← Book details Buzu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 82

Sashe 10

Buzu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nene ta ce "Ranka ya daɗe me zai sanya a tsare ni? Mahmoudu ne naku dama, ku ci gaba da tsare shi da duk abin da za ku yi masa, amma ni ina roƙon alfarma a ƙyale ni na tafi"

Matawalle ya ce "Jayayya za ki yi da abin da muka ce kenan?"

Nene ta sunkuyar da kai ta yi shiru. Hammad ya ce "Zan cika miki alƙawarin da na ɗauka, babu abin da zai faru in sha Allah, ki yi haƙuri gobe in Allah ya kaimu zan zo da ita" Nene ta yi shiru cikin sanyin jiki.

Duk yadda Sultan ya so ƙanƙame Muhsin ya ƙi yadda, ya zamo ya sauka daga jikinsa, ya koma jikin Nene ya kwanta, ya saka hannunsa a baki.
Gaba É—aya Sultan ya kasa zaune ya kasa tsaye, saboda ganin Muhsin, bayan shafe lokaci yana fatan É—an nasa ya samu haihuwa.

Sardauna ya ce "To ita matar Mamman me ya kawo ta cikin wannan lamarin ne? Na ga kamar yaron ma ya santa?x

Hammad ya ce "Eh, a gurinta yake ne" Haka aka killace Nene da Mahmoudu, aka hana su zuwa ko ina.

*****

Ko da ya shiga sashensa babu kowa, Asal ba ta nan, ya yi mamakin inda ta tafi. Ya tafi kitchen ɗin da Nana take girki, ya shiga ya buɗe fridge ya samu sassanyar madarar raƙuma, ya tsiyaya ya fita.
A ƙalla ya kai awanni biyu a zaune, sai ga Asal ta dawo, babu tsammani ta gan shi a falo a zaune.
Ɗan turus ta yi tana kallon sa. Ya ce "Ƙaraso mana" Jiki a sanyaye ta ƙarasa ta zauna a kusa da shi.

"Ina ki ka je haka?"

"Nemanka na je yi" ta furta jiki babu ƙwari.

"To zan gudu ne? Ai gani na dawo"

"Wancan karon ma ai ka tafi ka bar ni"

Ya yi murmushi ya ce "Wannan na larura ne ai Cherié" Ya yi maganar yana miƙewa, har ya nufi bedroom ta ce "Hammad" tsayawa ya yi cak, jin ta kira shi da gundarin sunansa na yanka.
"Da gaske ka haihu da wata a waje ban sani ba?"

"Waye ya gaya miki?"

Asal ta kalle shi ta ce "Kar ka amsa tambayata da tambaya, ka bani amsa ko na samu nutsuwar zuciya, babu abin da yake yi mini daÉ—i. An ce ka kira ni da juya, kuma ka ce ka na da É—a, da gaske haka ne?" Ta yi maganar hawaye na cika mata ido.

Sai ya fasa shiga ɗakin, ya nufi inda take zaune, ya tsura mata ido sannan ya ce "Ni da ke na taɓa gaya miki haka? Ta girgiza kai jiki a sanyaye.

"Wanda ya gaya miki ya so cin mutuncinki ne, amma da bakina na taɓa faɗa?" Ta girgiza kai jikinta a sanyaye.

"To ki toshe kunneki daga jin abin da za a zo a gaya miki wai wai, ki jira abin da zai fito daga bakina zuwa kunnuwanki"

Ta yi ajiyar zuciya ta ce "To, amma ba ka gaya mini inda ka je ba"

"Wani aiki nake yi wa Sultan, ki kwantar da hankalinki" Ya miƙe ya tafi ya bar ta a gurin.
Da magariba ta ga yana ta shiri, ta ce "Amour ina zaka je ne?"
Ya ce "Eh yanzu zan yi miki bayani, zan je wani aiki da Sultan da ya saka ni ne, sai gobe in Allah ya kaimu zan dawo"

"Aiki kuma sai da daddare?"

Ya kalle ta ya ce "Asal, wai ki na zargina ne, yau na fara fita yin aiki da daddare, me yasa za ki tsare ni da tambayoyi kamar ba ki yarda da ni ba, shirya mu tafi tare" Yayi maganar yana haÉ—e rai.
Ta risunar da kai cikin girmamawa ta ce "Tuba nake yi, zuciyata ce ta cika fargaba, amma ka yi haƙuri"
Ya miƙe ya nufi hanyar fita, haka nan zuciyarta ta tsananta bugawa.

Bayan fitarsa ya tsaya a harabar gidan, ya É—auki wayarsa ya kira Tafawa.
Tafawa ya É—aga tare da yin sallama.
Hammad ya amsa tare da cewa "Barka da dare ranka ya daÉ—e"

"Barka dai" Ya amsa a taƙaice.

"Yauwwa, dama na kira ka ne na sanar da kai, ka san abin da za ka din ga sanar da Asal, ka daina shiga cikin batun iyalina, idan ba haka ba za ka iya saka wa ta rasa ranta ko lafiyarta"

"Hammad, ni ka ke gaya wa haka?"

"Kai ka bani damar na gaya maka hakan ai. Abin da ba ka sani ba shi ne, Asal ta riga ta fara so na, tsawon lokacin da ya gabata, ci gaba da gaya mata magana kowace iri a kaina, ka iya haifar mata da matsala. Amma 'yarka ce duk abin da ka ke ganin shi ne daidai ka yi ba wani abu" Ya kashe wayarsa gaba É—aya, ya shiga mota da kansa ya ja motar ya bar gidan.

A zaune ya tarar da Nana a ɗakin da kayanta suke, ta sanya atamfa riga da skirt, kanta babu ɗan kwali. Ta yi parking ɗin black natural hair ɗin ta, da siririn band na yi wa yara kitso. Dan zabura ta yi, da ta ji motsinsa. Hannunsa riƙe da ledoji, ya ƙarasa ya zauna ya ajiye ledojin ya ce "Sannu da gida, na bar ki ke kaɗai ko?"

"Dama can ai nikaÉ—ai É—in nake rayuwata"

Ya yi murmushi ya ce "Haka ne, amma dai kin rayu da ni É—in ko?" Ta yi masa shiru tana kai hannunta ta É—auki É—an kwalin kayan, za ga É—aure kanta. Ya janye É—an kwalin ya ce "A haka nake son ganinki, kin yi mini kyau sosai da sosai"

"Sayyid, duk wannan abubuwan da ka ke yi, ba za su taɓa tasiri a kaina ba, ka bani ɗana kawai na kama gabana"

"Gaskiya ne maganganuna ba za su yi tasiri a kan ki ba, ciki har da kirana da Sayyid. Ga abinci na kawo miki, ki ci"

Ta kalle shi cikin damuwa ta ce "Ai na ci Abincin kamar yadda ka ce, yaushe za ka ba ni É—a na?"

"Kin ci, amma ba kamar yadda nake buƙata ba, sonake ki ƙara ƙiba, alamu sun nuna ba kya nutsuwa ki ci abinci ki ƙoshi" Ta kawar da kanta gefe, dan kar ma ya ci gaba da jan hirar. Dan ba ta son duk wani abu da zai sanya a ranta ta ji za ta iya ci gaba da rayuwa da shi."

Ya kwance rawaninsa, ya rage kayan jikinsa, ta kawar da kanta gefe, ƙirjinta na bugawa da sauri da sauri.
Ya zauna a kusa da ita ta É—ago ta kalle shi, gashin nan a kwance ya sha gyara. Ya É—ago mata yatsunsa ya ce "Ina zobena ne? Kin saka an addabe ni a kan zoben nan da yawa" Yana nuna mata yatsunsa.

Ta yamutsa fuska ta ce "Na yar da shi"

"Kin yar da zobena, kin ajiye turarrukana da mayukan gashina, ki na kallo ki na jin daɗi. Soyayyar gaskiya mara algus. Gobe in Allah ya kaimu za mu je gaban Sultan, mu ji hukuncin da za a yanke mana. Saboda na aikata laifi mai girman da babu wanda ya taɓa aikata shi sai ni."

Ayshercool.
08081012143
81
Nana ta taɓe baki ta ce "Wanda za a yanke maka dai, ni babu abin da ya haɗa ni da masarautarku, kawai a bani ɗa na na tafi"

Ya zura mata ido, ya jinjina kai ya ce "Kin daina so na dai kenan ko?"

"Eh" ta faÉ—a tana kawar da kanta gefe.

"Shikenan, zan ƙara miki lokaci, zuwa lokacin da ki ka ga ya dace ki saurare ni, amma ki sani, ni shugaba ne, kuma wasu lokutan idan aka tashi kawo gyara, toshe kunne muke yi, mu farantawa wani mu ɓatawa wani, domin samar da gayar. Dan haka duk abin da ya kama zan banƙara na aikata, domin ganin ba ki suɓuce mini ba, ko da kuwa abin da zan aikata ɗin na nufin ƙara miki ƙiyayyata. Yanzu dai ga abinci ki samu ki ci, sai ki kwanta ki huta da wuri zamu tafi" Ta murguɗa baki ta sake kawar da kanta gefe.
Duk wannan abubuwan da take yi masa, ko sau ɗaya bai ji haushinta ba, shi dai fatansa da roƙonsa ta saurare shi cikin nutsuwa, ya warware mata zare da abawa, saboda ya san ko shi ne haka ta faru a kansa, zai ce wulaƙanci ne aka yi masa.
Ganin ya ƙi tashi ya bata guri, ya sanya ta ɗago ta kalle shi, ta ga ya zuba mata ido, kamar zai lashe ta.
Ta sake kai hannu ta É—auki É—ankwalinta, amma ya jefa shi bayansa.
Wannan kallon da yake ƙanƙance ido ya fara yi mata, ta ƙara tsuke fuska tana tattara nutsuwarta, amma ya kai hannunsa kan gashinta, ya fara shafawa a hankali. Bai sani ba ko dan ya saba ganin irin gashinsu Asal na buzaye nai laushi da santsi ya sanya na Nana yake burge shi.
Baƙi ƙirin da shi natural, mai cika sosai da sosai. Ta hau ture hannunsa, amma yaƙi barin abin da yake yi, sai ma lumshe mata ido da ya hau yi.
Duk wani abu da Nana za ta yi ta baƙanta masa rai, tana aikatawa domin gujewa barin nusarar zuciyarta ta sake yarda da shi, ta ba shi wata damar ya cutar da ita.

Sai da ya bar ɗakin ta samu ta ci abinci, ta tura ƙofar ɗakin, sai dai babu mukulli yadda za ta datse ƙofar dan kar ya shigo mata.
Tana kwanciya bacci, nannauyan bacci ya sake yin awon gaba da ita.
Chapter 10 · 0% Book details