← Book details Buzu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 82

Sashe 43

Buzu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya shafa gashin kanta, tare da fatan Allah ya sanya Asal ɗin ta canza gaba ɗaya, tare da yi musu addu'ar samun rabo na alkhairi. Kamar ya tashe ta, sai kuma ya ƙyale ta kawai ya lumshe idanunsa yana addu'a a ƙasan zuciyarsa yana jiran bacci ya ɗauke shi.
Yana tsaye a cikin sahara, ya riƙe akalar raƙuminsa, iskar sahara sai kaɗawa take yi, babbar rigar jikinsa na ɗagawa, ta cikin iskar yake jiyo sheshsheƙar kukan mace tana faɗin "Sayyid" ya waiwaya bai ga kowa ba. Shikaɗai ne a cikin saharar, sai dai bai daina jin sheshsheƙar kukan ba.
A hankali ya buÉ—e idanunsa, wannan shi ne karo na bai san adadi ba, yana wannan mafarkin tun da ya buÉ—e ido a faransa. Jin kiran sallar Asuba ya sanya ya tashi ya tafi salla.
Ranar farko da ya sake cin abinci bayan wanda ya ci da ya dawo, sai ya ji kamar ya san É—anÉ—anon abincin, amma ya manta a ina ya san shi.
Ranar da ya sake ganin Nana, Asal ta kira ta a kan ta zabga yaji a abinci ya kasa ci, sai da zuciyarsa ta kusa tsayawa, ya din ga jin kamar abu malaman haka ya taɓa faruwa, amma bai san a ina ba. Jikinsa ya din ga tsuma sakamakon jin sanyin da ya fara yi, ga kallon da take yi masa da ya sake burkita shi. Ya din ga matsa ƙwaƙwalwarsa, ko za ta ba shi wani abu, amma ya ji ya fara jin jiri.
Bai tsaya kammala karin kumallon ba, ya tashi ya fita ya je ya samu Sultan, baya ya kammala zaman Majalissa, yake ce masa shi fa haryanzu bai ga Mahmoudu ba. Sultan ya ce masa ya yi tafiya ne, amma zai dawo. Haka kurum ya ji bai yadda da hakan ba, amma bai kuma cewa komai ba.
Cikin hikima ya tambayi Asal inda ta samo Nana, ta sanar masa da a gidan Abincinsa na MaraÉ—i take aiki, ganin ta iya girki ya sanya ta kawo ta gidan, domin ta din ga dafa masa abinci.
Sai dai a kullum abubuwan da Nana take yi, su na ƙara dagula masa lissafi nesa ba kusa ba.
Matsin lamba da Hammad ya yi ya sanya aka sako Mahmoudu, kuma Matawalle ya jaddada masa lallai kar ya kuskura ya gaya wa Hammad komai a kan zuwan da suka yi Nigeria, kuma kar ya gaya masa É—aure shi suka yi.
Hammad bakinsa ya ƙi rufuwa, bayan ganin Mahmoudu da ya yi, saboda yadda yake jin Mahmoud a rayuwarsa ba ya jin Zahradeen yayansa da suke uba ɗaya haka. Sai ya yi ta yinƙurin ya yi wa Mahmoudu bayanin abubuwan ban mamakin da yake gani game da Nana, amma sai ya kasa. Babbn abin da ya sake ɗaure masa kai da ita, shi ne lokacin da ya hana ta cin ayaba. Ta karɓa ta ci, a lokacin ya ga Ƙisar a tare da ita. Ganin Ƙaisar ya ƙara hargitsa masa lissafi, saboda yana ganinsa hoton suffar Giyaz ya faɗo masa, amma ya manta a ina ma ya san fuskokin. Sai daga baya sannu a hankali ya tuna yadda Giyaz y fito masa a gidan tarihi, amma wanda ya gani tare da Nana bai kai wancan tsufa ba.

Gefe guda kuma Ƙaisar da Giyaz su na ta dambarwa, Giyaz ya ce ba zai taɓa rabuwa da Nana ba, ya mantar da Hammad wace ce Nana da duk wata rayuwa da suka yi a Nigeria saboda ta ci gaba da shan wahala.
Bokan da ya sanya Giyaz aikin ɓatar da Hammad kuwa, hankalinsa ya dugunzuma bayan da shi ma wands ya ba shi aikin, ya matsa masa lamba da masifar ya aka yi Hammad ya dawo Agadez bayan an ce har abada shi da Agadez.

"Ya kai Giyaz, ina alƙawarin da muka yi da kai? Na baka 'yanci bisa sharaɗin za ka yi mini aiki, amma kwatsam sai na ga wanda na baka aikin a kansa ya dawo Agadez"

Giyaz ya ce "A cikin aikin naka wanne ne ban yi ba? Na mantar da shi waye shi, na mantar da shi, ya bar Agadez ya yi nesa da ita, kuma ya yi. Ni da kai ba na tunanin akwai wanda yake bin wani bashi, na cika sharuÉ—É—anka kaf da muka yi yarjejeniya a kai"

Bokan ya ce "Amma ai ga shi ya dawo Agadez cikin ƙoshin lafiya a hayyacinsa"

"Eh, ai ba mu yi da kai zai bar Agadez har abada ba, na kuma yi iya abin da muka yi sharaÉ—i a kai"

"Kar ka fusata ni, ka sanya na sake kama ka na rufe ka, ni bami yi haka da kai ba"

Giyaz ya ce "Ƙarya ne, ni dai ka kama ni ka sake kulle ni, ba za ka iya wannan ba. Kuma duk abu dole na zauna inda zan iya ganin ɗa na. Kuma ina nan ina ci gaba da gudanar da aikin da ka bani bisa yarjejeniya, tun da haryanzu ina nan tare da shi ban bar shi ba"

Bokan ya ce "Waye É—an naka, kuma a ina yake?"

"Babu wannan a cikin yarjejeniyar aikina da kai, ka bar zancen a yadda na bar shi kawai"
Bokan nan ya san faÉ—a da Giyaz ba abu ne da zai haifar musu da É—a mai ido ba, sai dai dawowar Hammad mayar musu da aiki baya ne.
Mahmoudu tunanin Nana ya addabe shi, tare da ganin rashin dacewar abin da ya faru. Ga shi alamu sun nuna ƙiri-ƙiri Hammad bai san ya je ya yi wata rayuwa a Nigeria ba.
Ya kuma san muddin ya ce zai je Nigeria sai Hammad ya bi ba'asi, kuma kwana ɗaya ko biyu ya yi kaɗan ya je ya nemi Nana, balle ya yi masa ƙaryar kasuwanci zai je. Ya sha tambayar Mahmoudu a kan ko akwai wani abu dayake damunsa, saboda yanayinsa ya nuna akwai damuwa. Amma ya kan ce masa babu komai.
Hammad ya ce wa Asal baya buƙatar sake ganin Nana. Sai murna take saboda ta zata munin Nana yake gani, shi kuwa mafita yake nema, daga burkicewar da yake yi a duk lokacin da ya ganta. Sai dai kuma kwana biyu da ya daina ganinta sai ya shiga damuwa, ya zamana duk ranar da bai ganta ba, sai ya ji shi tamkar a kurku, wunin ranar bai yi masa daɗi ba sam.
Yana zaune a ɗakinsa, yake kallon yatsunsa babu zobe guda ɗaya, wanda shi ya fi kowanne muhimmanci. Shi dai Matawalle ya ce masa duk wanda ya tambayi zoben ya ce an kai zoben gyara ya samu matsala. Ya kalli tagullar hannunsa, ya din ga murza ta a hankali yana zancen zuci. Saboda gaba ɗaya a rikice yake, kasancewar Nana ta kai masa abinci tana ƙamshin turarensa da yake amfani da shi. Shi dai ya san babu wanda ya bawa turaren, kuma mai aiki kamar Nana ba za ta iya sayen turaren ba, kuma babu yadda za a yi a ce satar turaren ta yi har ta samu ƙwarin gwiwar shafawa. Yadda take yi masa wasu abubuwan kai tsaye wasu lokutan abin yana ba shi mamaki sosai da sosai.
Ganin ya yi hasken wutar ɗakin tana ɗaukewa tana kawowa, daga baya ta tsaya, sai ga wani ɗan gajeren abu a ya bayyana da tsawonsa bai fi 'yar tsana ba, kansa duk wasu ƙayoyi.
Hammad ya zuba wa abin ido, ganin yana motsi.
"Tuba nake shugabana na tsorata ka, ni ne aljanin da aka wakilta hidima ga duk wanda ya ɗauke da wannan tagullar, tun da ka ke ba ka taɓa nema na ba sai yanzu, me ka ke buƙata?"

Hammad ya ce "Waye kai?"

"Arun, bawan aljani ga Sultan Azhar, wannan tagullar mallakinsa ce, kuma ni mai hidima ne ga ma mallakin tagullar"

Hammad ya zuba ido sosai, ya ga ɗan abin tsoho ne tukuf sosai da sosai. Domin kuwa gemunsa ƙasa yake ja.

Ya ce "Amma da idan na murza zoben ba kai nake gani ba"

Arun ya ce "Ai ba ni ka ke kira, hadiman wancan zoben daban, nima kuma daban"

"To ina zoben nawa yake?"

"Ka yi kyautarsa ga wanda ka ke matuƙar ƙauna a matsayin tukuicin soyayya"

Hammad ya ce "Soyayya kuma? Ni É—in?

"Ƙwarai ya shugabana"

"To wa na bawa, kuma yaushe na yi soyayyar, kuma mace ce ko namiji?"

Arun ya sake cewa "Ba na son shiga hurumin da ba nawa ba, ina gudun sake rura wutar fitinar da ke tsakanin gangar jiki buyi, ruhika huɗu, alaƙa huɗu. Gangar jiki ta mutum biyu, ruhi huɗu, na mutum biyu da na aljan biyu, sai kuma alaƙar mata da miji da kuma uba da ɗa, sannu a hankali duk za ka fahimci abubuwan da nake nufi" Daga nan ya ɓace Hammad ya yi shiru yana juya maganganun da suka fi yi masa kama da shirme.
Ya tashi ya fita falo, ya san lokacin kawo masa shayin dare ya yi, sai dai tun kafin ya ƙaraso cikin falon yake jiyo sautin muryarta tana waƙa. Daga nesa kaɗan ya tsaya yana kallonta, yana jin yadda zuciyarsa take bugawa da sauri.

*_ina zana ganka_*
*_saƙo zana baka*_
*Hotona da naka*_
*_Ko ina zana bika*_
*_Kowa tsane ka, ni na tsane shi sanya a ranka*_
*_Zuciyata na baka duk masu ƙin ka su daina shakka*_
*_Rayuwata na baka_*
*_Ni ta ya zan guje ka*_
*_Ka dawo gare ni dan zuciya ta bar kewa*_

Gaba ɗaya sai ya daskare a gurin, gumi ya din ga tsatstsafo masa, ƙwaƙwalwarsa ta shiga Kai komo, kansa kamar zai yi tsawa ya fashe. "Tabbas akwai wani abu, ya san wani abu mai kama da haka, amma yaushe? Kuma a ina?"
Ya daɗe a tsaye a gurin, kafin ya saita nutsuwarsa ya shiga falon. Murmushi ta yi ta daina waƙar da ta ga ya fito ta risuna ta ce "Barka da dare"
Ya jinjina mata kai.

"Sayyid ga shayinka nan, ina fatan na kammala komai, zan iya tafiya?" Ya yi shiru yana jujjuya Sayyid da take kiransa da shi.
Chapter 43 · 0% Book details