Sashe 27
Buzu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mai bugun ne ya gaji da bugawa, ya turo ƙofar, Sultan ne tare da wata babbar mace fara solnda ita. Sai kuma Mahmoudu.
A rikice suka ƙarasa gaban gadon, cikin tashin hankali Sultan ya ce "Jikin ne?"
"Ki tashi mu tafi, zan rasa raina, ƙwaƙwalwata za ta tarwatse. Ki yi mini addu'a"
Tuni Nana ta fara kuka, ta ce "Ina yi maka, kai ma ka din ga yi ko a zuciyarka ne. In sha Allah babu abin da zai same ka"
Matar ta ce "Wannan ce matar tasa?"
Sultan ya jinjina kai ya ce "Ita ce"
Ta ce "Ikon Allah, lallai Allah gwani ne"
Mahmoud kuwa jiki a sanyaye ya ce "Sannu Imam"
"Hamud, dan Allah ka É—auke ni ka sake tafiya da ni, ba na son zaman garin nan, ba ku san me nake ji ba."
Mahmoudu ya kalli Sultan ya ce "Ranka ya daÉ—e, a irin wannan yanayin fiye ma da wannan, na bar Niger da shi a wancan lokacin. To kuma na ga alamar jikin na neman sake dawowa.
A hankali ya fara fita hayyacinsa, ya fara lanƙwasa Nana, ta rintse idanunta Sultan ya ƙarasa da sauri yana faɗin "Kai kar ka yi wa 'yar mutane illa, Hammad" Mahmoudu rasa abin yi ya yi, dan ya san ganganci mafi girma da zai aikata shi ne ya taɓa jikin Nana garin ƙoƙarin ɓanɓare shi daga jikinta.
Sai kuma Sultan ya ja ya tsaya shi ma ya rasa abin yi.
"Ke kin san me nake ji ai" ya sake futawa cikin ƙarfin hali.
"Na sani, shi ya sanya nake yi maka addu'a"
Sultan ya ce "Hammad, kar ka ji mata ciwo fa"
A hankali Nana ta ce "Ba zai ji mini ba in sha Allah"
Addu'a ta ci gaba da yi masa, tana tofa masa. Sultan kam kasa jurewa ya yi, saboda ba ƙaramin tashin hankali yake shiga ba, idan ya ga ɗan nasa a cikin wannan yanayin.
Sai kusan ƙarfe biyu na dare sannan ya dawo hayyacinsa gaba ɗaya. Ya yinƙura ya tashi zaune yana kallon Nana.
Ta ce "Sannu. Ka daina jin abin da ka ke ji É—in?"
Ba ta yi zaton zai iya magana ba ta ji ya yi, ya ce "Ina ji amma ya lafa mini"
Ta ce "To Allah ya baka lafiya ingantacciya. Amm ka yi haƙuri kana cikin yanayin larura zan tambaye ka abu" ya yi shiru yana kallon ta.
Ta É—ago masa wannan takardar ta ce "A cikin rigarka na ganta, waye ya saka maka ita?" Ya girgiza kai ya ce "Nima ban sani ba"
Ta sake cewa "Shekaranjiya wani abu mai kama da mafarki ya faru, har muka fita ta wata ƙofa, gaske ne ko kuma mafarki nake yi?"
"Gaske ne" Ya bata amsa kai tsaye.
"Ina buƙatar fahimtar wasu abubuwan, dan ka na yin abubuwan da ba kowane ɗan Adam ne zai iya ba. Tun mu na Nigeria ka ke yin wasu abubuwan. Kuma ina buƙatar na ji abubuwan da suka faru wanda ban sani ba" Ya numfasa ya ce "Zo ki raka ni shan iska tukuna" Suka sauka daga kan gadon. Ya zira rigarsa ya buɗe ƙofar nan, suka ƙara ratsa duhu suka fita wannan corridor.
Yau ma saharar ta gani, gurin ya É—auki sanyi sosai da sosai. Ta kalli Wannan tsaunin dake gefen saharar ta ce.
"Wai mene ne a cikin dutsen can, shi nake son sani"
Ya kalli gurin ya ce "Nan ne ainihin inda kakanninmu suka fara mulki, dan haka duk wani kayan tarihi, a ciki a ke adana su"
Nana ta ce "To ka gaya mini abin da na tambaye ka, kuma ina son ka kai ni na ga abubuwan tarihin garin naku"
"Zan kai ki, kuma zan yi miki bayanin amma yanzu ba na jin daÉ—i"
Ta É—an shafa bayansa ta ce "Sannu" ya jinjina mata kai. Ya matsa kusa da ita, ya rungume ta, sanyin gurin ya din ga ratsa su a tare.
Ta ɗaga kai tana kallon wannan tsaunin, da ya ce mata gidan tarihi ne, tana jin kwaɗaituwa da son sanin abin da gidan ƙunsa.
Tana jin kewar Ƙaisar, ta damu sosai ta san ya jikinsa, amma ko sama ko ƙasa ta daina ganinsa.
Ta lumshe idanunta ta buɗe, kewar gida kuma na sake bijiro mata, tana cikin matuƙar fargaba a kan irin karɓar da za a yi mata idan ta koma.
"Ma viee"
"Na'am Shugabana"
"Ina da wani kyakykywan albishir da zan baki, amma ba yanzu ba"
Ta yi murmushi ta ce "Sai yaushe?"
"Sai an wa Muhsin ƙani"
Ta ce "Babu rana kenan"
"Akwai mana nan kusa" yayi maganar yana ƙara ƙanƙameta.
Asal kuwa yadda ta ga rana haka ta ga dare, dan faÉ—a suka yi kaca-kaca da Hammad, duk da rarrashin da Sultan ya yi mata.
Ta kira Hasna a waya, Hasna ta É—aga tana "FaÉ—in Gimbiya Asal, kwana biyu"
Cikin kuka ta ce "Hasna, kin san abin da Hammad ya yi mini kuwa?" Gaban Asal ya faÉ—i ta ce "Meyafaru?"
"Hasna wai Hammad yana da É—a"
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, É—a kuma kamar yaya?"
Cikin kuka ta ce"Ɗa dai ya haihu da wata, Tafawa kuma ya tabattar mini da hakan, kin san ba zai yi mini ƙarya ba. Kuma ba na ce miki yarinyar nan ta gudu ba, mai yi masa girki ba, har nake ce miki duk inda ta gudu zan saka a nemo ta"
Hasna ta ce "Eh haka ne"
"Na je na kama shi da ita, a can cikin sashen Sultan, duk tsawon lokacin da aka shafe ba ta nan, suna tare su na lalacewa, na shiga uku Hasna, ji nake kamar na kashe kaina na huta. Na tsani Hammad na tsane shi, ban taɓa cin karo da abin da ya gigita ni ba, kamar abin da na gani yau ba. Kuma Sultan goyon bayansa yake yi, wai in bari za a yi mini bayani, bayanin me za a yi mini an cuce ni Hasna" Ta yi maganar tana ƙara rushewa da kuka, kamar wadda aka nuna wa ranar mutuwarta.
Hasna ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Asal, ki yi haƙuri ki nutsu, ki tattara hankalinki guri ɗaya kar ki yi ganganci da rayuwarki. Amma ni kwanaki na ji Al Hussain yana cewa ya kira shi ya ce ya yi masa bincike a kanta, a nemo kamfanin da suka kawo ta. To ni ban kawo komai a raina ba, na ɗauka da saninki, amma zan tambaye shi ko ya san wani abu. Amma dan Allah ki yi haƙuri ki kwantar da hankalinki"
"Ba ki san me nake ji ba, hankalina ba zai taɓa kwnaciya ba" Haka Asal ta kwana ido biyu, babu abin da take hangowa sai abin da idanunta suka gane mata a tsakanin mijinta da wannan baƙar yarinyar.
Bangaren su Nana da safe, da Mahmoudu ya kai musu abinci, ya sanar musu da cewa Sultan ya ce su zo gaba ɗayansu, mai maganin ya ƙaraso.
Hammad ya ce "Waye mai maganin?"
Ya ce "Ban san waye ba, kawai dai saƙon da ya bani kenan"
"Ni fa ba na buƙatar wani mai magani, ga maganina nan a gefe na" Ya yi maganar yana kashewa Nana ido.
Ta basar da shi, ta ɗan yi murmushi. Ya karya sannan suka rankaya suka fita tare. Tun da aka kawo Nana, sai a lokacin ta samu damar sake fitowa daga ɗakin da suke. Sai dai wani surƙuƙin ɗakin suka shiga. Abin har mamaki yake ba wa Nana, yadda ake ɗakuna a lunguna da saƙo na gidan, kamar marasa gaskiya, inda ba ka yi zato ba ma, sai ka ga ɗaki ne.
Da Asal ta yi tozali a É—akin, idanunta jawur, tana ganin Nana ta sake tsuke fuska, kamar ta tashi ta kashe ta ta huta. Suka je gaban Sultan suka gaishe shi, Nana ta basar ko kallon inda Asal take ba ta yi ba.
Sultan ya ce "Asal, na saka an kira ki ne, saboda a yi komai a gaban idonki, a ji me mai maganin zai ce, saboda kina da hakki ki sani kar ki ga ana ci gaba da rufe ki a kan abubuwa, tun da mijinki ne" Ta yi shiru, saboda shi kansa Sultan É—in haushin sa take ji.
Sallamar da aka yi ne ya sanya Sultan yin shiru, Nana kuma ta miƙe tana faɗin "Kaii Sarki, dama ka na nan?"
Ya yi dariya ya ce "Tuba nake uwar gijiyata, tuba nake uwar É—akina"
Bakin Nana ya ƙi rufuwa, tamkar ta ga wani ɗan uwanta na jini.
Cikin murmushi ta sake cewa "Sarki mai baka mai aska, kai ne mai maganin da zaka duba Sayyid?"
Ya ce "Ni ne uwar gijiyata, an yi mini lamuni, ko kuwa na koma ba a bani dama ba?.
Ayshercool 08081012143
88
1K NE VIA 0069685771
AISHA ADAM STANBIC IBTC BANK 08081012143
Nana ta kalli Sarkin baka ta yi murmushi ta ce "Wane mutum! Dama zan sake ganinka?"
Ya yi murmushi, hadimin da ya rako Sarkin baka, ya ankarar da shi Sultan. Cikin girmamawa Sarkin baka ya risuna ya kwashi gaisuwa a gaban Sultan.
Sultan ya ce "Na ga kamar ka santa ko?"
Ya jinjina kai ya ce "Ƙwarai uwar gijiyata ce" Sai kuma ya sauke idanunsa a kan Sayyid, ya yi murmushi ya kalli Mahmoudu ya ce "Kamar ba ka gane ni ba ko?"
Mahmoudu ya ce "Ina dai yi maka kallon sani"
Ya matsa gaban Hammad, ya zuba masa ido ya ce "Ka tuna ni?"
Hammad ya yi shiru sannan daga bisani ya ce "Na tuna ka"
"Waye ni?"
"Ba zan iya cewa ga waye kai ba, amma mun je gurinka a Nigeria"
Sarkin baka ya yi murmushi ya ce "Yanzu tunaninka kaf na zamanka a Nigeria ya dawo kana tuna komai?" Ya jinjina masa kai alamar eh.
Ya dubi Nana ya ce "Kin ga batutuwan duk da na gaya miki sun dawo ko? Kin yarda ko haryanzu kina da ja?"
Nana ta girgiza kai ta ce "Ba ta sauya zani ba, ina nan a kan bakana"
Ya ce "Babu laifi, amma an bani dama ko kuma na bar lamarin tun da na manya ne?"