← Book details Buzu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 82

Sashe 58

Buzu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sarkin baka ya numfasa ya fito da jakar nan tasa, ya nuna wa mai gadin nan,ya ce "Idan hatsabibancinka ya kai ya kawo, na san ka san wannan jakar, ko kuma ka ji labarinta, mussaman da Jaddul Jinn ya yi rayuwa a cikin Masarautar nan. Wannan jaka ce da uwar gijiyar Ƙaisar ta farko, Lanti ta haɗa, da gudunmawar uban duƙusa, ta hanyar yin amfani da wani sashi na gashin Jaddul Jinn. Da abubuwa daban-daban da baƙaƙen aljanu ba sa so. Ana iya yi wa aljani tarko da ita, ko ma halaka su baki ɗaya. Yanzu za ka yi mana bayani ne, ko kuma na gwada maka aikin jakar nan, na hallaka baƙin aljanin kanka, na haɗa ka faɗa da Giyaz, sannan na kashe ka?"
Ya din ga kallon Sarkin baka, yaƙi magana. Nana ta ji sanyi ya fara ratsata.
Mai gadin ya ɗan ja da baya yana kallonta. Ta waiwaya ta ga me yake kallo, kawai ta ga Ƙaisar a gurin.
Jikinsa na rawa ya nufi ƙofar ɗakin, ya ciro wani mukulli ya buɗe, yana buɗewa wani irin wari ya daki hancinsu suka ja da baya.
Jikin Nana ya hau tsuma, Shi kansa Sultan ja ya yi da baya cikin tsoro, yana kallon gurin.
Sarkin baka ya tankaɗa ƙeyar mai gadin nan, suka shiga ɗakin. Ɗakin duhu kafin daga bisani kawai su ga haske ya gauraye ɗakin.
Sarkin baka ya waiwaya ya cewa su Imam Zahradeen su shiga.
Suka bi wata doguwar hanya, su na shiga suka wari yana ƙara cika musu hanci.
Ɗakin tsohuwar kurkuku ce, da daga baya a ka mayar da ita gurin aikin zinaren da ake haƙowa. Wannan kurkukun da aka din ga azabtar da mutane a zamanin sarakunan baya.
Gurin gwanin ban tsoro babu kyawun gani ko kaÉ—an.
Nana ta kurma ihu ta ja ta tsaya jikinta yana tsuma, saboda razana da kuma firgicin abin da ta gani.
Ƙwarangwal ne na cikakken mutum, an soke shi a jikin mashi, an kuma soke wani abu mai kama da takarda a jikin ƙwarangwal ɗin, da hotonsa a jiki yana ci da wuta, sai kuma sunan Imam Hammad Jalaludeen, a jikin abin mai kama da takarda an soke allurai a jiki. Sak abin da ta gani a cikin mudubin Ƙaisar. Jikinta ya din ga wata irin karkarwa, saboda razani da tsoro.
Shi kansa Sultan daskarewa ya yi yana rarraba ido, saboda razani da tsoro.
Sarkin baka ya ƙarasa gaban ramin, ramin ba mai zurfi ba ne ba, sai dai wasu irin manya-manyan itace ne a cikin ramin nan. Ya kalli jikin ƙwarangwal ɗin nan, ya yi baƙiƙirin saboda azabar wuta.
"Ya ka yi wannan sihirin?" Sarkin baka ya yi maganar yana tsare shi da ido.
Ya yi shiru.
"Wallahi idan baka faÉ—a ba, sai na jefa ka a ramin nan na kunna wutar"
Ya tsaya ya kalli ramin, ya rufe idanunsa ya faɗi wasu abubuwa, ya kalli ramin a take wata irin wuta ta tashi a cikin ramin. Wata irin ƙara ta din ga tashi a cikin ɗakin. Nana ta toshe kunnenta, ta durƙushe a kan gwiwoyinta, ta toshe kunnenta, ta fashe da wani irin kuka na tashin hankali da gigicewa.
Sarkin baka ya ce "waye ya saka ka wannan aikin, kuma yaya aka yi kana mai gadi ka ke bokanci?"
Ya numfasa ya ce "Na koyi bokanci ne, domin na rama abubuwan da aka yi wa zuriyarmu. Na bautar da mu tun zamanin kakanni.
Nana ta fara neman ta burkice musu gaba É—aya, saboda sama-sama da numfashinta ya din ga yi.
A rikice Sultan, ya ce Zahradeen ya fitar da Nana, kar wani abin ya same ta.
Su na fita ta nemi guri ta zauna ta sauke numfashi cikin matsanancin tsoro da razani.

*****
Mama ce a gaban Likita kamar ta yi kuka, ta yi ƙasa da murya sai magiya take yi masa.
Ya kalle ta ya ce "Hajiya muddin ba ki gaya mini gaskiyar abin da ya faru ba, babu wani abu da zan iya yi a kan 'yarki"
Cikin damuwa ta ce "Likita ka san ɗan yau ne, ka haife shi amma ba ka haifi halinsa ba, abin kunya ta kwaso mini, na yi na yi da ita a zubar ta ƙi, shi ne aka gaya mini wata ƙwaya na je na karɓo aka ce na saka mata guda goma a cikin kunu zai fita."
Ya yi zuru da ido yana kallonta, ya ce "Amma baiwar Allah ba ki da imani, kin san abin da ki ka aikata kuwa?"
"Dan Allah likita ka yi haƙuri,  ka taimake ni kamar yadda Allah ya taimake ka" Sai da ya yi mata faɗa kamar zai yi mata duka, sannan ya rubuta abin da za a yi wa Jamila.
Hajiya Sa'a kuwa, ta daina magana gaba ɗaya, komai sai an yi mata. Ƙarshe Asibiti aka sallame ta, ta koma gida, gidan kuma babu mai jinyarta, abin duk ya damu Alhaji Fatuhu amma babu yadda ya iya.

*****

Nana har wani irin jiri take yi, jikinta yana tsuma saboda tsoro da razanin da ta shiga.
Sultan ya ƙi kallon inda Zahradeen yake, zai ɗauki Muhsin ya tafi da shi, amma ya yi masa tsawa ya ce kar ya taɓa shi.

Gimbiya Bilkisu sam ba ta san me yake faruwa ba, da daddare ta shiryo ta zo sashen Sultan. Yana zaune a gefen gado ya yi shiru, ji yake yi tamkar kansa zai tarwatse.
Muhsin yana kan makeken gadon Sultan yana bacci, gani yake yi idan ya kawar da ido daga kan yaron, shi ma cutar da shi za a yi, wani irin matsanancin tausayin Hammd ya hana shi sukuni. Da ya rufe idanunsa ya tuna abin da ya gani, sai tsigar jikinsa ta tashi.
"Ranka ya daÉ—e, ko nan zan kawo maka abincin daren naka ne, barori sun shirya maka abinci tun É—azu fa" Bai yi magana ba, ta mayar da idonta kan Muhsin ta ce "Wannan kuma a ina ka samo shi?" Ta yi maganar tana nufar gadon.
Cikin tsawa ya ce "Kar ki kuskura ki taɓa shi" Ta razana ta ce "Sultan lafiya?"

"Fita ki bani guri"

Cikin rashin fahimta ta ce "Me yake faruwa ne?"

"Na ce ki fita ki bani guri, ba na ko ƙaunar ganinki, ki fita kafin na ɗauki mummunan mataki a kanki" Babu shiri ta juya ta fice, ganin yadda jikinsa har rawa yake yi, saboda tsananin ɓacin rai. Ta din ga mamakin mene ne ya tayar masa da hankali ne har haka, yake wannan fushin?.
*****
Nana kuwa tun da suka baro gidan tarihin, Sultan ya ce ta zauna a É—akin nan da suke, ta samu nutsuwa.
Da kyar ta samu ta iya yin salla.
Tana zaune ta yi shiru, ta ga an buɗe ƙofar ɗakin, Hammad ta gani ya shigo, ba ta yi zaton ganinsa ba ko kaɗan. Ta miƙe tsaye ya ƙaraso fuskarsa ya zauna a kusa da ita, ya jingina da jikin gado. Sai kuma ya ɗago ya kwantar da kansa a jikinta.
Nana ta ƙara janyo shi jikinta, ta ƙanƙame shi tana fashewa da kuka, wani irin tausayinsa ya mamaye zuciyarta.
"Ya aka yi ne rayuwata, kukan me ki ke yi" Ya furta a hankali yana ƙara shigewa jikinta.
"Sonka kawai nake yi" Ta yi maganar tana kuma ƙanƙame shi.
"Wannan kukan, ya fi kama da na wanda ake tausayawa, meyafaru ki gaya mini"
"Ba komai Sayyid"
"To idan dai kina so na sosai, É—an bani sanyin mana" Yayi maganar yana É—an shafa jikinta yana murmushi.
Jin da gaske kukan take yi, ya sanya ya ɗago, shi ma idanunsa jawur, jikinsa babu ƙwari ya ce "Ki gaya mini, ko wani abin su Sultan suka ce miki?"
"A'a"
"Mene ne?"
"Dan Allah Sayyid duk abin da za a ce maka Asal ta yi, ka yi haƙuri ka yafe mata"
Ya yi murmushi mai ciwo, ya ce "Me Asal É—in ta yi?"
"Na san sai Sultan ya gaya maka, amma dan Allah ka yafe mata"
Hammad ya ce "Ki na tunanin ban san komai ba ne? Lokaci ya yi da yakamata na huta"
Nana ta ce "Wataƙila akwai abin da baka sani ba, dan Allah ko ka sani ka yi haƙuri ka yafe mata"
Ya yi shiru ya sake kwanciya a jikin Nana, ta ƙara ƙanƙame shi, cikin matsanancin tausayawa.

*****

Sultan na kashingiÉ—e, yana sauraren Tafawa, da sauran 'yan majalissa, sun kafe kai da fata a kan lallai a san matakin da za a É—auka a kan Hammad, saboda yadda ya karya musu Al'adar masarauta.
Sultan ya ɗago ya numfasa cikin ƙasaita, kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya ce "Amm kamar yadda kowa ya sani, Agadez ta gaji Al'adu da ƙa'idoji daban-daban, wanda wasu an samar da su ne, tun zamanin jahiliyyah kafin zuwan addinin musulunci, ina ga lokaci ya yi da yakamata mu kama addininmu, mu yi watsi da duk al'adun da muke ganin su na kawo mana koma baya.
Saboda haka a matsayina na Sultan mai ci na wannan lokaci, na soke wannan Al'ada a ƙasar Agadez. Baƙaƙen buzaye za su samu 'yanci, farin buzu ko buzuwa na da cikakken 'yancin auren duk wata ƙabila ko kalar fatar da yake son aure. Matar da Imam Hammad ya aura, bincikenmu ya tabattar da halattaccen aure suka yi, kuma mun karɓe ta. Hakazalika za mu bayyanawa duniya ɗan da ya haifa tare da matarsa ta Nigeria.

97
1k ne via 0069685771
Aisha Adam stanbic
08081012143

Gaba É—aya 'yan majalisar suka waiwayo suna kallon Sultan.

Tafawa ya ce "Jalaludeen wannan wace irin maganar banza ce, dan me zamu bar gadon al'adun da muka gada daga iyaye da kakanninmu saboda son zuciyarka da ƙoƙarin bawa ɗanka kariya? Babu wanda zai lalata mana dokokinmu da al'adunmu. Dole a hukunta Hammad dai-dai da abin da ya aikata"

"Mutanen farko ma, gadon iyaye da kakanni ne ya halakar da su. Daga lokacin da muka gaji al'adun, zuwa yanzu me al'adar ta haifar mana bayan tarin ɓarna kashi-kashi? Kuma ina bayar da wannan umarni ne a matsayina na Sultan, shugaba a Agadez ba magana nake yi ba a matsayin ɗan uwanku ko abokinku ba, duk wanda ya ɗaga murya ko kawo abin da ba shikenan ba, zan hukunta shi dai-dai da abin da ya aikata"
Chapter 58 · 0% Book details