Sashe 59
Buzu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Matawalle ya ce "Amma Allah ya baka yawan rai, yanke wannan hukuncin haka kai tsaye, baka tunanin zai sanya wa talakawanka wasi-wasi da kawo tashin tashina a tsakanin masarauta da kuma jama'ar gari"
Sultan ya numfasa ya ce "Lokuta da dama, gyara baya buƙatar lallai sai ka yi wa wani daidai, ko kuma sai kowa ya soka, ya yarda da kai mai gaskiya ne ko me kirki ne.
Haka zalika zan sauke wasu daga cikin Imam Imam na ƙasar nan, zan yi wa dokokin Agadez garambawul da gudunmuwar dokokin ƙasar Niger, domin kowane ɗan Agadez ya samu cikakken 'yanci kamar sauran ɗan ƙasa ba tare da al'ada ta tauye wasu daga cikin 'yancin da suke da shi ba a ƙasar nan.
Sai dai na san da yawa ba zai yi muku daɗi ba, za a ga kamar na yi rashin adalci saboda Hammad ɗana ne, amma kafin ku ce haka, bari mu yi komai a buɗe tare da ku". Ya kalli wani dogarinsa, ya ce "Ina da baƙo a mararrabar fada da hanyar cikin gida, ka ce ya iso"
Duk suka yi tsuru-tsuru su na jira.
Ba a jima ba, dogarin ya dawo tare da Sarkin baka sai kuma wannan mai gadi a ɗaɗɗaure da igiya tamau kamar ɓarawo.
Wanda ba su san me ake ciki ba, suka yi ƙuri su na jiran jin ba'asi, wanda abin ya shafa kuma cikinsu ya ɗuri ruwa.
Sarkin baka ya risuna ya yi gaisuwa a fada, cikin shigarsa ta hargi ya shigo hakan ya ƙara sanyawa duk aka zuba masa ido.
Sultan ya kalli Sarkin baka ya ce "Yi musu bayani"
Sarkin baka ya kalle shi ya ce "Duk da na san, sun sanka amma ka yi musu bayanin waye kai"
Ya sunkuyar da kai ya ce "Mai gadin gidan tarihin Agadez"
Sarkin baka ya ce "Kuma me?"
"Boka da nake yi wa wasu daga cikin manyan Agadez aiki"
"Mene ne dalilinka na yin hakan?"
Ya numfasa ya saci kallon Sultan ya ce "Na haka ne, saboda huce takaicin yadda ake bautar da mu tun daga kan kakana, wannan dalilin ya sanya lokacin boka Riyan, na koyi harkar bokanci a gurinsa"
Sultan ya ce "Ina fatan kun ga É—aya daga cikin illolin wannan al'adun da muke yi, marasa tsuhe balle makama? Mu na jinka ci gaba"
Sarkin baka ya ce "Ba ka ji ka ci gaba mana"
"An bani wasu ayyuka, duk da ba kowa ya san ina bokanci ba, sai dai akwai wani babba a masarautar nan da shi ya ƙarfafe ni na koyi harkar bokanci.
Ni aka saka na yi wa Imam Hammad Asiri, da aljanin da ya sanya ya bar ƙasar nan, ya manta komai da ya shafe shi, ciki hadda tuna waye shi.
Sannan aka bani aikin yi masa asiri da wani tsohon aljani a cikin gidan tarihin, da yake sanya masa wannan zafin jikin da yake gigita shi".
Sarkin baka ya sake cewa "Yaya ka ke yi?"
"Da fari na haƙa rami a cikin tsohuwar kurkuku, ana kawo mini itace cikin dare, ina tona tsofaffin kabarurruka na cikin gidan, na ɗauki ƙwarangwal ɗin, na saka shi a cikin wuta, da hatimai daban-daban da sunan Imam Hammad, duk lokacin da na babbaka wannan wutar yadda ƙwarangwal ɗin nan yake ƙonewa haka yake jin zafin a jikinsa. Idan ƙwarangwal ɗin ya murmushe saboda zafin wuta, sai na kuma tono wani. Daga baya kuma aka koma kawo mini sababbin gawarwaki na koma yin aikin da su, idan na saka musu wutar nan, haka yake jin wannan zafin a jikinsa"
Gurin ya yi tsit, aka rasa wanda zai yi magana. Jikin Matawalle yana rawa ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, amma suwaye haka?"
Sultan ya ce "Ba sai an faɗe su ba, amma sun san kansu, kuma duk wanda yake da ja a kan maganar, yana iya zuwa gidan tarihin da kansa ya tabattar. Dan haka a yau na kawo ƙarshen zaman yau, dan haka zan zo da sauran bayani da abubuwan da zamu caccanza".
Nan aka ci gaba da salallami, aka rasa mai sake cewa komai.
Nana tana kwance tare da Hammad, kamar zai shige cikinta, sai shafa gashin sa take yi sannu a hankali.
Ta yi shiru tana tunanin abin da ya faru.
Yadda bokan nan ya din ga yi musu bayanin, Imam Omar da mahaifinsa Sardauna, suke zuwa da yadda suka yi masa asirin nan na zafin jiki. Kuma da sanin Tafawa, kowa fafutukarsa É—ansa ya samu mulki. Haka zalika Asal ta yi soyayya da Omar, ita take ajiye wa Hammad takardun nan. Ko da auren Hammad sun yi soyayya tare, kafin daga bisani da ta ga babu amfani soyayyar tasu, ta fara son Hammad ta daina biye masa.
Sai dai ya ci gaba da yi mata barazanar sai ya tona mata asiri, irin hirarrakin da suke yi. Sai dai babu wani abu na saɓon Allah da ya taɓa shiga tsakaninsu, sai dai duk wasu zantuttuka na banza har da wanda bai kamata ba, suna yi. Babu abin da bai sani ba a game da aurenta, da abubuwan da yake faruwa tsakaninta da Hammad ba.
Hatta sirrin shimfiÉ—ar aurensu, babu abin da Omar bai sani ba. Shi ya din ga ziga ta, tun daga lokacin da aka ce za a yi aurenta da Hammad, shi ya din ga ziga ta har bayan auren.
Ya ci gaba da zuwa gurin bokan nan, yana karɓar wannan takardar, yana bawa Asal, wanda da ya yi tozali da takardar yake sake ruɗewa, jikinsa ya rikice ya yi ta jin ihun da alajanin nan yake yi a jikin ƙwarangwal ɗin nan, duk ya fita hayyacinsa.
Babu yadda Omar bai yi da Bokan nan, ya yi masa abin da Asal za ta yarda shi, amma ya ce ba zai yi wannan cin amanar ba saboda Hammad yana yi masa alheri ta wasu ɓangarorin. Gaba ɗaya bokan ya gaya musu labarin, da abin da yake tsakanin Omar da Asal a baya.
Babban abin da ya ɗaga wa Nana hankali, bai wuce yadda bokan ya ce, ko za su kashe shi, zai iya lalata sihirin da ya yi da aljanin jikin ƙwarangwal ɗin da yake amfani da shi, amma ba zai iya raba Hammad da Giyaz ba, saboda Giyaz baya saɓa alƙawari, kuma ga Nana tana tare da Hammad, yana ganin ɗansa a jikinta, idan ba kashe Giyaz za a yi har lahira ba, ba zai rabu da shi ba.
Da ta zo nan a tunaninta, ta lumshe idanunta hawaye na zirarowa a hankali.
Hammad ya yinƙura ya tashi zaune, ta maze ta goge hawayenta. Ya ƙare mata kallo ya yi wani irin tattausan murmushi, ya shafa gashin kansa ya ce "Ba ƙaramin kyau ki ka yi mini ba ma vie, ina kewa, ɗan yi mini waƙar mana abar ƙauna" Yayi maganar yana sumbatar hannunta, tare da matsawa kusa da ita.
Ta É—an matsa kaÉ—an ta ce "Ana ta kai ka na ta kaya"
"To ni kayan ne suka fi damuna, fiye da kayan ai. Ki kwantar da hankalinki babu abin da zan yi miki, kuma ina roƙon Allah kar ya kama ki da laifin guduna da ki ke yi, saboda kin fi ni gaskiya ta kowace fuska.
Amma har abada ni mai ƙaunar ki ne, kuma ba zan taɓa yarda a raba ni da rayuwata ba in sha Allah" Ya yi maganar yana sake rungume ta, wani abu mai sanya nutsuwa na fizagarsa game da ita.
"Ka daina yi mini wannan kallon mana" Ta yi maganar tana hararasa cikin wasa.
"Idan ban kalle ki ba wa zam kalla, kina nan a yadda ki ke ma vie, kamar baki haifi Muhsin ba"
Ta ɗan ɓata fuska ta ce "Da na canza daina sona za ka yi kenan?"
Yayi murmushi ya ce "Haryanzu ba ki san waye Hammad ba, ke É—in nake so ne Asmy, babu abin da zai canza a tattare da ke, na ji na daina sonki ko kaÉ—an. Ina son Husna"
"Sake faÉ—a" Ta yi maganar tana tsare shi da ido.
"Sai kin yi mini waƙa tukuna" Ta yi dariya tana jan hancinsa ta ce "Sai ka biya ni tukuna."
Ya É—an yi shiru ya ce "Ina tuna mutane daban-daban da muka rayu da su a Nigeria, ko ina yayarki É—in nan, da ta yi ta É—awainiya da mu? Da 'yan gidanku, da mutumin nan da na tsana, wanda na yi wa gadi da farko. Sai kuma mutanen gidan da muka zauna, da muka yi aure"
Nana ta ce "Gidansu budurwarka ko?"
Ya ce "Eh nan"
"To tashi daga jikina"
Hammad ya ce "Ba zan tashi ba, ai ni ban ce budurwata ba, ke ki ka fara."
Ta yi murmushi ta ce "Babu abin da ba zai wuce ba sai ikon Allah, ni dai ina ta zaman jiran tsammanin abin da za a yanke a kanmu"
Ya ce "Alkhairi in sha Allah, ni nama manta, yana nemanmu anjima, ban san me zai ce mana ba. Amma ina tsammanin alkhairi daga bakinsa"
"Allah yasa ina fatan hakan nima, amma dan Allah ka sanya baki, na ga ya yi fushi sosai da sosai da É—an uwanka, ko zaka saka baki?"
"Ba ruwana" Ya bata amsa kai tsaye.
Nana ta ce "Kar ka ce haka" Ya miƙe tsaye gaba ɗaya, sannan ya ce mata "Zan je na dawo, ki yi mana addu'a Allah ya sanya hukuncin da Sultan zai yanke, ya yi mana daɗi"
Ya ƙarasa maganar yana sumbatar goshinta.
Kamar zata tashi sama, haka Gimbiya Bilkisu ta faÉ—o turakar Sultan hankalinta a tashe, ko haÉ—iyar yawu ta kasa, saboda bushewar da bakinta yayi.
A nutse ya juyo ya kalle ta, bayan ya gama warware rawanin kansa.
Sai kuma ta tsaya ta kasa magana.
Can kuma ta ce "Sultan, wai da gaske zaka sauke wasu daga cikin Imam? Meyasa? Kuma ina fatan babu Zahradeen a ciki?"
"Idan da shi me za ki yi?"
"Amma dai ka san bai kamata abin da ka yi, kuma a kan me zaka sauke Zahradeen yana ɗan cikinka? A wancan karon ka naɗa ƙaninsa a matsayin shugabansa, sannan ka zo ka sauke shi ai muzantawar tayi yawa. Zai ma zama abin surutu a Agadez"