← Book details Buzu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 82

Sashe 29

Buzu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Abin yi ɗaya, a ci gaba da addu'a, kuma ku ƙara taka tsantsan, sannan ban sani ba ko uwar gijiyata za ta nema mana alfarmar shugaba, ko akwai abin da zai iya yi a kan lamarin"
Nana ta É—an tsuke fuska tana mazewa.

"Wa za ta roƙa mana " Sultan ya yi maganar cikin damuwa.

"ÆŠan nasa mana, ai hadiminta ne, kuma babu abin da za ta saka shi, ya kasa yi mata"

Sultan ya kalli Nana ya ce "To ko za ki roƙa mana ɗin, duba da mawuyacin halin da yake shiga idan ciwon ya tashi" Nana ta yi shiru ta sunkuyar da kanta.

Sarkin baka ya ce "Kar a yi gaggwa, a bi ta a sannu tukuna, ta yanke hukunci da kanta"

Sultan ya ce "Shikenan, a mayar da kai masauki, kafin na kuma nemanka"

Nana ta ce "Allah ya baka nasara, dan Allah zan yi magana da shi, idan babu matsala a hakan" Sultan ya ce "Babu damuwa"

Hammad ya haÉ—e rai, amma Nana ta tashi ta bi shi waje.

Ta ce "Sarkin baka, dama kana raye? Ƙaisar ya ce mini kashe ka zai yi"

"Nana Asma'u, uban duƙusa bai kashe ni ba, sai dai na ji jiki kamar ba zan rayu ba. Shi ya kawo mini magani ma, sannan ya ƙara yi mini kashedi sosai a kanki. Daga nan ma har wasu magungunan ya sanar da ni"

Ta ce "Ikon Allah, sarki ya magunguna ya marasa lafiya? Ina Salamatu da wannan aljanar taka"

Ya yi dariya ya ce "Duk su na nan ƙalau"

"To ya aka yi ka san cewa asiri aka yi wa Sayyid?"

Ya harare ta ya ce "Halinki dai yana nan uwar ɗakina. Mutum mai hankali zai yi abin da mijinki yake yi ne? Abin da nake so da ke, ki ƙara addu'a kar ki yarda da kowa, kunnuwanki da idanunki su zama a buɗe komai na iya faruwa idan Allah ya taimake ki wataƙila ya samu lafiya ta hannunki"

Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Ƙaisar ya nuna mini abubuwa da dama, sai dai ba na son gazgatawa ne, na shiga ruɗani, amma har yadda asirin yake na gani, to amma idan ya rabu da Giyaz iya samun lafiya duka?"

"Ba na ce ba, tun da ban san a kan me da me aka ba shi aikin ba. Kuma ba shi da fuskar da zan tambaye shi. Amma ina jakar da na baki?"

Kafin ta amsa, Sayyid ya fizgi hannunta da ƙarfi ya yi gaba da ita.

Bai tsaya da ita ko ina ba, sai da suka je ɗakin da yake jinya. Idanunsa jawur ya ce "Dan wulaƙanci kawai ki je ki tsaya ki na surutun banza da mutumin da ba muharraminki ba"

Ta marairaice ta ce "Haba Shugaba, wa nake da shi a nan daga ƙasarmu, yaushe rabon da na ga wani wanda na sani? Kuma Sarkin baka duk da yana wasu abubuwan da nake tantama a kansu, mutum ne da ba zan taɓa mantawa da shi ba. Bayan tafiyarka daga gidansa, abubuwa da yawa sun faru, ni a gidan nasa a ka bar ni"

"Ba na son jin koma mene ne ya faru" ya yi maganar yana tsuke fuska.

Ta ce "Haba Shugaba, kar ka manta, maganinsa ya taka muhimmiyar rawa lokacin da ka yi rashin lafiya"

Yayi mata shiru yana huci, tabbas a rayuwarsu da shi a Nigeria ta san shi da azabar kishi.

Ta kwantar da murya, tana shafa bayansa ta ce "Haba Shugaba, dama mutum zai iya fushi da rayuwarsa, tuba nake É—an manyan mutane, kuma babban mutum" ÆŠan guntun murmushi ya saki, ita ma ta yi masa murmushin.

Ya ce "Yauwwa, ki yi mini addu'a, in ajima za a sanar da Asal da iyayenta, matsayinki a gurina.

Nana ta kwaɓe baki ta ce "Na yi maka addu'a, ta mutu mana, nima ban mutu ba da kishiyata ta mayar da ni baiwa saboda tana da kuɗi, ga kuma mijina ina kallonsu tare, amma ban isa na ce komai ba".

Tsam ya miƙe, saboda ya san idan aka ci gaba da jan maganar faɗa za su yi. Ya ce "Ki shirya, idan na dawo yau komai dare, za mu je gurin kayan tarihi na Agadez, kuma zan baki labarin duk abubuwan da suka faru"
Ta yi masa shiru ta cika ta yi fam, kamar za ta fashe.

Ya tausasa murya ya ce "Na san kin yi haƙuri, amma ina sake baki haƙuri, dan Allah ki saki fuskarki"

"Ni ka rabu da ni, ka je ku lallaɓa matar so, da al'adarku ta yarda da ita, ni kuma ka sake ni ku kora ni ƙasarmu" Ta yi maganar har da ƙwallar baƙin ciki.

Ya yi murmushi ya ce "Duk wata matar so a bayanki take Gimbiya Ma vie. Kin ci Agadez kin ci Nigeria" ta murguÉ—a masa baki, ya shammace ta ya yi kissing É—in bakinta.

****

Asal ce a gaban Sultan, da Matawalle da Sardauna, ga kuma Tafawa sai Imam Asadullahi, da Imam Hammad sai Mahmoudu.

Matawalle ya ce "Na san za ku yi mamakin dalilin da ya sanya, muka neme ku a yammacin nan, bayan sallar magariba haka.
Mun san za ku ji abin wani banbarakwai, amma mu ma haka nan ya zo mana. Duk ana kan dambarwar É—a da Imam Hammad yake da shi, wani abu ya sake faruwa da dole mu yi muku bayani, domin babu yadda muka iya mu ma, sai dai mu na kan tunanin matakin da za mu É—auka."

Tafawa ya ce "Mai girma Matwalle, wannan kwana-kwanar ta yi yawa, ka yi mana bayani kai tsaye."

"Kamar yadda ka yi ta bin diddigi a baya, tabbas Hammad ya yi rashin lafiya, ya kuma je Nigeria jinya. Asal na san abin da ki ka gani ya É—aga miki hankali kina ta wasi-wasi. ÆŠan da Hammad yake da shi, ba É—an kowa ba ne face É—an matar da ki ka kawo a matsayin kukunsa. Wannan kukun tasa matarsa ce"

AREWABOOKS

Wani irin nannauyan numfashi Asal ta ja, tana jin kamar daga shi ba zata sake jan wani numfashin ba. Gaba É—aya sai ta kasa gane me ma ake son a yi mata bayani. Wace ce ma kukun? Take tambayar kanta.
Tafawa ma sak ya yi, yana murza yatsun hannunsa, ya tsare su da idanu ɗaya bayan ɗaya, sannan ya numfasa ya ce "Ku na nufin Imam Hammad ya auri wata wadda ba ƙabilarmu ba, daga Nigeria har ta haifa masa wannan yaron da na gani?"

Sardauna ya ce "Haka ne"

Ya sake rausayar da kai ya ce "To ina fatan a wannan karon, za ku yi adalci dokar masarauta ta yi aiki a kansa, a yi masa hukunci daidai da abin da ya aikata."

Sardauna ya ce "Tukuna dai, sai mun ga abin da hali ya yi, saboda yanzu hankalinmu na kan samun lafiyarsa"

"Lafiya, wace irin rashin lafiya kenan yake fama da ita? Kuma me ya kai shi Nigeria? Kuma a kan me ya karya dokar masarauta?"

Matawalle ya ce "Wannan duk abu ne da za ka ji daga baya, amma yanzu a kan wannan gaɓar muke, zuwa gaba kaɗan za mu duba abin da ya dace a yi"

Wani irin kuka Asal ta fashe da shi ta ce "Hammad, abin da za ka yi mini kenan, ka munafunce ni? Ka cutar da ni, ka ajiye ni hoto ban haihu ba ka je ka haihu da wata. Saboda ka tozarta ni ba ma ka auri Buzuwa daidai ni ba sai wannan ƙazama mummunar yarinyar?"

Tafawa ya ce "Rufe mini baki, mutuniyar banza uban waye ya ce ki je ki kawo ta gidan sarauta, a matsayin kukun mijinki, alhalin kin san ba haka dokar masarauta take ba?"

Hammad ya kalli Asal ya ce "Ki yi haƙuri, na san na yi miki laifi mai girman gaske, amma ina mai baki haƙuri yadda al'amuran suka kasance ba wai da gangan na yi ba. Kin san babu yadda za a yi ina zaune haka kurum na ɗau jiki na tafi Nigeria na...

"Ka yi mini shiru, babu wata magana da zaka faɗa na yarda da kai, maƙaryaci...

"Hattara!" Matawalle ya yi mata tsawa.

"Ko me ya yi miki, dole ki ambace shi da girmamawa kar ki kuskura ki faÉ—i wani abu mummuna a kansa, ko me ya yi kuwa. Dan haka ki kiyaye harshenki"

Cikin kuka take cewa "Wallahi sai ka sake ni, ba zan zauna da kai ba, kuma na bar ka da Allah sai ka sake ni"

Sultan ya yi gyaran murya ya ce "Yarinyar kirki, na san za ki ji abin wani iri, amma babu abin da zai raba aurenki da Imam. Haryanzu mu na kan tattauna matakin da za mu É—auka amma sai kin bamu cikakken haÉ—in kai kin nutsu. Haryanzu ke ce halattacciyar matar Imam da kowa ya san da zamanta."

A fusace Tafawa ya tashi ya kalli Asal, da gaba ɗaya ta rikice take kuka ya ce "Ke tashi mu tafi" Ta yinƙura ta tashi ta yanke jiki ta faɗi.

Hammad ya taso da sauri ya nufo ta, amma Tafawa ya ce "Kar ka kuskura ka taɓa mini 'ya" Ya kalli Asadullah ya ce "Zo ka ɗauke ta mu tafi"

Hammad ya ce "Ba zai yiwu ba, ba zai ɗauke ta ba. Kar ya fara taɓa mini mata"

"Ni ka ke gayawa kar ya fara taɓa maka mata?"

"Ni nake da hurumin ɗaukarta, ko na taɓa ta ban yarda ya taɓa mini mata ba" Ya yi maganar yana tsare Tafawa da ido.

Sardauna ya ce "Tafawa ko da an samu rashin fahimta, bai kamata a ce ka hana shi taɓa matarsa ba, sai ka gama wannan ɓaɓatun ita kuma ta baka kunya, ai ba a shiga tsakanin mata da miji. Bari a kira barori mata su zo su ɗauke ta, a kai ta ɓangaren Gimbiya Bilkisu"

Ya ce "Babu wanda ya isa, ba wanda zai taɓa mini 'ya"

Sultan ya ce "Umarni ne, a kaita sashen Gimbiya Bilkisu, idan ta farfaɗo ta ɗan nutsu sai a kai ta gida" Tafawa ya tsaya cak yana kallon Sultan cikin ƙunar rai. Ƙaninsa yana ba shi umarni kuma dole ya bi.
Chapter 29 · 0% Book details