a daina amfani da duk wani nau'i na gurɓatacciyar al'ada a Agadez"
Nana ta rungumo shi ta ce "Yauwwa farincikina, Ubangiji Allah ya saka maka da alkhairi, ya ƙara kare mini kai daga dukkanin wani sharrin. Allah ya ƙara ɗaukaka mini darajarka zuwa inda zato bai taɓa zato ba. Allah ya yi maka kyakykywan tsari daga sharrin duk wani abin ƙi komai ƙanƙantarsa."
Ya tsurawa Nana ido, sannan ya ce "Ta yaya ake so na iya rayuwa babu wannan halittar? Halittar da harshenta kullum cikin yi mini addu'a da fatan Alkhairi take.
Mai ɗauke da zuciyar da kullum take ƙoƙarin kusantar da ni ga Allah, baiwar Allah da kullum burinta ta sadaukar Saboda da komai saboda ni. In sha Allah mutuwa ce zata raba ni da ke rayuwata. Allah ya yi miki tukuci da gidan aljanna. Ina ƙaunrki Asma'u." Ya yi maganar yana tsare ta da manyan idanunsa, da ba ta san dalilin canzawarsu zuwa ja ba.
"Nima ina ƙaunarka mijina, irin sosai da sosai, ban san ya zan misalta maka ba"
"Ba sai kin misalita mini ba, na gani a zahiri" Ta sunkuyar da kanta tana É—an murmushi.
Ya ce "Yanzu me za ki shirya mana, na shirin bikin? Sultan ya ce sai an yi biki sosai a Agadez, me za ki shirya mana? Me da me ki ke so?"
Ta girgiza kai ta ce "Kai kaÉ—ai kawai nake so, kai kaÉ—ai ka ishi Nana komai"
Ya yi dariya ya ce "Zan kawo miki Imrana da Muhsin, har ma da Nene anjima su É—ebe miki kewa"
Nana ta ce "Amma kuwa da ka kyauta, na gode sosai da sosai"
Ya dungure mata kai yana murmushi.
*****
Alhaji Fatuhu kuwa bacci ne ya gagare shi, kamar yadda dariya ta gagari kare, ya gagara yin bacci.
Idan ya samu baccin ya fara ɗaukarsa, kawai sai ya ga Hajiya Sa'a, tana kuka tana sake maimaita abin da ta faɗa da suka je. Duk yadda ya din ga addu'a, da ƙoƙarin kawar da tunanin daga zuciyarsa, amma abu ya faskara.
Sai dai ya danne ya ci gaba da addu'a.
Sai kuma doctor Sharif ya faɗo masa, da shi ma yake cewa ya yafe masa, to ya yafe masa da ya yi masa me? Gaba ɗaya sai al'ajabi, ya hana shi yin farincikin dawowar kayansa. Ga shi ya zo gaya wa Alhaji Zailani, tun da dama shi ne abokin kasuwancinsa, amma ya tuna yadda Fadila ta gargaɗe shi a kan haka.