← Book details Buzu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 82

Sashe 56

Buzu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*****
Asal duk ta fita hayyacinta, kullum cikin kuka, ta yi wata irin muguwar rama.
Tana zaune a É—akinta, Tafawa ya shigo É—akin, ta É—aga kai ta kalle shi. Ya ce "Dalilin me ne ne ya sanya ba kya cin abinci?" Ta yi shiru ba ta ce masa komai ba.
"Kar ki saka damuwar abin da yake faruwar nan a cikin zuciyarki, duk yadda zan yi dole sai na tabattar da an hukunta Hammad, ba zai ci bulus ba abin da ya aikata."
Asal ta yi shiru, wani irin baƙin ciki na taso mata a zuciyarta, ta din ga tuna yadda mahaifin nata ya din ga ingizata da tursasa ta aikata Wasu abubuwan. Ya yi wa rayuwarta illa duk a ƙoƙarin sa na ganin ya cimma wani burinsa da abu ne mai wahala ya samu cikarsa.
Yana magana amma ta lula Duniyar tunani, ta tuna lokacin da aka kusa auren, ya kawo mata wani abu a ƙoƙo ya ce ta sha, sai bayan da ta sha sannan ya ce bai aura mata Hammad dan taje ta haihu da shi ba, domin har abada baya fatan ya haihu balle ya sanya ran samun magaji ya ƙara dagula masa lissafi gurin cim ma burinsa.
Wasu irin zafafan hawaye suka zubo wa Asal, ta daɗe da gane rashin haihuwarta na da nasaba da wannan magani da mahaifinta ya bata, duk da a ɓoye ta je ganin likita a kan matsalar rashin haihuwar, aka ce mata hakan yana da alaƙa da ta'amalli da chemicals masu ƙarfi da ta yi. Da fari ta yi tunanin shaye-shaye da take yi, sai dai ko da shaye-shaye ta fi kyautata zaton maganin da Tafawa ya bata ne sila.

Nana ta samu ta sake sosai da sosai da Imran ta din ga bashi labarin abubuwan da suka faru bayan tafiyarsa, wasu guraren sai da ya yi hawaye. Haka kuma ya din ga yi wa Nene addu'a, a kan abin da ta yi wa Nana na taimako.
Nene ta ce "Babu komai, É—a na kowa ne. Kuma in sha Allah Nana daram zata zauna a É—akin mijinta"

Nana ta kalli Imrana ta ce "Imrana tsoro nake ji, ban san yaya su Baba za su kalle ni ba, ban san me zan ce musu ba, ga shu kai ma tun da ka tafi ba ka je gidan ba?"

Imrana ya ce "Ba za ki daina wannan zancen ba, ba abin da za su yi miki. Nima ban je É—in ba"

Nene ta ce "Ai dole mu kafa mu tsare, daga nan Agadez a tashi tawaga, su je har gida a bawa iyayenku haƙuri, kaga yanzu kai ne waliyyinta, a tashi manya daga Agadez su je har Nigeria su ba wa iyayenku haƙuri a kan abin da ya faru, sannan kuma a yi. Sannan ya zama dole a yi wa Nana duk wani abu na dukiyar aure, a yi cikakken biki na 'yar gata duniya ta shaida auren yadda yakamata, dan gudun kar ma a zo a samu wata matsala a nan gaba."
Imarana ya ce "Wannan gaskiya ne, amma kina ganin za su amince da hakan?"
Nene ta ce "Dole za su amince, ko dan son da suke yi wa É—an su. Tun da É—ansu yana son iyalinsa."

Hammad kuwa gidansa ya koma, sai dai ya rasa abin da yake yi masa daÉ—i, ya din ga juyi yana tunani, tare da tambayar kansa, kenan duk abin da yake faruwa da sanin Zahradeen. Kasa jurewa ya yi ya tashi ya tafi gurin Sultan. Yana zaune Gimbiya Bilkisu ta sanya shi a gaba, tana ta maganganu a kan kar ya nuna son kai akan hukuncin da zai yanke, kuma ya duba Asal ita ma a yi mata adalci.
Babu tsammani sai ga Hammad ya shigo, yanayin yadda fuskarsa ta yi jawur, ya sanya Sultan miƙewa yana tambayarsa ko lafiya? Amma Hammad ya yi shiru bai ce komai ba. Sultan ya kama hannunsa ya shiga da shi cikin ɗakinsa, ya zaunar da shi ya ce "Ka gaya mini mene ne?" Sai gumi da yake ta tsatstsafo masa amma bai yi magana ba.
Mahmoudu kuwa daga fitowar Hammad ya biyo bayansa, ya neme shi ya rasa, yana son su yi magana, ya lallaɓa shi su bi abin a sannu su fahimci Zahradeen, dan ya ga alamar ya ɗau zafi lamarin ya ɗaure masa kai.
Matar Imam Zahradeen ta yi sallama, suka amsa. Ta kalli Nana cikin sakin fuska ta ce "Gimbiyar Imam Hammad, Imam Zahradeen yana kira"
Nana ta yi murmushi ta ce "Nana dai za ki ce"
"Ina, wa ya isa faɗar sunan Gimbiya" Nana ta yinƙura ta tashi ta bi bayanta.
Bayan sun shiga, matar Zahradeen ta koma, Nana ta zauna a ƙasan Carfet.

Ya ce "Kin ga mijinki ya ɗauki zafi, yaƙi tsayawa ya saurare ni, balle ya fahimce ni, amma na ga ke kina cikin nutsuwarki, za ki fi fahimtata. Amma kafin nan kin ga ke ki ka zauna da shi, ko za ki iya gaya mini abin da ki ka sani, bayan haɗuwarku lokacin yana cikin rashin lafiya?"
Ta jinjina masa kai, sannan ta yi masa bayanin, abin da take ganin ya dace ta gaya masa.
Ya ce "Shikenan, Sultan ya kira ni a waya, ya ce yana nema na, na san wataƙila ya gaya masa ne, tare da ke za mu je gobe in Allah ya kaimu da safe"
Nana ta amsa masa da "To"

*****
Hajiya Halima ta kiÉ—ime, tun bayan da Sagir ya kira wayarta yake tambayarta, ko Yusra ta je gidan.
Har ta fara shirin tafiya Kano, Yayar Baban Yusra ta kira ta a waya, ta sanar mata ga Yusra ta zo tun ƙarfe shida na safiya tare da wani jariri da ba su san a ina ta samo shi ba.
A kiɗime Hajiya Halima suka shirya, suka tafi gidan Antyn, su na zuwa suka tarar da ita cikin yanayin ɗimuwa, ba ta magana ga kuma wani ƙosashshen jariri da ba a san inda ta samo shi ba.

Hajiya Halima ta ce "Ai ni mijinta ya kira ni cikin tashin hankali, yake tambayata wai ko Yusra ta zo, ya neme ta ya rasa. Hankalina a tashe na fara shirin tafiya Kano, kin san uwargidanta fa ita ma an neme ta an rasa.

"Mami" Yausra ta faɗa da ƙarfi.
"Na'am Yusra, sannu"
"Ku gaya wa Daddyn Haidar yaje ya É—aukko Shukura, za su kuma sace ta"
Cikin rashin fahimta ta ce "Suwaye?"
"Nima ban san su ba, amma sace ta za su yi, na baro ta a can"
Duk yadda suka yi da Yusra ta yi musu bayanin yadda za su gane, ta kasa sai kukan aje a É—aukko Shukura kar a kuma sace ta.
Hajiya Halima ta kira Sagir da lambar da ya kira ta, ta sanar masa ga Yusra a Abuja tare da wani jariri da ba su san a inda a ta samo shi ba. Cikin kiÉ—ima da tashin hankali, ya É—auki mota ba tare da ya gaya wa kowa ba, ya kama hanyar Abuja.

*****
Bayan su Nana sun hallara a gaban Sultan, ta yi tozali da Giyaz a tsaye da sandarsa a bayan Hammad, sai da jikinsa duk rauni ya ƙara tsufa ya yi wani iri. Jikinsa sai hayaƙi yake yi ya zubo mata ido.
Sultan ya dubi Imam Zahradeen ya ce "Zahradeen me ka yi wa ɗan uwanka ne, ya ƙi magana, sunanka kawai ya furta ya yi shiru, a nan muka kwana tare da shi, ko sau ɗaya bai yi magana ba.
Imam Zahradeen ya haÉ—iye wani abu mai É—aci a wuyansa, yana tunanin ta ina zai fara bayani.
Nana ta ce "A je a zo da Sarkin baka gurin nan, idan ba haka ba Giyaz zai iya haddasa matsala"
Duk suka kalli Nana Imam Zahradeen ya ce "Waye hakan?"
"Ku zo da shi dan Allah, kar a samu matsala wani abin yake son aikatawa"
Ganin Nana na neman burkicewa, ya sanya Sultan É—aukko wayarsa ya É—an daddana, Hammad dai bai ce komai ba.

Imam Zahradeen ya ce "Kafin na ce komai, ina mai neman afuwarku a kan abin da zan faÉ—a, kuma ina neman afuwa da ni da waÉ—anda zan faÉ—a a cikin maganata.
Na ji daɗi sosai da sosai da ka neme mu a keɓantaccen guri kamar haka, ina roƙon ku rufa mana wannan asirin dan Allah"
Sultan ya ce "Zahradeen, ka tafi kai tsaye ka yi mini bayani, kana ta zagaye-zagaye daga mu sai mu a gurin nan"
Ya ƙarasa maganar yana kallon wayarsa, ya danna ya ce "Ku ba shi dama, shikaɗai ya shigo"
Sarkin baka ya shigo da sallama, ya risuna a gaban Sultan ya kwashi gaisuwa, ya juya ya gaida Imam Zahradeen, amma ya yi shiru yana kallon Imam Hammad da kuma Nana.
Sultan ya ce "Ga mai maganin an kira shi, ya aka yi?"
Sarkin baka ya ce "Uwar gijiyata, meyafaru da Giyaz ne?"
"Ƙaisar ya ce mini faɗa suka yi." Ta mayar da idonta kan Sultan ta ce "Allah ya baka nasara, ya ci gaba da maganar a gaban Sarkin baka, shi ma amintacce ne, idan ya fita Giyaz zai iya aikata masa wani abin"

Sultan ya ce "Waye Giyaz É—in ne?"

Sarkin baka ya ce "Aljanin da aka yi masa asiri da shi ne ranka ya daÉ—e"

Imam Zahradeen ya fara magana ya ce "Tabbas na san ni mai laifi ne, kuma duk hukuncin da za a yanke mini zan karɓa"
Chapter 56 · 0% Book details