← Book details Buzu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 82

Sashe 45

Buzu Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Mahmoudu ya karɓi wayar ya ce "Zan tura maka" Gaba ɗaya jikinsa ya yi sanyi, ya kuma kasa shan shayin. Sule ne ya zo gurin a kan babur, ya kafe baburin, ya sauka ya gaida Hammad cikin girmamawa. Hammad dai ya amsa yana bin sa da kallo.
Suka gaisa da Mahmoudu ma, ya ga sun sake sun fara hira. Mahmoudu yana ta satar kallon Hammad, ko zai É—ago ya tuna wani abin, amma ya ga babu alamar hakan. Bayan tafiyar Sule, yake gaya masa ai abokin kasuwancinsa ne na Nigeria. Kawai ya jinjina kai.

Ƙaisar ne ya bayyana a gaban Giyaz, fuskarsa babu annuri ko kaɗan. Giyaz ya ɗaga kai ya kalle shi, ya ce "Ɗan samari ya dai?"

"Zuwa yaushe zaka ci gaba da wannan mugun wasan da ka ke yi?"

Giyaz ya ce "Wanne daga ciki?"

"Kowanne ma? Ka dawowa da mutumin nan tunaninsa ya tuna da yarinyar nan, ga ɗa a tsakaninsu ko iya yanzu ka ɗauki fansar ai, ka ƙyale ta ta huta haka?"

"Yaro yaro ne. Yarinyar da kakaninta suka cutar da mu, ta zo ta ƙona ni ta sanya ni jinya, ita ka ke tunanin na ɗagawa ƙafa ma sassauta mata?"
"Ba na son alaƙata da kai ta ƙara tsami, amma zan yi abin da ba ka zato, ba zan zuba ido ka ci gaba da cutar da ita har haka ba" Ƙaisar ya yi maganar cikin ƙunar rai.
Giyaz ya ce "To babu laifi, ka yi abin da duk za ka yi"

Hammad kuwa da ya koma gida, ya kasa zaune ya kasa tsaye, hoton yaron nan ya din ga kaiwa da komowa a cikin kwanyarsa. Yaya za a yi a ce a samu yaro yana irin wannan kamanin da shi, ba kamanni sama-sama ba, kamanni na zahiri nesa ba kusa ba. Bayan haka yaron ya yi masa kama da wani wanda ya sani ko ya taɓa gani, amma ya manta waye, ya din ga duba wayarsa ko Mahmoudu ya turo masa hoton yaron, amma wayam bai tuta masa ba.
Gefe guda ya so haÉ—uwa da Nana, amma bai ganta ba. Sai washegari da ta kawo masa Abincin safe ta yi masa ya jiki.
Ya ce "Sai yanzu za ki yi mini ya jikin?" Ya yi maganar yana tsare ta da manyan idanunsa, saboda wani irin kyau da ta yi masa. Ga ƙamshin da take yi, har wani ƙara nutsuwa ya yi yana kallonta.
"Tuba nake ranka ya daÉ—e" Sayyid É—in da take kiransa da shi, ya din ga kaiwa yana komowa a cikin kwanyarsa.
Haka da rana da ta yi shigar Atamfa, kamar ya sace ta ya gudu. Ta karya É—aurin É—an kwali, ta yi kyau.
Ya ce "Amm Asma'u ko?"
Ta jinjina masa kai duk da yadda ta ji Asma'un banbarakwai a bakinsa.
"Cherié ta ce mini a gidan cin abinci na Maraɗi ta ɗaukko ki ko?"
"Eh Sayyid"
"Me ya kawo ki Niger ne? Ko takanas ki ka nemi aiki da mu, tun daga Nigeria?"
Nana ta girgiza kai ta kalle shi ta ce "Abuna ne ya ɓata na zo Niger neman sa, ina son a yi mini izini, nan kusa na koma Nigeria"
Ya jinjina kai kawai ba tare da ya gama fahimtar abin da take nufi ba.
A daren ne kuma Nana ta jiyo kakarinsa, Asal ta fice ita kuma ta shiga É—akin.
Ƙara lafewa ya yi tamkar ya shige cikin ta, saboda daddaɗan sanyin da ya mamaye jikinsa. A hankali ya buɗe idanunsa, ya ji yadda ta ƙanƙame shi tana kuka. Ya saurara ya yi shiru ya ji ba muryar Asal ba ce. "Allah ka duba mu, ka yaye masa wannan ciwo, Allah ka yi masa maganin abin da yake damunsa. Yana jin yadda take shafa gashinsa tana ci gaba da kuka tana faɗin "Da gaske ba ka gane ni ba Sayyid, ko kuma wasa ka ke yi mini da hankali kawai. Na fara sarewa Sayyid, idan wasa ne ka tausaya mini haka, wahalar da na sha ta isa, ka duba ni ka duba makomar abin da na haifa maka dan Allah" Ta yi maganar tana ƙanƙame shi tana ci gaba da kuka. Gaba ɗaya sai ya rikice, bayan kukanta da maganganun da take yi da suka rikita masa lissafi, gangar jikinsa kuma wani saƙon take aika masa na daban, har wata tsuma ya fara yi. Sai dai Allah ya taimake shi, bai yi wani yinƙuri ba, ya ji tana magana da Ƙaisar, ta kwantar da shi a kan pillow ta koma gefe.
Tunani ya din ga yi ina Asal ta tafi? Ya aka yi Nana ta shigo har turakarsa kai tsaye haka, kuma wasu irin maganganu take yi haka? Ya yi lamo kamar bacci yake yi, amma idonsa biyu.
Sai gefin Asuba da ta bar ɗakin, ya tashi ya zauna, yana jin wani irin raɗaɗi a tsakiyar kansa, zuwa ƙirjinsa gaba ɗaya ji yake kamar zai fita hayyacinsa ƙwaƙwalwarsa na nema ta hargitse.
Garau ya miƙe bayan sallar asuba, ya sake tuna yaron da Mahmoudu ya nuna masa, da maganganun da ya ji Nana tana yi. Ya kira Al Hussain a waya, ya ce masa lallai yana son cikakken bincike a kan Nana.
Ga Sultan ya tura shi wakilicin wani É—aurin aure, amma kusan baya cikin cikakken hayyacinsa, kansa cunkushe da lissafi kala-kala. Maganganun Nana suka din ga karafkiya a cikin kwanyarsa, da rungumar da ta yi masa ba tare da tsoron komai ba.
Ko da ya dawo, har ya wuce É—akinsa, amma kansa ya din ga wani irin ciwo, kawai ya yanke shawarar zuwa ya turke Nana, ta yi masa bayani dalla-dalla.
Sai da ya bari Asal ta yi bacci, sannan ya tashi ya tafi É—akin Nana. Sai dai da ya je É—akin ya tarar ba ta ciki, sai wayarta da take kan katifarta a ajiye.
Har zai juya ya fita, kawai ya nufi kan katifar ya sanya hannu ya ɗauki wayar. Ya jujjuya wayar, yanayin yadda screen ɗin wayar ya dusashe ya sanya ya gane wayar ta kwana biyu. Kawai ya danna madannin gefe a take hoton fuskar Nana da Muhsin ya bayyana a kan screen ɗin wayar. Mutuwar tsaye ya yi zuciyarsa ta yi wani irin mummunan bugawa da ƙarfin gaske. Alamun tahowar Nana ya ji, babu shiri ya jefa wayar kan katifar ya yi sauri ya kashe fitilar ɗakin.

AREWABOOKS

Ko da Nana ta shigo É—akin, jikinta ya bata akwai mutum a ciki.
Da ta kunna fitilar ta yi arba da shi, ta rikice ta kusa kurma ihu, sai dai duk da a tsorace yake shi ma, amma  kasancewar sa Namiji ɗan gwagwarmaya ya sanya ya danne tsoronsa da tashin hankalin da yake ciki, ya yi mata duk tambayoyin da ya yi mata, sai dai bai tambaye ta haƙiƙanin abubuwan da yake son tambayarta ba. Duk amsoshin da ta ba shi, ba su gamshe shi ba, haka ya fice ya bar ta.
Tun da ya bar ɗakin kusan kwanan tsaye ya yi, ya din ga kaiwa yana komowa a ɗakinsa ya dafe kansa, ya zauna ya tashi. Duk wani lissafi da ya yi sai ya ji babu mafita. Shi dai bai taɓa ganin Nana ba, amma meye haɗinta da yaron da Mahmoudu ya nuna masa? Sannan mene ne alaƙarta da shi da ta iya shiga turakarsa ta rungume shi take faɗar wannan maganganun da suke nuna da alaƙa a tsakaninsu.
Har aka yi kiran sallar Asuba ko gyangyaÉ—i bai yi ba.
Da Asuba da ya dawo daga masallaci, har zai wuce hanyar ɗakinta, ya koma ya nufi ɗakin nata. Ya jima a gurin yana kallon ƙofar. Ya buɗe ƙofar ɗakin a hankali. Ya tarar da ita tana bacci. Sai dai abin da bai sani ba, Ƙaisar ne ya ƙara wa Nana nauyin bacci, amma duk abin da yake faruwa tana gani, sai dai ba za ta iya motsi ba. Cikin sanɗa Hammad ya ɗauki wayar ya yi waje.
Bai ko sake nufar É—akinsa ba, ya fice. Gidan Mahmoudu ya tafi, ya je ya tarar da shi a zaune yana lazumi.
Sai da Mahmoud ya tsorata ya ce "Lafiya na ganka da duku-dukun nan?"

"Mahmoudu wane ne yaron nan da ka nuna mini? Kuma wace ce yarinyar da Asal ta kawo a matsayin mai yi mini girki?"

Mahmoudu ya kalle shi ya kalli screen É—in da yake nuna masa, tabbas Nana ce ba wata ba, amma zai so ya yi magana da Nana kafin gaya wa Hammad wani abu.
"Ka yi magana ka tsaya ka na kallo na" Ya yi maganar cikin hasala.

Mahmoudu ya ce "To ai Asal yakamata ka tambaya ba ni ba, ni fa cin karo kawai na yi da hoton na nuna maka"
Zai yi magana kansa ya sara, ya saki wayar ya fara ja da baya yana dafe kansa, ya tafi zai faÉ—i Mahmoudu ya yi saurin tare shi, ya kwantar da shi a hankali.
Ya É—auki wayarsa ya kira Al-Husssain. Bayan sun gaisa Mahmoudu ya ce "Imam Hammad ya yi maka magana a kan yi masa bincike a kan yarinyar da Asal ta kawo Agadez ta din ga yi masa girki ko?"

"Eh ya kira ni, ya yi mini maganar"

"To yaya ake ciki, me aka gano a kanta?"
Chapter 45 · 0% Book details