← Book details Buzu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 82

Sashe 37

Buzu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka Sultan ya saka Hammad haÉ—awa Asal lefe, na ban mamaki, lefe na 'yar gata. Aka yi gagarumin biki da ya tara manyan mutane, ana ta jinjina yarintar amarya da ango, dan ma dai Hammad a nutse yake sosai.
Bayan an yi aure, Hammad ya tsallaka ya tafi karatu tare da Mahmoudu, ba tare da ya sake bi ta kan Asal ba. Bayan ya zo hutu, Tafawa ya dage sai ta tare. Haka aka ginawa Hammad danƙareren gida a cikin gidan sarautar aka saka Asal a ciki.
Tun da Asal ta tare, bai taɓa gigin zuwa inda take ba, ta din ga yi masa alwashin tun da ya aure ta, sai ya ga tashin hankali da bala'i. Ta din ga surfa masa rashin mutunci da tijara iri-iri, tun yana jurewa har ya fara gaya wa Mahmoudu zai ɗauki mataki, amma ya din ga rarrashin sa yana ba shi haƙuri.
Bayan sun koma makaranta, ita ma Asal aka mayar da ita makaranta, sai dai aka kama mata gida, saboda makarantar nesa ce da Agadez. Idan ya tafi ko son tuna Asal baya yi. Saboda tashin hankali da rashin biyayya, ango na ƙiba shi kuwa ya yi uwar rama.
Tafawa kuma ya din ga nanata mata, duk wani motsi na Hammad, ta din ga sanar da shi. A haka aka shafe shekaru uku da aure, ya mayar da hankali a kan karatunsa, da ginin katafaren gurin cin abincinsa a Agadez.
Ita kuma mahaifiyar Asal ta fara saduda, tare da kwaÉ—aitawa Asal ta kwantar da hankalinta, idan Allah ya sanya ta haifi namiji, babu lallai Asadullah ya yi mulki.
Ko da suka kammala degree na farko, suka dawo Niger, Asal babu abin da ya yi mata zafi da shi, shi ma bu kula ta yake yi ba, duk inda za ta fita yawonta babu ruwanta da neman izininsa.
Wataran da daddare yana zaune a turakarsa, yana duba wasu litattafai ta yi sallama hannunta da tray. Ya amsa mata ta shiga ta ajiye masa ta ce "Ga shayi na dafa maka" Cikin mamaki ya din ga bin ta da kallo. Ya gyaÉ—a kai ya ce "To na gode" Ta na É—an murmushi ta tashi ta fita.
Bayan fitarta ya din ga kallon flask ɗin shayin, ya murza zoben hannunsa, sannan ya kalli kofin a take sai ga wani irin baƙin hayaƙi yana fitowa daga cikin kofin, shayin ya koma baƙi ƙirin mai kauri. Ya yi shiru yana mamakin yadda ƙiyayyar da take yi masa za ta sanya ta iya cutar da shi, dan tun da ya ga hakan ya san akwai wani abu a cikin shayin.
Har ta fara shirin kwanciya, ya shiga ɗakin hannunsa riƙe da kofin. Bai ce mata komai ba ya zauna a kusa da ita ya miƙa mata kofin ya ce "Sha" ta dube shi ta ce "Ai na sha"

"So nake ki sake sha ai". Ta girgiza masa kai tana kallon sa.

Ya murza zoben hannunsa ya shafi saman kofin da yatsunsa, sai ga Asal ta ga abin da ya gani a cikin kofin.

Ya sake kallon ta ya ce "Ki sha, ba za ki kashe ni nikaɗai ba" Ya yi maganar cikin tsawa. Ba ta taɓa tunanin zai yi mata kwarjini haka ba, gaba ɗaya ta rikice ta hau kuka.

"Gaya mini wane ne? Waye ya baki wannan abin ki bani, kuma na mene ne?" Ta hau girgiza kai tana kuka.
"Ki gaya mini kafin na É—auki matakin da ya dace" Ta kasa magana ta ci gaba da girgiza kai.

"Shikenan, tun da ba za ki faɗa ba, idan na kai ki gaban Sultan kya gaya masa meyasa ki ka yi yinƙurin cutar da ni" Ya fice ya bar ta a ɗakin, hankalinta ya yi mummunan tashi, ta kira lambar Abbanta amma ta ƙi shiga, ta karaya ajalinta ya zo a Agadez. Amma kwana uku shiru babu wanda ya kira ta, kuma ba ta sake ganinsa ba.
Kwana na huÉ—u har ta kwanta, ta tashi ta shiga sashensa, ta gan shi a zaune yana cin dabino yana kallon labarai. Yana ganinta ya tsuke fuska ya tashi ya bar mata falon. Ta tsaya a falon tana wasi-wasi, sai dai ta shiga lissafin halin za za ga shiga idan ya tona mata asiri, ta san duk abin da za a yi mata ba za ta iya tona wa mahaifinta asiri ba. Ta daÉ—e tana tufka da warwara ta ga dai ba ta da sauran mafita.
Dan haka kawai ta bi bayansa, gara duk wadda za a yi, a yi. Sai dai da ta shiga kawai ta tarar yana Video call da wata baturiya. Wani abu mai ɗaci ya tsirga mata ta tsaya tana kallon kyakykywar fuskarsa mai cike da ƙuruciya yana murmushi.

Ayshercool

91

Bai daina wayar ba, kasancewar malamarsa ce a faransa. Sai dai bai bari ta fuskanci hakan ba. Ta ƙarasa gabansa cikin ƙunar rai da wani abu da ta kasan gano ma mene ne a ranta. Ta je ta tsaya masa a ka. Bai kula ta ba, ya ajiye system ɗin, ya fara ƙoƙarin kwanciya. Ta zauna a gefen gadon ya ce "Imam gurinka na zo"

"An sake aiko kin ne?" Ta girgiza kai cikin sanyin jiki.

"FaÉ—i abin da ya kawo ki zan kwanta"

"Dan Allah ka yi haƙuri" shiakɗai ne abin da ta iya furtawa, ta fashe da kuka.

"Na yi haƙuri da aka yi me?"

"Abin da na yi maka, wallahi ba dan san raina ne ba"

Hammad ya ce "Ba da son ranki ba? Bayan kin gaya mini ba kya so na, ba kya ƙaunar zama da ni, sai na yi dana sanin aurenki, ai ba abin mamaki ba ne ba dan an haɗa kai da ke an cutar da ni. Amma ko ba ki kalle ni a matsayin miji ba, yakamata ki kalle ni a ɗan uwanki ki yi haƙuri mu zauna lafiya. Koma waye ya saka ki, ku sani ba zan mutu ba sai wa'adin da Allah ya ɗibar mini ya yi "

Asal ta din ga kuka tana ba shi haƙuri, dan ba ta yi zaton zai ma rufa mata asiri na kwanakin da ya yi ba.
Daga ƙarshe ya ce "Tashi ki je babu wanda zan gayawa"

"Dan Allah da gaske?" Ya tsare ta da ido, sai kuma ta nutsu ta ce "Na gode sosai da sosai, ba zan sake ba in sha Allah"

"To ban guri zan kwanta"
Ta ce "Dan Allah" sai kuma ta yi shiru.

"Mene ne kuma?"

"Dan Allah wace ce wadda ku ke waya da na shigo?"

Kawai ya kwanta ya share ta. Yana jin yadda take kuka, ya hau baccinsa, saboda haryanzu yana jin ɗacinta, a kan yadda ya iya danne abin da yake ransa ya yi wa iyayensu biyayya, amma ita fuskarta a tasa ta gaya masa, ba ta son sa ba ta ƙaunarsa.
Kasancewar ya saba baccinsa shikaɗai a ƙaton gadonsa, ya sanya shi ƙoƙarin yin juyi, amma ya ji kamar an yi masa dabaibayi. Asal ce a jikinsa tana ta bacci. Ya yinƙura zai ture ta saboda yadda ya ji shi wani iri saboda rashin sabo. Amma ta hana shi hakan."Ke ni fa kin matse ni, ki koma ɗakinki mana" Ta yi masa shiru duk da tana jin sa. Ƙarshe dai asancewar su 'yan Adam lafiyayyu, ba su bujirewa abin da gangar jikinsu ta buƙata ba.
Tun daga lokacin Asal ta ɗan nutsu, musamman da take tsoron, kar wataran ya faɗi abin da ta yi masa. Duk da ba daina tsiyatakunta ta yi ba, idan ta bushi iska tana yi. Shi kuma baya son duk wani dalili da zai sanya a ga gazawarsa ko ya yi ƙorafi a kanta.
Hankalin mahaifiyarta ya koma kan ganin Asal ta samu juna biyu, saboda zigar da Gimbiya Bilkisu take yi mata, a kan lallai ita ma ta yi ƙoƙarin ganin, 'yar ta ba ta zama abar morar Tafawa da ɗansa ba kawai. Dan ta san dole idan Asal ta haihu ta jiƙa musu aiki.
Shi ma ɓangaren Hammad, sai Allah ya jarrabe shi da matsanancin son 'ya'ya.
Gefe guda Tafawa bai fasa sanya Asal, yi wa Hammad binne-binne ba. Sai dai babban abin da yake ba shi mamaki shi ne yadda abubuwan ba su fiye tasiri a  kansa ba, har kiran Asal yake ya ƙare mata zagi, ya yi zaton ko ita ce ba ta yin aikin dai-dai, duk da wasu lokutan tana tsoron asirinta ya ƙara tonuwa.
Aka tafi shekara ta shida da aure, a lokacin ne Hammad haƙurinsa ya fara ƙarewa, saboda haihuwa yake so, kuma ba dan komai ba shi kawai yaran yake so. Duk Imam ɗin ƙasar su na da aure da 'ya'ya amma shi shiru. Ya ce wa Asal su je Asibiti a duba ko lafiya, amma ta ce ba za ta je ba, ya kaɗa ya raya ta ce ba zata ba.
Ya ce mata tun da haka ne, shi aure zai yi, ko ya mallaki kuyanga, dan saboda azabar kishinta ya sanya babu ruwansa da barorinsa.
Tun da ya faɗi haka ta hau rashin lafiya, Sultan ya je duba ta, ta din ga yi masa kuka a kan ya roƙi Hammad kar ya yi aure, yayi haƙuri tana addu'a ta san za ta haihu wataran.
Bata taɓa tunanin ta fara son Hammad har haka ba, sai da ya yi zancen aure, dan har iƙirarin kashe kanta ta yi. Tafawa ya samu Sultan har da kukan munafunci a kan ya saka baki, kar ya rasa Asal, ya rarrashi Hammad.
Ganin yadda Asal ta gigice, ya sanya Sultan ya din ga rarrashinta, ya samu Hammad ya ce "Hammad, na san kana yi mini biyayya, kuma kai mutum ne mai haƙur da juriya, dan Allah ina son ka sanya a ranka, rashin haihuwa jarrabawarku ce. Kuma ba a san me Allah zai yi nan gaba ba, dan Allah ka yi haƙuri da batun auren nan, kuma ka daina yi mata zancen haihuwar nan, saboda a samu hankalinta ya kwanta."
Chapter 37 · 0% Book details