← Book details Buzu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 82

Sashe 47

Buzu Part 3 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Sannu a hankali ya fara samun nutsuwa, ya miƙe tsaye a hankali, ya shiga banɗaki ya watsa ruwa, sai dai jiri ya din ga ɗibarsa.
Ya fito ya zura rigarsa ya fita, ya hau kan doguwar kujera ya kwanta. Ya lumshe idanunsa, abubuwan da suka faru a Nigeria suka din ga dawo masa saɗara-saɗara, zuwa dawo da shi Niger da aka yi. To ya ya aka yi ya manta da ita komai nasa ya shafe da ya baro Nigeria, kuma yaya aka yi ya manta da komai nasa da yaje Nigeria. "Anya babu wata maƙarƙashiya ko wani abu da ban sani ba, game da rayuwata ba?"

Bakinta ɗauke da sallama ta shigo ɗakin, hannunta riƙe da kwandon kwanukan Abinci.
Wata irin karaya ta ziyarce shi, zuciyarsa ta din ga azalzalarsa ya tashi ya rungume ta, Asmynsa ce, amma zuciyarsa ta din ga gargaÉ—insa kar a samu matsala, dan ya san dokar Agadez.

"Barka da wannan lokaci Sayyid, ga abincinka, na ga na safe ma baka ci ba, ko ba shi ka ke so ba ne?" Hannu kawai ya É—aga mata, ya lumshe idanunsa, mamaki ya cika ta, ganin ba shi da niyyar magana, ya sanya ta tashi ta fita cike da damuwa.
Tana fita ya haɗe tafukan hannayensa, ya dafe fuskarsa ya fashe da kuka, da wace fuskar zai kalle ta? Me zai ce mata? Ta ina za ta yarda da shi cewar ba yana sane ya ƙi kula ta ba. A hankali ya ci gaba da tuna tsantsar juriya da sadaukarwar da ta yi saboda shi. Ba ta haƙura ba ta taho nemansa, sun haɗu kuma bai gane ta ba.

Ya so fita ya je ya samu Habu, amma ba zai iya ba, saboda ji yake yi tamkar an sauya masa gangar jikinsa.
Wayarsa da ya bari tun daren jiya a falon tana caji, ya É—auka ya duba ya ga Mahmudu ne yake kiransa.
Ya É—aga wayar bai yi magana ba, Mahmoudu ya ce "Hammad ina tunanin yaron nan fa É—an gurin Nana ne, kuma..

"Nana matata ce, ina iya tuna komai yanzu"
Mahmoudu a rikice ya ce "Ina fatan ba ka gaya mata ba?"
"Babu wanda na gayawa"
"Alhamdillah, kar ka ce mata komai, sai mun tabattar da abin da muke bincike, ka zo mu je MaraÉ—in gurin Umma, na san za ta saurareks fiye da ni. Amma ya aka yi ka tuna komai?"

"Maganar ma da kyar nake yi Mahmoudu, ba zan iya fitowa ba. Mu yi magana anjima" Ya ajiye wayar hawaye na ci gaba da zuba daga idanunsa.

Haka ya wuni ba tare da ya ci komai ba, jikinsa kuma gaba ɗaya babu ƙwari, kamar wanda aka zarewa laka.
Babu abin da yake yi banda tuna rayuwar da suka yi da Nana, da girmama yadda aka yi ya manta da ita, ya kasa tuna ta.
Sai dare sannan ya iya samu ya sha shayi kawai. Sai dai zuciyarsa babu daɗi a cunkushe. Ya lallaɓa jikinsa da yake a mace, ya nufi hanyar ɗakin Nana, sai dai ya tsaya a bakin ƙofa yana lissafin me zai ce mata? A hankali ya ɗago hannayensa, ya kalli yatsunsa, ya tuna yadda ya yi mata kyautar zoben, a lokacin da yake tsakiyar jin shauƙin ƙaunarta. A hankali ya murza tagullar hannunsa, sai ga Arun ya bayyana. Ya ce "Na amsa kira ya shugabana"
"Ka duba mini; me yarinyar cikin É—akin nan take yi?"

Arun ya risuna ya ce "Tana ninkin kaya ne ya shugabana, amma alamu sun nuna a gajiye take sosai da sosai, kuma akwai damuwa a tare da ita, sai kuma bacci da take ji. Gajiyar da ta yi da damuwar da take ciki ya haifar mata da kasala sosai. Kuma ta yi kuka mai yawa awanni kaÉ—an da suka gabata".
"Ya isa haka, ina son ta yi bacci yanzun nan"
Arun ya ce "Shiga kanka tsaye mai gidana, an riga an gama."
Hammad ya numfasa ya buɗe ƙofar ɗakin ya shiga, ya mayar da ƙofar ya rufe. Ɗakin sai ƙamshin turaren wuta yake yi. Tana kwance a ƙasa ga kayan ninkin nata a gefe. Daga ita sai zani da ta ɗaura a ƙirjinta, saboda daga wanka ta fito ta zazzage kayan ta hau ninkewa ko za ta ga wayarta da ta nema ta rasa.
Jikinsa har rawa yake yi, ya ƙarasa gabanta, bai yi wata-wata ba ya ɗago ta yana kallon kyakykyawar fuskarta.
Wata irin karaya da matsanancin tausayinta ya ratsa zuciyarsa. Ya ƙanƙameta a jikinsa yana wani irin kuka zuciyarsa na yi masa zafi da ƙuna.
Chapter 47 · 0% Book details