← Book details Buzu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 82

Sashe 31

Buzu Part 3 Complete Hausa Novel · about 3 min read

89
LITTAFIN KUÆŠI NE 1K 0069685771
Aisha Adam stanbic
08081012143
A hankali Nana take ƙoƙarin buɗe idanunta, zuciyarta cike da matsanancin tsoron, da rabon da ta ji makamancinsa har ta manta, tare da fatan Allah ya sanya ta farka daga wannan mafarkin mara kan gado. A hankali take jin numfashin sa na sauke a fuskarta. Ta buɗe idonta sosai ta sauke a kan fuskarsa da ya tsare ta da idanunsa, sai dai kan ta yi wani yinƙuri, ƙamshin ɗakin ya mamaye mata hanci, hakan ya sake tabattar mata da ba mafarki ba ne ba zahiri ne. Ta zabura da sauri ta gansu a kan gadon tare ita da shi a cikin ɗakin dai.
A gigice ta fara ƙoƙarin sauka daga kan gadon cikin matsanancin tsoro, tana zazzaro masa ido. Sayyid ya riƙe ta ya ce "Dan Allah ki daina tsorata kanki, ki nutsu mana. Babu wani abin tsoro a gurin nan"
"Ta yaya zan nutsu, kana caza mini ƙwaƙwalwa, na ma rasa me yake faruwa, kuma sannan ka ce babu abin tsoro a gurin"
Ya ce "Zaki fahimci abin da yake faruwar, amma dole ki nutsu, kuma ki saurare ni"  Ya ɗago yatsunsa ya kalli zobunan hannunsa, da space ɗin guda ɗayan sannan ya dubi Nana ya ce "Abubuwan da ki ke gani a tare da ni, su na da alaƙa da wannan zobunan na hannuna. Nana ta kalle shi ta kalli zobunan cikin rashin fahimta.
"Ina Zoben da na baki, mu na Nigeria?" Ba ta ba shi amsa ba, kawai ta hau ƙoƙarin tashi ta bar gurin.
Ya din ga kokowa da Nana, amma idonta ya rufe, hanya kawai take nema ta gudu ta bar gurin. Dan gani take idan ta ci gaba da zama zaucewa za ta yi.
Sai da ƙyar ya  lallaɓa ta ya ce "To shikenan, mu je na mayar da ke mu tafi, tun da ba za ki nutsu ba" Ya riƙo hannunta, sai dai duk a tsorace take, su na fita daga wannan ɗakin ya shiga da ita wani ɗakin.
Gurin duk an yi wearing ɗin fitilu, sai dai da ya kunna fitilun gurin ya yi haske. Ta ƙara razana da ganin gurin. Komai na zamanin da ne sosai da sosai.
Wasu zane-zanen mutane ne a manyan frames a kafe, har zuwa kan wasu hotunan da suke dishi-dishi na Black and white na da, zuwa kan hotunan da ake iya gane mutanen jiki sosai wanda ya nuna na baya-baya ne hotunan sai hoton Sultan da ya fita fes. ÆŠaya bangon Hoton Sultan ne shi ma, da hotunan Imam Imam na Agadez a jere.
Sai dai mutanen na jikin zanen da na hiton duk masu kyau ne, kuma yanayinsu ya nuna daga zuriya É—aya suke.
Sai kuma gefe  wasu ƙananan hotunan a wani ɓangare na ɗakin, da suke nuna yaƙe-yaƙe, da yanayi na zamanin bayi.

Hammad ya ce "Wannan hotunan da ki ke gani, tun daga kan na zanen nan, hotunan wasu daga cikin sarakunan da suka yi gwagwarmaya gurin kafa masarautar Agadez ne.
Waɗannan kuma, wasu daga cikin bayi ne, da suka yi wasu laifuka na rashin kyautawa, wanda tun daga zamanin har kawo yanzu, duk wanda aka haifa a zuriyarsu bawa ne, ciki har da wannan dattijon da yake gadin ƙofar gidan tarihi na Agadez. Idan ya mutu dole zuriyarsu za su bayar da wani wanda zai ci gaba da wannan aikin.

SHEKARUN DA SUKA GABATA.
Chapter 31 · 0% Book details