Sashe 72
Buzu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Alhaji Sabo ya ce "To shi ne me, kowa ma na haka ne ai. Kana ganin zaka iya zama a gidan nan kai kaÉ—ai, ko a samo maka wanda zai tayaka zama?"
Ya girgiza kai jiki a sanyaye, duk da mutuwar Yusf ta dake shi, amma bai taɓa jin mutuwar da ta daki zuciyarsa kamar mutuwar Hajiya Amina ba. Kan ƙiftawa da Bismillah. Ya ɗauka aljanin da ya bawa mahaifarta shikenan ya tseratar da ita daga ƙungiyar, abin da bai sani ba shi ne, bai isa ya tseratar da ita daga ajalinta ba.
Ya nemi guri a gefen gado ya zauna, kawai ya din ga ganinta tana yi masa gizo. Duk izza da ƙafafa ta matan masu kuɗi, da ta'amalli da 'yan aiki, Hajiya Amina ba ta yadda mai aiki ta dafa masa abinci ba. Duk da son da yake yi mata, baya hana shi ya ci mata mutunci wasu lokutan. Amma ko ta yi fushi na lokacin ne ta ware.
Ya yi mata wani irin so, mai wahalar mantawa.
So yake yi ya samu damar zubar da hawaye, amma abu ya gagara. Vibrating wayarsa ta yi a kan gadon, ita ma yadda ya tafi ya bar ta, haka ya dawo ya tarar da ita. Ya ƙura mata ido daga bisani ya kai hannu ya ɗauka ya duba.
Saƙo aka turo masa da lambar Doctor Sharif, ana sanar da shi Allah ya yi wa mai wayar rasuwar, za a yi jana'izarsa da yammacin ranar.
Ya fito daga cikin saƙon, ya ga saƙon Yusuf na ƙarshe, da yake ce masa Daddy idan ka ga saƙona ka kira ni dan Allah na kasa samun ka a waya.
Ya tuna yadda suka yi waya, Yusuf yana tsara masa yadda zai yi walimarsa na kammala master's da ya yi, suka da daÉ—e su na waya cikin raha da barkwanci. Ya tuna yanzu duk ba sa Duniya.
"Saura kai, nan da anjima kai ne zaka mutu" Ya ji wata zuciyar ta raya masa. A take zuciyarsa ta tsinke ya buɗe idonsa a razane ya miƙe tsaye yana waige-waige. Wata irin fargaba ta shige shi, wani abu da bai san ko mene ne ba, ya tsirga masa tun daga cikin kansa har ƙafafuwansa. Da sauri ya fita daga ɗakin ya koma falonsa yana mayar da numfashi.
****
Hammad ya kalli Asal da take ta kuka ya ce "Ko ki yi mini shiru, ko ki fita ki koma tun da ba dole na yi miki ba" Ba shiri ta hau goge hawayenta ta ce "Yi haƙuri, na daina" Ta yi maganar muryarta ƙasa-ƙasa.
Gaba ɗaya zuciyarta babu daɗi, har ga Allah ba ta son saɓa wa mahaifinta, amma ta san ba a kan gaskiya suke ba. Kuma idan ya kashe mata auren yaya yake son ta yi?.
Ta yi shiru ta rakuɓe a gefen motar, kamar mai tsoron wani abu. Ya saka hannunsa ya janyo nata ya ɗora a kan cinyarsa yana murzawa a hankali hannu ɗaya kuma yana tuƙinsa. Ta ɗaga kanta ta kalle shi, ta ga ya mayar da hankali sosai a kan tuƙinsa.
Ji ta yi kamar ta kwanta a jikinsa, amma ta tuna girman laifuffukan da yake kallonta da su yanzu, dan haka ta fasa.
Ko da suka je gidan, ta tarar an yi wa gidan gyara sosai, an canza furnitures. Ta kalle shi za ta yi magana, amma sai ta fasa saboda gani take kamar fuskarsa a haÉ—e take.
"Ina fatan canje-canjen da na yi ya yi miki, ban ɓata miki rai ba"
Da sauri ta ce "A'a sun yi na gode sosai"
"A'a faɗi gaskiya dai, na san ki da iyayi da ƙaƙale, idan bai yi ba a mayar da kayan a canzo wasu, tun da kamfanin wata uku suka bayar idan bai yi ba a mayar"
Ta girgiza kai ta ce "Yayi sosai da sosai"
Duk barorin gidan ba wani sonta suke yi ba, saboda fi'ilinta da wulaƙanci, amma da suka ga ta dawo sun yi murna, dan duk da wulaƙancinta akwai kyauta. Hannunta a buɗe yake sosai da sosai gurin ungo.
Shi ya zo musu da abincin da ya saka aka kawo, daga gidan Abincinsa na Agadez.
Ya ci kayansa kamar ya share ta, ganin ta ƙi sakin jiki ta ci, duk da ya ce ya yafe mata, amma wasu lokutan da ya kalle ta wasu abubuwan suke dawo masa. Duk da yafiya aba ce mai wahala wasu lokutan, amma mantawa da laifuka ya fi komai wahala.
"Cherié, ba za ki ci abincin ba ne?"
Ta ce "Na ci"
"Ba ki ci da yawa ba ai, ke da na san ki da son abinci, matso na baki a baki" Haka ya yi ta ƙoƙarin danne komai, kamar yadda ya saba yi a baya.
Da suka zo kwanciya ma, kasa sakin jiki ta yi, sai raɓe-raɓe take yi, tana satar kallonsa. Shi kuwa hankalinsa yana kan wayarsa, yana tsokanar Nana da roƙonta dan Allah kar ta kasa bacci, zai zo su haɗe ta mafarki.
Emojin dariya ta tura masa, ta ce "Da kenan, ka ke yi mini wannan rufa idon, yanzu ina gane komai, ka yi addu'a ka kwanta sai da safe" Ya yi murmushi ya rufe data. Ya juya ya kalli Asal ya ce "Na canza kamanni ne?" Ta ɗan sunkuyar da kai tana girgiza kai. Ya miƙa mata hannunsa ya ce "Ƙaraso mana" A hankali ta ƙara, ya rungumo ta jikinsa, ya kwantar da ita sosai a kan gadon. Ya tashi ya je ya kashe fitilar ya dawo ya kwanta a kusa da ita. A ƙasan zuciyarsa ya din ga roƙon Allah ya sanya yafewa Asal da ya yi da sake karɓar ta a matsayin mata, kar ta sake yinƙurin cutar da shi.
"Ya Allah da kyakkyawar niyya na yafe wa wannan baiwa taka, saboda ina tausayinta. Ubangiji Allah ka sanya ta gyara rayuwarta mu zauna lafiya"
Sosai ya sake da ita, tamkar babu wani abu na rashin daÉ—i da ya faru.
*****
Duk yadda Alhaji Zailani ya so kawar da komai a ransa a kasawa yayi. Ya din ga zagaya gidan yana kallon hanyar ɗakin Shukura, da har a yanzu idan ta zo gidan, a nan take kwana. Ya kalli inda Yusuf yake zama mussaman idan zai kalli ball. Suna kallon ƙwallo tare dukkanin su akwai team ɗin da suke supporting. Ya tuna kai komon Hajiya Amina a tsakaninsu, da ƙoƙarinta na ganin kowa ya samu abin da yake buƙata. Amma yanzu babu Yusuf babu Amina, Shukura kuma babu wani abu da ta tsana a yanzu sama da shi. Gidan ya yi masa wani irin zafi Duniya ta din ga juya masa. Dama salla ba wani damuwa ya yi da ita, domin rashin kiyaye ta na daga cikin dalilan da yake kawo musu rashin jituwa tsakaninsa da Amina.
Ya din da ga jin sa tamkar a cikin wata Duniya yake, aka bar shi shikaÉ—ai.
Bugun ƙofar da ya yi yawa ne ya tashi ya je ya buɗe ƙofar main falon, ya tarar da mai delivery ya kawo masa abinci, kamar yadda Alhaji Sabo ya yi masa order, ya yi shiru yana tunanin ina mai gadi, da har mai delivery ya shigo haka. Ga harabar gidan babu kowa yan gaisuwa ma duk sun watse ya karɓa ya koma ya ajiye ya nemi guri ya kwanta.
Rufe idanunsa ke da wuya, ya ga duhu ya yi, alhalin yamma ce da sauran haske. Ya buɗe idanunsa ya yinƙura zai tashi, amma ya ji tamkar an saka igiyoyi an ɗaɗɗaure shi, ya kasa motsa ko da yatsansa. Yana jin yadda zuciyarsa take bugawa ya sare cewa kan shi ma ya mutu ne, ya din ga rarraba idanu ya ga ta ina zai fara ganin mala'iku sun bayyana. Ya hango cewar shi ma yanzu likkafani za a saka masa a je a binne shi a rami a tafi a bar shi. Ya yi wani yinƙuri domin ya tashi amma abu ya gagara. Wata irin dariya ya ji ana yi mara daɗin ji, cikin sauti mai ƙarfi.
"Abin da ka ke gudun sai ya faru, ba za ka tsere wa mutuwa ba, dole ka biya wa dodo buƙatar sa, ko kuma ya yi ajalinka. Ɗif ya daina jin muryar, sai kuma fuskar matarsa ta farko da ɗanta na fari, suka fara fitowa a ɗakin. Ya sake rikicewa sai dai bai iya kowane yinƙuri ba, Shukura ta bayyana jikinta duk jini, kamar ba ta daɗe da haihuwa ba, ta tunkaro shi gadan-gadan da wuƙa ta fara ƙoƙarin caka masa. Kamar wanda aka tasa daga bacci ya gan shi a tsakiyar titi, ƙafafuwansa ko takalmi ko babu. Ya kalli jikinsa babu suturar kirki, gari shiru ko ina duhu alamar dare ya tsala. Sai da ya yi da gaske sannna ya gano cam gaban unguarsu ya tafi. Rashin gurin zuwa ya sanya tilas ya sake koma wa gidan nasa, ya ci uwar tafiya da ƙafa ya koma.
Sai dai ƙofar gidan a buɗe, babu masu gadi, abin da bai sani ba tuni zancen ya fara zagayawa, a kan abin da ake zarginsa da shi, kasancewar mai aikin gidan na laɓe ta ji maganganun da aka yi. Suna watsewa da aka tafi da Hajiya Amina Asibiti, aka tafi da Alhaji Zailani ta tattara kayanta ta gaya wa mai gadin abin da yake faruwa ta gudu.
Alhaji Fatuhu ya ƙi sanar wa Iyalinsa abin da ya faru, sai dai gaba ɗaya ba shi da nutsuwa, ga kayansa ana ta saya babu ƙaƙƙautawa amma ba ya iya taɓuka komai, sai dai ya ɓuya ya yi kuka.
Babu tsammani Fadila ta ritsa shi yana kuka, ya kasa cin abinci.
Cikin damuwa ta ce "Daddy, ina gama ka da zatin Allah ka gaya mini abin da yake damunka, da ba haka ka ke yi ba fa. Gaba kamar ma a tsorace ka ke Duniyar, kuka fa ka ke yi dan Allah ka faÉ—a mini mene ne?"
"Wallahi Fadila a tsorace nake da Duniyar, komai tsoro yake bani, ni dama rashin lafiyar da na yi na mutu, ban tashi ba da ban ji wannan abubuwan da damuwa da baƙin cikinsu zai halakka ni ba, bayan warkewr da na yi daga jinya ba"
Ba ta san lokacin da ta fara kuka ba ta ce "Dan Allah Daddy mene ne?"