Sashe 38
Buzu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Karo na farko Hammad ya buɗe baki zai yi magana, amma Sultan ya dakatar da shi ya ce "Baka saba haka ba, kar ka fara a wannan karon, kai mai haƙuri ne, a wannan karon ma ina son ganin tasirin hakan a gare ka" Ya haɗiye yawu mai zafi, idanunsa suka yi jawur. Ya din ga zuwa Asibiti shikaɗai aka duba shi aka ce masa lafiyarsa ƙalau.
Asal kuma ta ci gaba da yi masa kuka da magiya a kan ya yi haƙuri su ci gaba da addu'a, ta san wataran za ta haihu, amma ya bar maganar ƙara aure, dan da gaske idan ya yi aure sai ta kashe kanta. Ya so ya yi mata magana a kan to ta bari su je Asibiti, amma ya tuna abin da Sultan ya ce masa, dan haka a dole ya ja bakinsa ya yi shiru ya ci gaba da addu'a.
Duk wanda ya yi alkhairi fatansa ya yi masa addu'a Allah ya ba shi haihuwa mai albarka, duk inda ya ji maganin haihuwa, da ya yadda da ingancinsa, sai ya karɓo ya kawowa Asal. Shi kansa Sultan abin ya dame shi, ba yau ba gobe cikin yi wa Hammad addu'a yake, ganin yadda yake ruɗewa idan ya ga 'ya'ya, duk wanda ya haihu a masarauta muddin ya ji labari, sai ya yi masa kyauta mai tsoka ya ce shi ma a yi masa addu'a.
Matawalle ya samu Sultan ya ce "Anya ba ka ganin kamar an cutar da Imam Hammad da yawa, da an bari ya jarraba auren wata matar mu gani ko Allah zai sanya a dace"
Sultan ya girgiza kai ya ce "In sha Allah zai ga daidai a rayuwarsa. Ina jin tausayin Asal ne, gaba ɗaya hankalinta a tashe yake, amma a ɗan ƙara haƙuri a ci gaba da addu'a. Kuma ka san mahaifinta ba ya raina abin magana, yanzu sai abin ya zama na surutu.
Ita kanta Asal abin ya dame ta, mussaman ganin yadda Hammad ɗin yake damuwa da lamarin 'ya'ya, sai dai baya yi mata maganar. Tun da ƙananan shekaru, Hammad ya haɗu da larurar hawan jini ake ta fama.
Asal ta ƙara shiga tashin hankali, ganin yadda ake ƙara yi wa Hammad tayin matan aure, ga shi matan ma farmaki suke kawo masa, saboda yadda siffofin kamala da cikar zati ke bayyana a tattare da shi. Su kansu kuyangin gidan su na neman su zama mallakinsa.
Sai dai a ransa ko zai yi kuyanga, baƙaƙen nan yake so ba farare ba. Duk ya kawar da kansa saboda Asal.
Wataran ya fito zai fita, wata hadima ta risuna cikin girmamawa tana gaishe shi ya ce "Sa'ada na daina ganinki kwana biyu"
"Allah ya taimake ka, na yi rashin lafiya ne"
"Subhanallah, ai ban sani ba, kin rame sosai da sosai. Maza ki je a duba ki, kuma ki ci abinci sosai, kin fi kyau lokacin da ki ke da ƙiba, Allah ya sauwwaƙe" wasu lokutan Hammad akwai raha, saboda a cewarsa hakan zai ƙara masa kusanci da hadimansa, shi ba ya son wannan tsoron nasa da suke yi.
Ta risuna cikin girmamawa tana murmushi ta yi masa godiya. Aikuwa ta sha bala'i a gurin Asal, ƙarshe ta kore ta daga sashen girke-girken gidan, zuwa wani abin daban.
Asal ta saka masa kukan, dan me zai kula wannan hadimar, sannan ya yabi jikinta. Ya din ga rarrashinta ya ce shi ba da wani abu ya yi ba.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, ana tursasa Hammad jure abubuwa da dama Saboda Asal.
Kwatsam Tafawa ya kira Asal, ya ce ta je ta same shi, sai da gabanta ya faɗi tana zaton ko wani laifin ta yi. Ya kira ta cikin turakarsa. Ya ɗaukko mata wata 'yar ƙaramar laya, ya ba ta ya ce ta je ta samu wani guri da ido ba zai kai kanta ba, inda Hammad yake zama ta saƙale ta.
Ta yi shiru tana kallon layar, amma babu yadda ta iya haka ta karɓa ta tafi da ita. Ta din ga tunani ta saka ko kar ta saka. Saboda ba ta san ta mece ce ba. A iya zaman da suka yi tsawon shekaru tare, ba za ta iya cewa ga wani abu na cutarwa da Hammad ya yi mata ba, sai ma shi da yake shanye abubuwa da dama take yi masa, komai cutarwar hakan a gare shi.
Cikin dare yana tsaka da barci, ya ji tamkar ana girgiza gadon da yake kai, ya din ga ganin wasu irin halittu marasa kyan gani da tsoratarwa. A haka ya wayi gari kansa na neman juyewa, tun gari ya waye ya daina magana. Asal kanta sai da ta tsorata. Sai da suka kwana biyu da kyar yake iya cin abinci, sai ya din ga abu kamar baya cikin hayyacinsa. Tafawa kuma ya din ga kiranta yana tambayarta duk halin da ake ciki.
Sai da ta ga da gaske baya magana, ko majalisa baya fita, ta tsorata ta sanar da Sultan halin da ake ciki. Aka kai shi Asibiti amma aka kasa gane abin da yake damunsa. Sai dai jininsa da yake hawa fiye da kima. Ya yi jinya sosai da sosai.
Da kyar ya warke, sai dai Tafawa bai haƙura ba, gefe babar Asal ta bazama neman maganin haihuwa tana ba wa Asal. Sai dai kwatsam! Ita ma ta haɗu da jinya, ciwon suga ba ta san tana da shi ba ya yi ajalinta. Asal ba ƙaramin kaɗuwa ta yi ba, da rasuwar mahaifiyarta tamkar za ta zare. Hammad ya yi ta rarrashinta yana ba ta baki.
Tafawa bai samu zama ba, ya tashi nan ya faÉ—i can, duk domin ganin burinsa ya cika, gaba É—aya rayuwarsa ba shi da cikakken sukuni, haka nan ya hana Asal ta zauna lafiya tare da mijinta.
Ya zamana ku san kullum ba shi da cikakkiyar lafiya, yau da lafiya gobe babu.
Tafawa ya fara magantuwa a kan yawan rashin lafiya da Hammad yake yi, yakamata ya sauka daga kan shugabancin Majilisar Imam, a bawa wani. A majalisar Sultan aka soke maganar da ya kawo.
Hammad kawai yana tafiya ana ganinsa, amma a cikin jikinsa shikaɗai ya san abin yake ji. Ko Asal bai fiye sakin jiki da ita ya gaya mata damuwarsa ba, saboda sam ba ta da alƙibla, kuma tsawon shekaru da suka shafe tare, ba ta iya fahimtar damuwarsa rashin lafiya kai tsaye, sai idan tana da buƙatar wani abu a gurinsa.
A haka ta sake neman komawa karatu, lokacin Hammad ya karaya da neman haihuwa. Idan yana salla har kuka yake yi, abin yana burge shi ya ga mutum da ɗan uwansa sun haɗa kai, shi kuma ba shi da wanda suke ciki ɗaya. Mahaifinsa kuma ayyuka sun yi masa yawa, matarsa kuma bai gama gane kanta ba. Dan haka duk wani rikicinsa, shi kuma ba ya gajiya. Wasu lokutan ya na jin daɗin ya bi Mahmoudu gurin Ummansa, su je su wuni, su ci abinci tare. Duk da yana matuƙar jin nauyinta, na abin da aka yi mata a masarautarsu, sai dai bai taɓa ganin hakan a fuskarta ba.
Ya yi shiru yana kallon Nana, da ta yi shiru tana saurarensa.
"Ya ka yi shiru kuma?"
"Na gaji, kuma bacci nake ji"
Ta ce "A'a wannan wayo ne na kar ka ƙarasa mini, dama ni ƙarsheƙarshen nan, ba jin daɗinsa na yi ba, gara ma farkon labarin tun da tarihi ne."
"Saboda zancen Asal ne?"
"Zan iya cewa eh É—in ma, saboda mutane kaÉ—an na tsana a Duniya, kuma ta shiga cikinsu" Ta yi maganar tana tsuke fuska.
"Amma meyasa?"
Nana ta ce "Kawai ba ta yi mini ba"
Hammad ya yi shiru ya ce "Ba na tunanin kishi ne kawai ya sanya ki ka faÉ—i haka, akwai wani dalili, ba kya faÉ—ar magana haka kurum mara ma'ana"
Ta ɗan gyaɗa kai ta ce "Ba mai ma'anar ba ce gaskiya, mu je a haka kawai, kishi ne ya sanya na faɗi haka. Yanzu dai ni ka tsallake nan, ka gaya mini yadda aka yi ka din ga wasa da hankalina, da yadda ka gane ni amma ka share ni, nake yi wa matarka aiki cikin ƙasƙanci da wulaƙanci. Kuma alhalin ka na iƙirarin ka na so na. Har kuka na yi mata, da ta ce za ta kawo ni Agadez na ce mata ina da jariri, amma buɗar bakin matar nan ta ce ni ta shafa, tun da talaka ce ni dole na yi abin da take so. Ba zan manta wasu abubuwan da ta yi mini ba na cin mutunci har abada"
Ya É—ago da fuskar Nana tana kallonsa ya ce "Ba wannan ne dalilin da ya sanya ki ka ce ba kya sonta ba, akwai dalili. Wannan ba halinki ba ne, idan wannan dalili ne da abin da na yi miki ba za ki sake zuwa inda nake ba"
AREWABOOKS
Ta kawar da kanta gefe ta ce "Ka ƙarasa mini kawai, mu bar wannan maganar"
"Asmy, Asal ko ba aure tsakanina da ita matata ce, ban kuma gaya miki halin da muke ciki, domin na tozartata ba, iya abin da na sani na sanar da ke game da zamantakewar mu, saboda shi ne mahaÉ—in labarin rayuwata da ke"
"Ai dama ban ce kar ka so ta ba, ka je ka yi ta son nata"
Ya ce "Ai ba zancen so muka yi da ke ba, ki yi shiru mu ƙarasa an kusa fara kiran Asuba"
"Ba na son ji" Ta yi maganar tana kifa kanta tare da tsuke fuska.
"Merci ma viee, ba na son ki din ga ɓata ranki, mun bar wannan maganar tun da ba kya so, yadda ba na son kowa ya raɓe ki, ke ma haka ne na sani, kuma na san kin yi ƙoƙari kin yi haƙuri sosai da sosai da juriyar da ki ka cancanci a sara miki, amma ki yi haƙuri mu ƙarasa maganar, daga ƙarshe duk hukuncin da ki ka yanke mini, zan karɓa"
Ta ɗago kanta, zuciyarta na yi mata wani irin zafi, azababben kishin Asal yana taso mata, babu abin da yake ƙara ɓata rai irin cin mutuncin da Asal ta din ga yi mata a matsayin kishiyarta.
"Kin huce mu ci gaba?" Ta yi masa shiru.