← Book details Buzu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 82

Sashe 53

Buzu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tafawa bai yi shiru ba ya ci gaba da zazzaga bala'i kamar zai ari baki. Har sai da ran Sultan ya ɓaci. Ya yi wa Hammad umarnin ya tashi ya tafi kawai. Yana rumgume da Hammad ya ji muryar Asal a bayansa.
Ya tsaya ya waiwaya yana kallonta, tamkar mahaukaciya sabon kamu ta ce "Hammad yau nika tozarta a gaban jama'a ka zaɓi bare baƙuwar haure a kaina, ka ƙasƙanta ni a gaban mutane, Hammad ni?"
Ya girgiza kai ya ce "Asal ban ƙasƙanta ki ba, kuma har abada ba zan yi ba. Kamar yadda Nana ta faɗa daga ni har ke mu na cikin ahalinmu, muna da cikakkiyar ahali ita kuma fa? Sannan kuma harshenka alƙalinka Asal. Da raina da lafiyata da ƙuruciyata ki ka kalli tsabar idona ki ka din ga jifa na da kalaman ba kya sona ba kya ƙaunata. Duk da na yi miki uzurin ƙuruciya da yarinta a wancan lokacin, amma haryanzu ina ganin wani abu a cikin idaunki da ban tantance so ne ko ƙiyayya ba. Nana ta so ni a bata san waye ni ba, ta so ni a mutum mara asali da makoma auren shahada da kasada, ta rayu da ni da na ɓacewa duniyarta ta ci gaba da bulayin nema na, ba dan tana sanya ran na saka mata ba. Ki duba ratar za ke tsakanin misalan da na baki" Ya wuce rungume da yaronsa ya tafi.
A ƙarshe dai Imam Zahradeen ne ya mayar da Sultan turakarsa sai jiri yake yi saboda ɓacin rai. Ya ɗebo ruwa ya ba shi ya karɓa ya sha yana mayar da numfashi.
Sultan ya ce "Zahradeen"
Ya amsa da "Na'am Abbie".
"Na rasa ta ina zan ɓullowa lamarin nan gaba ɗaya"
Zahradeen ya numfasa ya ce "Allah ya taimake ka, da Tafawa ne a matsayin da ka ke, komai za a yi ba zai taɓa ƙin goya wa ɗansa baya ba, dan ya faranta muku ba. Ka rintse idanunka ko toshe kunnenka. Ka kamanta yarinyar nan a matsayin 'yar cikin ka. Ana maganar shekara biyu zuwa ta uku rabonta da gidansu. Ka ga dai yadda yake zare idon nan, bai ƙi ya aikata duk wani abin kunya da zai zubar da mutuncin Agadez ba.
Abie shin ba ka tunanin wata aya ce Ubangiji Allah ya saukar mana, domin ya nuna mana fari da baƙi halittarsa ce kuma duk yana kishi da son abin sa? Ka lissafa Allah ya hana shi haihuwa duk da ya yi aure da ƙanan shekaru, aka hana shi ƙara aure. Lokaci ɗaya Allah ya jarabce shi da ciwon da sai da ya keta ya bar Niger ya tafi Nigeria rabon wannan ɗan ya kai shi har can. Kuma duk da haka Allah ya jarabce shi da ciwon da sai tana kusa da shi yake samun afuwa. Yanzu idan muka rintse idanu daga hukuncin da Allah ya zartar dan mutunta al'ada muka tozarta baiwarsa kana tunanin Allah zai barmu? Ka duba ɗan jaririn yaron nan da yake kai komo a tsakanin su cikin farin ciki idan aka raba su, duk gatan da za a nuna masa bai kai ya tashi a tsakanin iyayensa ba. Abie Mai girma Tafawa ɗan uwanka ne, kuma ɗan uwan mahaifiyata ne, amma ina mai tabbatar maka ba zai taɓa ƙaunarka ba, har gara ni yana yi mini kara saboda ɗan 'yar uwassa ne, amma ba zai taɓa son Hammad ba. Kai kuma Hammad ɗanka ne komai za a yi ka banƙara shi ma ya samu abin da yake so"
Sultan ya yi shiru cikin nazari, ya numfasa ya kalli Imam Zahradeen ya ce "To yanzu kai me ka ke tunani, kuma meyasa ba ka yi mini duk wannan bayanin tuntuni ba?"
Zahradeen ya ƙara nutsuwa ya ce "Ina tsoron shiga lamarin ne a baya, amma Hammad da kansa ya same ni da maganar, kuma ya nuna mini yarda ta hanyar ajiye ɗansa a gidana. Yanzu ka bar wani batun Tafawa da wata majalissa kai ne Sultan, idan ka yi doka dole a bi ta. Ka bar Imam Hammad da matarsa, kuma ka soke wannan al'adar da aka ba wa wannan ƙarfin, ka yi musu fatan alkhairi"
Sultan ya girgiza kai cikin jimami ya ce "Ba abu ne da zai yiwu cikin sauƙi ba"
"Ka duba dai Abie, ka duba makomarsu baki É—aya"
"Shikenan, ka je zan yi tunanin abin yi"
Imam Zahradeen ya ce "To shikenan Abie, amma dan Allah kar ka jira sai ka yi shawara da wani a cikin 'yan majalisarka"
Sultan ya ce "To shikenan"
Imam Zahradeen ya miƙe tsaye, ya ce "Bari na ƙarasa gurinsu, zan karɓi Muhsin na tafi da shi"
Sultan ya jinjina kai kawai.

Hammad ya shiga ɗakin da Nana take, cike da takaicin yadda ta ce, ita ta haƙura da shi, a bata ɗanta ta koma Nigeria, sai dai ya tarar da ita tana kuka.
Ya kwantar da Muhsin da ya yi bacci, ya ƙarasa gabanta ya ce "Meyafaru kuma ki ke kuka?" Ta yi shiru ta ci gaba da kukan.
"Mene ne?" Ya sake tambayarta.
"Sayyid" Ta kira sunan shi a raunane. Ya zauna a kusa da ita ya ce "Mene ne?" Ya yi maganar yana É—ago ta cikin damuwa.
Ta ƙanƙame shi tana kuka ta ce "Sayyid na faɗi haka ne dan su daina yi maka faɗa, amma ina sonka wallahi Sayyid, dan Allah kar su raba ni da kai" Ta yi maganar tana sheshsheƙar kuka.
Shi ma rungumota ya yi sosai da sosai a jikinsa, yana wata irin ajiyar zuciya.
Da kyar ya tattara nutsuwarsa, ya ce "Ki yi haƙuri Ma vie, Ubangijin da ya haɗa mu ne kaɗai zai raba mu. Ni da ke mutu ka raba in sha Allah"
Zata yi magana suka ji ana bubbuga ƙofar ɗakin, Nana ta motsa za ta tashi, amma ya riƙe ta kuma ya yi umarnin a shigo.
Imam Zahradeen ne ya buɗe ƙofar ɗakin ya shigo, kunya duk ta kama Nana.
Ya É—an tsaya yana kallonsu ya ce "Kuka ku ke ne?" Nana ta yi saurin tashi tana share hawayenta ta ce "A'a".

Imam Zahradeen ya ce "Ga idonki nan duk hawaye. Wai  me ki ke gaya masa ne, ya sanya duk ya rikice haka a kanki"
Nana ta sunkuyar da kai tana murmushi.
Imam Hammad ya ce "Komai ma gaya mini take yi, shiyasa nake jin tamkar raba ni da ita, raba ni da rayuwata ne"

Zahradeen ya jinjina kai ya ce "Na ga alama ai. Amma dan Allah ku kwantar da hankalinku, ku ci gaba da addu'a, in Allah ya yarda a dalilinki za a sauya tsarin wasu dokokin na Agadez. Yanzu dai Muhsin zan É—auka zamu tafi"
Cikin marairaicewa Nana ta ce "Dan Allah ka bar mini shi a nan" Ta yi maganar tana kallon Imam Zahradeen.
Ya girgiza kai ya ce "A'a barinsa a nan babu tsaro, tsawon lokacin nan yana tare da ni a can gidana, gobe in Allah ya kaimu za a kawo masa maman Mahmoudu. Idan kuma ba a yarda da ni ba, na bar ku abinku"
Nana ta ce "A'a amma dan Allah ka tafi da ni, ina son na zauna tare da shi, kuma na ga Nene."
"Wani irin mugun kallo Hammad ya yi mata"
Zahradeen ya ce "Ai ko ba ki ce komai ba, dole za ki bar gidan nan, taso mu tafi"

Hammad ya ce "Ya haka? Ku tafi ku je ina? Kuma yaya zaka tafi da ita Sultan bai sani ba?"

Imam Zahradeen ya ce "Idan zaka biyo mu ne taso"
Nana kuwa ta yinƙura ta tashi ta ɗauki jakar kayanta dama da hijjabi a jikinta.

Hammad ya miƙe ya ce "Wai bin nasa za ki yi?"

"Ni ba na son zama a nan, na gaji" Nana ta furta tana tura baki.

Imam Zahradeen ya É—auki Muhsin, ya kalli Imam Hammad ya ce "ÆŠaukko mata jakarta"

Zahradeen yana fita, Hammad ya riƙe ta ya ce "Dan me zaki ce za ki bi shi? Meye haka ki ke yi ne?"

"Amma Sayyid na ga yayanka ne fa"

"Ko ma wane ne, dan me za ki bi shi?"

Ta girgiza kai idanunta na cika da hawaye "Ni na gaji da zaman gurin nan? Ni gaba É—aya ma tsoro nake ji"

Sayyid ya ce "Muje kar ki yi mini kuka" Ya saka Nana a gaba, suka bi ta baya, sai ga su a harabar gidan. Zahradeen har ya kwantar da Muhsin a cikin motar.

Hammad ya buÉ—e wa Nana bayan motar, sai hararta yake yi, amma ta basar ta shige cikin motar ta kawar da kai. Haka nan take jin kamar ta fito daga kurku sai wani irin farinciki take ji da nishaÉ—i, a haka ya bar gidan da Nana a cikin motar.

Tafawa kuwa ya ɗauki zafi, ya ci gaba da ziga 'yan majalisar Sultan a kan lallai su sanya ido a hukunta Hamma, sannan ya yi baƙin cikin fito da zoben nan da aka yi.

Matar Imam Zahradeen ita ma haka take kyakykyawar gaske, fara sol da ita, yaransu huɗu, kyawawa su ma. Sai dai Nana ta ga matar ba ta ƙyamace ta ba, ta rungume Nana tana faɗin yau ga Umman Muhsin, baƙar Gimbiya ta farko a kaf faɗin Agadez.
Nana dai ta kasa sakin jiki da matar, dan duk mutanen Agadez É—in tsoro suke bata, kusan kowa ba abin yarda ba ne.
Ganin Nana ba ta sake da ita ba, ya sanya ta bar ta a É—akin da aka sauke ta.
Chapter 53 · 0% Book details