← Book details Buzu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 82

Sashe 16

Buzu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka kurum bayan tafiyarsa hankalina ya ƙi kwanciya.
Kawai na kira shi na ce masa yana ina? Ya ce mini ya tafi zagaye can wajen gidan adana kayan tarihi na Agadez. Kawai na hau raƙumi na bi shi.
Sai dai na je gidan adana kayan tarihi na tarar bayanan, aka kira ni da ɓoyayyiyar lamba, aka ce mini an san Imam Hammad nake nema, ya bi cikin sahara. Ba tunanin komai na kewaya bayan gidan inda Sahrar nan take.
Na yi tafiya ta kai ta awa huɗu, saboda ina ganin sahun raƙumi a gurin. A tsakiyar sahara na ci karo da Imam Hammad cikin fita hayyaci a sume. Abin ya bani mamaki, na ciro shimfiɗa a jikin raƙumina, na yi na kwantar da shi na dudduba jikinsa na ga babu wata alama ta ciwo. Na jira ya farfaɗo ko na ɗauke shi mu koma gida.
Cikin ikon Allah ya farfaɗo, na ce masa meyasa ya taho cikin sahara haka? Ko ba shi da lafiya ne?" Ya yi mini shiru. Na ba shi ruwa ya karɓa ya sha.
Na ɗora shi a raƙumina ina mamakin yadda yanayinsa ya canza.
Muka doshi dawowa, sai dai muna nufo Agadez ya din ga wani irin ihu, ya faɗi a cikin sahara daga kan raƙumin ya din ga burgima yana kururuwa. Na sauka na riƙe shi ina tambayar ko lafiya? Amma ba ya iya magana sai ihu kawai.
Hankalina ya tashi na rasa yadda zan yi da shi. Da mun nausa cikin sahara sosai sai ya yi shiru da mun nufo gida, sai ya rikice. Na rasa yadda zan yi ga yamma tana yi. Ba zai yiwu na ɗaukko shi na taho da shi yana wannan kururwar ba kowa yana ganinsa. Kawai aka kira ni da ɓoyayyiyar lambar nan aka ce, kar na dawo Niger da Imam, idan ba haka ba zai yi hauka tuburan ƙarshe ya rasa ransa gaba ɗaya. Na tambayi waye amma ba a bani amsa ba a ka kashe wayar.
Na din ga mamakin waye wannan ya kira ni haka? Kasancewar na ga alamun gaskiya a abin da aka faÉ—a, da na juya da shi yake rikicewa, kawai sai na nufi Nigeria da shi cike da fargaba da zullumi.
Akwai abokan hulaÉ—armu na Nigeria, da muke kasuwancin asuwaki da dabino wanda da yawa ba su san waye ni ba, kuma ba su san Imam ba, kawai sai na neme su a waya. Aka ci gaba da kirana da wannan lambar ana gargaÉ—ina kar na saka a masarauta a san da abin da ya samu Imam Hammad, saboda za a ce dole sai an dawo da shi, idan aka dawo da shi kuma zai rasa hankalinsa da rayuwar sa.
Haka na ɓad da kamanni da ɓoye waye Imam, na shiga da shi Nigeria muka fara neman magani. Sai ya shafe sati bai yi magana ba, ya manta waye shi gaba ɗaya.
Sai dai aka ɓoye lambar asusu, aka din ga turo mini kuɗi cikin asusuna, na ci gaba da harkar safarar dabino zuma da asuwaki tsakanin Nijar da Nigeria, ina tsoron taɓa kuɗin da ake turo mini saboda ban san na waye ba.
Sai dai duk gurin masu magungunan da muka je, sai su ce mu yi haƙuri ba za su iya ba shi magani ba. Mun je gurin masu magunguna daban-daban amma bamu samu magani ba. Ya manta komai nasa da ya shafi Agadez.
Na samu wani gida da abokan hulÉ—ata suke gadi, muka shiga cikinsu.
Zai yi wanka zai ci abinci zai yi salla, amma ba zai yi magana ba sai jefi-jefi. Idan kuma abin ya juyo ba ya ko cin abinci ba ya magana. Sai dai gaba ɗaya al'amuransa sun ƙara rikicewa, ya din ga abu kamar yana gane-gane. Kwatsam aka kawo mahaifiyar Muhsin, ita kuma za ta din ga aikin rainon yaro. Duk lokacin da ya ganta ya kan ƙure ta da idanunsa kamar yana ganin wani abu a tare da ita. Sai da na taɓa tambayarsa ko ya santa ya ce mini a'a amma tana da wani abu da yake nema domin ya tuna waye shi.
Tsawon wannan lokacin ban taɓa gaya masa waye shi ba, saboda fatana ya tuna da kansa kuma kar na yi wani abu, da asirinmu zai tonu ko a cutar da shi.
Kwatsam! Ban san abin da ya faru ba, muka tarar da ita a sume a cikin ɗakinmu, daga ita sai shi. Babu alamun ya yi mata wani abu na cutarwa, sai dai an ce abinci aka bata ta kawo mana ta suma a ɗakin. Mahafinta ya ce ba zai yadda ba ya ce sai ya aure ta. Ba zan ɓoye maka ba Sultan mahaifiyar Muhsin yar masu ƙaramin ƙarfi ce. Aka din ga dambarwa babanta ya ce sai dai Imama ya aure ta. Ina ta lallaɓawa ina bayar da haƙuri, amma ya ce na biya masa sadakin.
Ba ni da ikon yin jayayya da shi, dole aka É—aura musu auren. Sai dai mai kirna a wayar nan ya kira ni, ya sanar mini da ya san batun auren da aka yi wa Imam Hammad.
Tun bayan aurensa da ita, ya fara samun sassauci, ya dawo yana magana, wasu daga halayensa suka canza. Yana kishinta fiye da kima, yana sakin jiki da ita ya yi hira da ita, ya yi wasa da ita abin da ba ya yi ma a rayuwarsa ta nan.
Na sani akwai abin da ta din ga ɓoye mini game da zaman da take yi da shi, duk da nima ban bayyana mata waye shi ba. Amma na san ciwon nan yana motsa masa, duk da na yi mata bayanin ciwon nasa amma iya abin da na sani. Sai dai har aka je aka ɗauke mu daga Nigeria bata taɓa nuna mini yana yin wani abu na irin wannan rashin lafiyar ba. Dan haka ko dai tana da maganin ciwon sa, ko kuma rufa masa asiri ta yi."

Sultan ya sauke wani irin nannauyan numfashi ya ce "Gaskiya na ji daɗi sosai da yadda ka rufa wasu abubuwan a gaban su Matawalle duk kusancina da su, akwai abin da ba zan so su sani ba. Amma ya aka yi ta san yana Agadez ta zo, nifa ina jin tsoron raɓa ɗa na da wanda zai cutar da shi"

"Allah ya taimake ka, neman Imam ne ya sanya ta baro Nigeria babu wanda ya sani ta taho da tsohon ciki Nijar. A hannun mahaifiyata ta zauna. Duk da ba komai na sani ba, bayan na baro Nigeria, a bakinta za a ji komai. Amma Umma ta ce mini, ta gaya mata rashin lafiya ya yi sosai bayan an É—auke mu daga Nigeria"

Sultan ya jinjina kai ya ce
"Kuma haryanzu baka san waye ya ɓoye lambar yake kiranka ba?" Ya girgiza kai ya ce "Ban sani waye ba, lokacin da aka rufe ni an karɓi wayata, da aka dawo mini da ita ma, ba a sake kirana ba"
Sultan ya É—an yi shiru sannan ya ce "Shikenan, amm zan yi magana da Matawalle, a je a taho da ita, idan ma an mayar da ita Nigeria ne, duk inda take a Nigeria a nemo ta. Amma ko waye yake kiran nan naka, yana da masaniya a kan abin da ya same shi. Amma shikenan"
Mahmoudu ya É—an yi Jimm, yana tsoron a gano Nene ta É—auke ta, dan kuwa ba ya tunanin an sake waiwayar Nana tun da aka ce a je a killace ta, dan da tuni sun farga an baza nemanta, ko dan kar ta je ta faÉ—i cewa ita matar Hammad ce. Sultan ya sallame shi ya tashi ya tafi.
Sultan ya dafe kansa ya yi shiru, saboda yadda al'amura suke ƙara rincaɓewa. Duk tarin yaransa babu wanda yake tausayi kamar Hammad. Kuma yana burin Hammad ɗin ya gaje shi, amma shi ne wanda jarrabawa kala-kala take bibiya.

*****

"Nene, wai wannan naman da nake ta ci kashi-kashi na mene ne, ni gara ki bani hatsi kawai"

Nene ta ce "To mijinki ne ya turo kuÉ—in ciyar da ke, kin ga kuwa dole na baki ingantaccen abinci."

"Ni k ƙyale masa kuɗinsa, kawai lokaci nake jira idan ba ki yi wani abu ba, na je duk bala'in da za a yi, a yi a bani ɗa na, kan na basu mamaki wallahi. Dan ko zan mutu sai na raba su da shi"

Nene ta ce "Ba ma za ki mutu ba. Za ki karɓi Muhsin, ki koma ɗakin mijinki Gimbiya, ina jinjina lamarin Ubangiji Nana, ashe duk wahalar da ki ka sha, duk zaman da muka yi Gimbiya ce ke Nana"

Nana ta ɓata fuska ta ce "Dan Allah Nene ki daina, sai na ji wani banbarakwai, ni Sayyid nake so, ba Imam Hammad ba, ko kaɗan ba na sha'awar wannan gidan. Azabar tension ɗin da na sha a baya ma ta ishe ni, yanzu hutu nake buƙata"

Nene kawai dariya tana girgiza kai, ta ce "Yaro man kaza, Nana na taɓa soyayyar nan fa nima, ba za ki yi mini wani alaye ba. Amma ni da ke mun sha banban. Allah ya zaɓa abin da ya fi alkhairi ".

Nana ta yi shiru, gaba ɗaya magungunan da Nene take bata, bata taɓa kawo na mene ne ba.
Gaba ɗaya tana kwance ta kasa bacci, sai juye-juye take yi, a jikinta take jin yanayinta ya ƙara canzawa fiye da yadda take a baya. Dama lallaɓa rayuwarta take yi a hankali.
Shiru ta yi tana tunanin ko wani hali Muhsin yake ciki?. Sai kuma ta tuna ta ji wayar da Nene ta yi da Mahmoudu a kan cewa, an sanya wa Hammad takunkumin fita. Ta tafi tunanin tun daga wane lokaci ya gane ta, amma ya share ya nuna kamar bai santa ba.
Guntun tsaki ta ja, ta juya zata gyara kwanciyarta. Ta fara jin wannan ƙamshin na ɗakin nan da take ganinta tare da Sayyid yana ratsa hancinta.
"Ina fatan ba da ni ake wannan tsakin ba?" Ba shiri ta buÉ—e idonta, kamar yadda ta yi tsammani a É—akin ta gan su sai dai ya rame sosai da sosai.

Tsiwa ta so yi masa, sai kuma jikinta ya yi sanyi ta ce "Ba ka da lafiya ne?"
Chapter 16 · 0% Book details